Thursday, 29 December 2016

BAYANIN IBNU TAIMIYYAH GAME DA CIN YANKAN DA AHLUL KITABI SUKA YI SABODA IDINSU: Dr. Ibrahim Jalo Jalingo.

BAYANIN IBNU TAIMIYYAH GAME DA CIN YANKAN DA AHLUL KITABI SUKA YI SABODA IDINSU:

Dr. Ibrahim Jalo Jalingo.

Kwanakin baya mun yi bayani gameda hukuncin karban kyautukan idi na dukkan nau'ukan kafurai, mun kuma yi bayani game da hukuncin cin yankan da Ahlul Kitabi; watau Yahudawa da Kiristoci suka yi saboda idodinsu, to amma muna jin akwai mutanen da suka karanta wancan rubutun namu amma kuma suka kasa fahimtar wani bangare nasa, watakila saboda yawan rubutun. Dalilin da ya sa kuwa muka ce akwai wadanda ba su fahimci abin da aka rubuta sosai ba shi ne: irin yadda aka cigaba da aiko mana da tambayoyi game da mas'alar cin yankan da Ahlul Kitabi suka yi domin bukuwan idodinsu.
***************
A wannan rubutu namu za mu kawo bayanan Salaf ne da Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya kawo dangane da hukuncin cin yankan da Yahudawa da Kiristoci suka yi domin bukukuwan idodinsu. Ibnu Taimiyyah ya ce a cikin littafinsa mai suna Iqtidhaa'us Siraa'til Mustaqim 2/555,558 :-
((وأما ما ذبحه اهل الكتاب لاعيادهم وما يتقربون بذبحه الى غير الله نظير ما يذبح المسلمون من هداياهم وضحاياهم متقربين بها الى الله تعالى، وذلك مثل ما يذبحون للمسيح والزهرة، فعن احمد روايتان: اشهرهما في نصوصه: انه لا يباح اكله وان لم يسم غير الله تعالى. ونقل النهي عن ذلك عن عائشة وعبد الله بن عمر.....والرواية الثانية ان ذلك مكروه غير محرم))
Ma'ana: ((To amma abin da Ahlul Kitabi suka yanka saboda idinsu, da kuma abin da suke yin ibada ta hanyar yanka shi ga wanin Allah' kamar abin da suke yankawa saboda Almasihu, da Zahrah, irin dai abin da Musulmi suke yankawa na Hadaya, da Layya, domin neman kusantar Allah da shi, to, Imam Ahmad yana da fatawowi biyu game da hakan, fatawar farko wacce ita ce ta fi shahara: Wannan ba ya halatta a ci shi koda kuwa ba a ambaci sunan wanin Allah a kansa ba. An kuma nakalto hana cin wannan yankan ma daga Nana A'isha, da Abdullahi Dan Umar..... Fatawa ta biyu ita ce: Cin wannan yankan makruuhi ne ba haramun ba. Wannan ita ce mazhabar Malikiyyah, Imam Malik ya kyamaci cin abin da Ahlul Kitabi suka yanka saboda Coci-Cocinsu, ko saboda idinsu amma ba tare da ya haramta hakan ba)).

Har yanzu Ibnu Taimiyyah ya ce a cikin Iqtidhaa'us Siraa'til Mustaqim 2/559 :-
((ونقلت الرخصة في ذبائح الأعياد ونحوها عن طائفة من الصحابة رضي الله عنهم، وهذا فيما اذا لم يسموا غير الله، فان سموا غير الله في عيدهم او غير عيدهم حرم في اشهر الروايتين، وهو مذهب الجمهور، وهو مذهب الفقهاء الثلاثة فيما نقله غير واحد، وهو قول علي بن ابي طالب وغيره من الصحابة، وهو قول اكثر فقهاء الشام وغيرهم. والثانية: لا يحرم وان سموا غير الله، وهذا قول عطاء ومجاهد ومكحول والاوزاعي والليث)).
Ma'ana: ((An ciro yin sauki a kan cin yanke-yanken idodin (Yahudawa da Kiristoci) da makamantansu (su yanke-yanken) daga wani sashi na Sahabbai Allah Ya kara musu yarda amma fa wannan sai idan ba su ambaci wanin Allah a lokacin yankan ba, in kuma har sun ambaci wanin Allah a lokacin yankan to cin sa ya haramta a cikin fatawa mafi shahara daga cikin fatawowi biyu da Imam Ahmad yake da su a cikin mas'alar, wannan kuwa shi ne mazhabar Jumhur, kuma shi ne mazhabar Fuqaha'un nan guda uku, kamar yadda mutane da yawa suka ruwaito, kuma shi ne maganar Aliyyu Bin Abi Taa'lib, da waninsa a cikin Sahabbai, daga cikinsu ma akwai Abud Dardaa, da Abu Umamah, da Irbadh Bin Saa'riyah, da Ubaa'dah Bin Saa'mit, kuma shi ne maganar malaman Sham da wasunsu. Fatawar Imam Ahmad ta biyu ita ce: Cin wannan yankan ba haramun ba ne koda kuwa sun ambaci sunan wanin Allah a lokacin yankan, wannan kuwa shi ne maganar Ataa, da Mujaa'hid, da Makhuul, da Auzaa'iy, da kuma Laith)).

Allah muke roko da Ya yi mana muwafaka har kullum. Ameen.

Albany Dabai,
08069123479.

LABARAI A TAKAICE

LABARAI A TAKAICE

*Rundunar sojan Najeriya ta ce ta samu KOFIN ALKUR'ANUL KARIM da shugaban 'yan ta'addan Boko Haram Abubakar Shekau ke rikewa da kuma tutar helkwatar sa a dajin Sambisa da a ka ragargaza.

*Rundunar ta ce ta hakikance littafin mai girma mallakar Shekau ne da ya bari lokacin da ya arce.

*Yanzu dai za a mika KOFIN NA ALKUR'ANUL KARIM ga babban hafsan rundunar sojan Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai don ya mika shi ga shugaba Buhari.

*Daga wannan labari dai za a fahimci Abubakar Shekau ka iya zama ya arce ne ba ya rasa ran sa daga lugudan wuta ta sama ba.

*Ministan tsaron Najeriya Burgediya Janar Mansur Dan Ali ya ce tun 'yan makwanni sojoji ke tsare-tsaren murkushe 'yan ta'adda a dajin Sambisa inda da zarar kammala ruwan damuna a ka samu sararin jefa boma-bomai kan maboyar 'yan ta'addan a dajin.

*Dan Ali ya kara da cewa bayan kammala jefa boma-boman dakarun sojan kasa sun shiga dajin inda su ka kammala share fage da kwace dajin.

*Hakanan ministan ya ce ta kan yi wu sauran matan Chibok sun saje cikin kimanin mutum 1000 da a ka ceto daga dajin kuma ba mamaki sun yi aure da sai an tantance za a gano su.

*Ministan ya yi kira ga mutane su ci gaba da taka tsantsan da mutanen da ba su gane take-taken su ba da kai irin wannan labari ga jami'an tsaro.

*Jami'an soja sun tabbatar da damke wani dan Boko Haram da alamu su ka nuna ya arce ne daga dajin Sambisa inda ya shigo anguwar Utako Abuja ya fara wa'azi rike da Alkur'ani mai girma da kuma sarka a wuyan sa mai alamar gicciye na Yesu Kiristi.

*Masu ibada a masallacin kasuwar gwarawa da ke Jabi su ka ankara da yanayin mai wa'azin da kazalika ya ke rike da wata leda da ke da dabino da wani turare.

*Don kara bincike,an kawo wanda a ke tuhumar masallacin jumma'ar Umar Ben Khaddab inda ya rika bayanai na rashin kan gado da alamun rashin gaskiya.

*Jami'an sintiri na birnin Abuja sun gaiyato sojoji daga barikin Gowon wadanda su ka garzayo su ka yi awun gaba da shi.

*Tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau ya ce a matsayinshi na Malami har yanzu bai ga wani abin a zo a gani ba da BUHARI ya yi wa kasa Najeriya.

*Shekarau ya ce dukka abubuwan da Buhari ya ce zai yi a lokacin Kamfen har yanzu bai yi wani guda daya ba wanda za'a ce yau gashi yayi.

*Kamar Yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito tace tsohon gwamnan ya fadi hakanne a garin Gombe.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
29/Rabi-Al'Awwal/1438
29/December/2016

Albany Dabai,
08069123479.

Friday, 23 December 2016

LOKUTTAN SALLAH NA GARIN KATSINA

Assalamu Alaikum Warahmatullah
Ga  Lokuttan Sallah na Garin Katsina
Alfijir "05:33"
Fitowar Rana "6:48"
Karyawar Rana "12:35"
La'asar "3:45"
Magrib "06:10"
Isha'i "07:08"
Yau kuma "24/03/1438" "HIJIRA" zamuci gaba da kawo maku duk juma'a da yardar Allah Wa Nas'alulaha AttaufiQ.  juma'at mubarak

Friday, 16 December 2016

LOKUTTAN SALLAH NA GARIN KATSINA

Assalamu Alaikum Warahmatullah
Ga  Lokuttan Sallah na Garin Katsina
Alfijir "05:30"
Fitowar Rana "6:45"
Karyawar Rana "12:35"
La'asar "3:42"
Magrib "06:08"
Isha'i "07:08"
Yau kuma "17/03/1438" "HIJIRA" zamuci gaba da kawo maku duk juma'a da yardar Allah Wa Nas'alulaha AttaufiQ.  juma'at mubarak

Thursday, 15 December 2016

LABARAI A TAKAICE

LABARAI A TAKAICE

*Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da bayanan kasafin kudin 2017 da ya kai Naira tirliyan 7.28 da ya wuce na bara da 19.5% don kasafin 2016 Naira tiriliyan 6.8.

*An dora kasafin kan hako gangar mai miliyan biyu da dubu dari biyu a wuni kuma kan hasashen gangar za a ke sayar da ita dala 42 a kasuwar duniya.

*Yayin da matsayin canjin gwamnati ya ke Naira 197 kan dala daya a kasafin kudin 2016, kasafin 2017 canjin ya koma Naira 305.

*Kasafin kudin 2016 zai kammala ne a watan Afrilun 2017 gabanin sabon kasafin ya fara aiki.

*Shugaban Najeriya ya yi albishir din fatar fita daga kuncin tattalin arziki a sabuwar shekara.

*Shugaban Buhari ya baiyanawa gamaiyar majalisun dokokin Najeriya dalilan dage gabatar da kasafin kudin 2017 daga safe zuwa rana.

*Shugaban sanye da babbar farar riga da hula,ya ce bai iso Najeriya da wuri ba ne daga Gambia sai hudu da rabi na asubahin Najeriya.

*Tsaikon dai ya faru sakamakon yadda shugaban ya ba da labarin rage hanya da ya yi wa sauran shugabanni 3 na sasanta Yahaya Jameh da Adama Barrow.

*Wannan ya nuna shugaban ya sauke shugaba Bai Koroma a Freetown,Ellen Johnson Sirleaf a Manrovia da John Dramani Mahama a Accra kafin jirgin na sa ya iso Abuja.

*Hakanan tun farkon tafiyar ma sai da shugaban ya biya ta wadannan kasashen don daukar shugabannin 3.

*Tawagar shugabannin Afurka da ta je Gambia ba ta samu nasarar shawo kan shugaba Yahaya Jameh ya sauka daga mulki ba.

*Tawagar karkashin shugabar Laberiya Ellen Johnson Sirleaf ta gana da Yahaya Jameh da shugaba mai jiran gado Adama Barrow.

*Jameh dai ya bukaci wa imma a sake sabon zabe ko kuma a yi raba daidan iko tsakanin sa da Adama Barrow.

*A halin yanzu dai sojoji na mamaye da hukumar zaben Gambia a birnin Banjul inda Jameh ya shigar da kara kotun koli don kalubalantar sakamakon zaben.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
15/Rabi-Al'Awwal/1438
15/Safar/1438

Albany Dabai,
08069123479.

Wednesday, 14 December 2016

HANYOYIN SAMUN INGANTACCIYAR HADDAR ALQUR'ANI.

HANYOYIN SAMUN INGANTACCIYAR HADDAR ALQUR'ANI:

Daga
Sheikh Aliyu Saeed Gamawa.

1. Ka fara haddar ka da addu'ar neman taimakon Allah cikin wannan niyya taka ta alheri.

2  Ka kula sosai da kanka wajen nisantar kazamtar haramun, wato ka tsaya wajen cin halal, domin cin
haram yana toshe basirar Dan Adam

3. Ka nisanci fara hadda don burin samun dukiya, kuma ka cire kwadayin abin duniya a zuciyarka. Haddar Alqur'ani bata zama a cikin kwakwalwar duk wanda ya
matsu yaga ya tara dukiya a cikin haddar sa da zafi-zafi.

4. Kayi karatu a wajen Malami na Allah wanda yasan Karatun, Kuma serious malami wanda ya maida hankalinsa akan hidimtawa Alkur'anin.

5. Ka nemi goyon bayan mahaifan ka tare da rokon addu'arsu, don sanya albarka daga iyayenka  ginshiki ne wajen nasarar samun haddar ka cikin sauki.

6.  Kaifin basira da hazaqa yana taimakawa wajen saurin samun yin hadda mai kwari cikin karamin lokaci

7. Ka fara hadda da niyya mai kyau, wato ka zamo mai kwadayin son karatun da burin haddar alkur'ani.

8.  Ka zamo mai juriya akan kowacce irin wahalar da zaka riska a wajen neman karatun ka, ka cire son hutu da yawan kasala ko son nishadi da wargi da zai jawo maka lalaci.

9. Tanadin abinci yana da muhimmanci don ka samu natsuwa, don ba'a iya hadda mai kyau da yunwa amma kar kace sai kaci mai kyau kasha mai kyau a kullum.

10.  Kar ka sanya gaggawa wai sai ka gama hadda a karamin lokaci, ka natsu ka bi a hankali  domin
ba'a samun ilimi a cikin dare daya.

11. Samun abokan karatu na kirki da zaku na tafiya tare cikin hadda yana taimakawa, amma ka kiyaye Idan fa abokanka suka zamo na banza, ko wadanda basa son karatun ko masu kasala to tabbas ka hadu da matsala da ci baya a harkar karatun ka.

12. Ka tsara gwargwadon abinda zaka na haddacewa  a kullum, wato kamar ka tsara cewa a duk cikin kwana 3 zaka yi haddar allonka ko shafi daya ko biyu ko makamancin haka..

13. Ka rika karanta wuraren da ka haddace a cikin Sallar ka  ta farilla da nafiloli a kowanne wuni.

14. Idan da dama ka nemi allo ka rubuta da kanka wajen da kake son ka haddace, ko ka samu littafi mai rubutun da idon ka zai karanata sosai, sannan kayi ta QwamI.. Ba-ji ba-gani.

15. Ka tsarawa kanka lokaci a cikin safiya da maraice kana tilawa na maimaita wurin karatun ka adadi mai yawa, wato kana biyawa a kullum kamar sau 100 in zaka iya.

16. Ka za6i yin tilawa da dare da jijjifin safiya, ka tsara yadda zaka Qaranta barcinka, kuma abinda yafi shine kana bacci da wuri don ka samu tashi cikin dare, ka kula wajen cin abinci madaidaici, Ka takaita yawo da surutu maras amfani da zaman wurin hira. kuma ka rage yawan abokai

17. Ka kula sosai da yawan ibada da nisantar aiyukan sa6o.

18. Ka gujewa sauraron wakokin banza da
raye-raye da kallon film don suna  makantar da zuciya.

19. Ka tsare harshen ka daga batsa da zagin mutane da kallon haramun da latse-latsen waya maras amfani.
20. In kana samun wahalar rike hadda kayi hakuri ka dogara ga Allah, ka yi juriya ka nisanci debe tsammani da karaya a zuciyar ka. Lallai in kana himma da dagewa zaka samu taimakon Allah.

Ina rokon Allah ya karfafa niyyar mu, ya cika mana burin mu ya hore mana saukin hadda ya bamu karatu mai albarka, amin

Albany Dabai,
08069123479.

LABARAI A TAKAICE


LABARAI A TAKAICE

*Tsohon gwamnan jihar sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya karbi ziyyarar jaddada goyon bayan kungiyoyin kabilar Yarbawa da Igbo a gidansa na Sokoto dake Shinkafi Road. Kungiyoyin dai sunczo bada gaisuwar girma ne tare da nuna goyon bayansu ga jagoransu Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa.

*A nasu jawabin shugabannin sun nuna jaddada goyon bayansu ga jam'iyyar PDP akoda yaushe har zuwa 2019, tare da biyayya ga shugaban jam'iyyar PDP Alhaji Ibrahim Milgoma da sauran shugabanni jam'iyya.

*Daga karshe Garkuwan Sakkwato ya yi bayanin godiya da wannan ziyara da wadannan manyan kungiyoyin suka yi masa inda ya maida jawabi ga kungiyoyin da sucigaba da hakuri da adawa da suke yi da kuma biyayya ga jam'iyyar PDP.

*Sojojin Nijeriya sun samu nasarar ceto kimanin Shanu 300 daga barayin shanu a jihar Zamfara inda aka mika su ga jami'an gwamnatin jihar don mika su ga wadanda suka mallake su.

*Kwamandan Birget ta Daya da ke Sokoto, Birgediya Janar Ginikanwa Nwosu ne ya bayyana haka inda ya nuna cewa a kowane mako suna ceto akalla shanu 500 daga barayin Shanun. Ya kara cewa an kara yawan sojoji a jihar don murkushe ayyukan satar mutane da shanu.

*Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya tabbatar da cewa jam'iyyar APC ta tafka manyan Kurakurai wanda dole sai ta zauna don duba yadda za ta shawo kansu.

Dogara ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da ya kai ziyara ga Shugaban APC na Kasa, Cif John Odigie Oyegun a hedkwatar jam'iyyar da ke Abuja inda ya nuna cewa akwai bukatar samun kyakkyawar alaka tsakanin majalisa da bangaren gwamnati.

*Kotun tarayyar Najeriya  da ke garin Ado Ekiti da ke jihar Ekiti ta umarci hukumar EFCC da ta gaggauta bude asusun ajiyar Bankin Gwamnan Ekiti, Ayo Fayose wanda ta rufe kwanaki bisa Izinin wata kotun tarayya da ke Lagas.

*A hukuncin da Alkalin kotun, Mai Shari'a Taiwo Taiwo ta yanke, ya nuna cewa hukumar EFCC ba ta bi tsarin doka wajen rufe asusun guda biyu da ke Bankin Zenith. Alkalin ya kuma nuna cewa EFCC ta shiga hakkin Fayose a matsayinsa na Gwamnan wanda kuma dokar kasa ta bashi kariya daga fuskantar tuhuma.

*Shugabar kasar Liberian Ellen Johnson Sirleaf, wacce ta jagoranci wata tawagar shugabannin kasashen yammacin Afrika don sasanta rikicin siyasar kasar Gambia ta ce babu wata yarjejejeniya da suka cimma don kawo karshen dambarwar.

*Tun da farko dai Sojoji a Gambia sun mamaye hedikwatar hukumar zabe yayin da Jam'iyyar Mr Jammeh ta shigar da kara a kotun kolin kasar inda ta bukaci a soke zaben.

*Sai dai a halin yanzu kotun bata da isassun Alkalai, saboda haka ba a san takamammen lokacin da za a saurari karar ba. Abaya dai Shugaban kungiyar ta ECOWAS, Marcel de Souza, ya yi barazanar cewa za su yi amfani da karfi idan Mista Jammeh ya ki mutunta kundin tsarin mulkin kasar.

*Zababben shugaban kasar Adama Barrow, wanda ya lashe zaben na 1 ga watan Disamba, ya nemi taimakon kasashen duniya. A watan gobe ne ya kamata a rantsar da shi a kan karagar mulki.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
14/Rabi-Al'Awwal/1438
14/December/2016
Albany Dabai,
08069123479.

LABARAI A TAKAICE

LABARAI A TAKAICE

*Ayau talata ne ake saran tawagar kungiyar kasashen Afirka ta Yamma zata isa kasar Gambia dan janyo hankalin shugaba Yahya Jammeh na ganin ya sauka daga mukamin sa cikin ruwan sanyi bayan shan kashin da yayi a zaben shugaban kasar.

Shugabar kungiyar ECOWAS Ellen Johnson Sirleaf zata jagoranci tawagar wadda ta kunshi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da shugaban Saliyo Ernest Bai Karoma da shugaban Ghana mai barin gado John Dramani Mahama.

*Shugaban. Naijeriya, Muhammad Buhari ya tabbatar da cewa kafin shekarar 2019, gwamnatinsa za ta gina Madatsun ruwa 400 a duk fadin kasar nan don gudanar da noman rani.

Shugaban ya bayyana haka ne a wurin taron kungiyar yaki da yunwa ta FCPN wanda aka yi a Abuja inda ya nuna cewa yawan 'yan Nijeriya ya rubanya  a tsakanin shekaru 25 yana mai jaddada cewa a kan haka ne ya sa gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen farfado da harkar noma da ma'adinai.

*Ya ce ta hanyar gina Madatsun ruwa ne, manoma za su iya yin noma sau uku a duk shekara.

*Gwamnan Jihar Akwa Ibom da ke kudancin Nijeriya, inda rufin wata Majami'a ya fadi akan masu ibada a ranar Asabar da ta gabata, in da mutane da yawa suka mutu, ya bada umarnin kama wadanda suka yi kwangilar ginin, cewar wata kafar yada labarai ta jihar.

*Gwamna Emmanuel wanda yake a majami'ar yayin da al'amarin ya faru, kuma ya tsira ba tare da jin ko da ciwo ba, ya bada umarnin kamen.

*Maimaita zaben majalisa na jihar Rivers da ke kudu maso kudancin Najeriya bai wanye lafiya ba inda 'yan bangar siyasa su ka hallaka wani jami'in 'yan sanda DSP Alkali Muhammed kazalika su ka fille kan sa.

A wannan harin da ya faru a yankin da shugaban babbar jam'iyyar adawa na jihar ya fito, wassu abokan aikin dan sandan sun sha da kyar.

*Jihar Rivers dai ta dade da zama mai hatsarin gaske wajen gudanar da lamuran zabe inda baya ga kisan gilla da 'yan bangar ke yi su kan fille kan wanda su ka kashe don firgita jami'an tsaro da sauran 'yan siyasar da su ke hamayya da su.

*Wasu 'yan bindiga dadi da har yanzu ba a san ko su wane ne ba sun arce da wasu mata 35 a kauyen Matankari da ke karkashin masarautar Dansadau a karamar hukumar Maru da ke jihar Zamfara.

*Da yake tabbatar da aukuwar lamarin Kwamishinan 'Yan sanda jihar, Shaba Alkali ya ce rundunarsa ta samu nasarar kwato wasu daga cikin Matan kuma a halin yanzu suna ci gaba da farautar wadannan 'yan ta'addan da nufin kwato sauran Matan.

*Rahotanni dai sun nuna cewa 'yan bindiga dadin wanda yawansu ya kai kusan mutum 100 sun aukawa kauyen ne inda suka rika harbe harbe ta yadda suka tarwatsa mutanen kauyen sannan suka arce da Matan.

*Gwamnatin jihar Bauchi da ke arewa maso  gabashin Najeriya ta biya ma'aikata albashi na wasu watanni  da su ke bin bashi inda hakan ya kawo walwala a jihar.

*Gwamna Muhammad Abdullahi Abubakar na jam'iyyar APC ya sha ba wa ma'aikatan hakuri da nuna gwamnatin ta sa na bin duk hanyoyin da su ka dace don biyan albashin.

*Akwai jihohi da dama da su ka gaza biyan albashi musamman don raguwar kudaden shiga da kuma kason da jihohin ke samu daga gwamnatin taraiya.

*Hakanan jihohi da dama sun dauki matakan bincike don rage ma'aikata musamman na bogi da wadanda ke karbar albashi ba bisa ka'ida ba.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
13/Rabi-Al'Awwal/1438
13/December/2016

Albany Dabai,
08069123479.

Friday, 9 December 2016

Kyautar bikin Kirsimeti: Halal ko Haram? -Dr. Sani Umar R/Lemu

KYAUTAR BIKIN KIRSIMETI:
HALAL KO HARAM?

Da yawa Musulmi suna tambayar shin ko ya halatta su karbi kyautar kiristoci a ranar kirsimeti,musamman wandan da suke zaune lafiya tare da su,ko suke aiki a guri daya.

Ga bayanin da Malamai suka yi dangane da haka:

1- Baya halatta ga Musulmi ya nuna farincikin sa da wannan ranar,ta hanyar aikawa da gaisuwa ko kyauta ko furanni, ko makamantan su.

2- Ba ya halatta gare shi ya ci abin da aka yanka da sunan wannan rana.

3- Ya halatta ya karbi kautar da za su bashi a wannan ranar, Kamar yadda ya halatta gare shi ya ci abin da za su ba shi wadanda ba yankawa ake yi ba.
Kamar kayan marmari.

4- Dalili kuwa shi ne:

A) Baihaqi ya ruwaito a cikin littafinsa As-
Sunanul Kubra 9/234 cewa, Muhammad Bn Sirin ya ce: an kawo wa Ali, Allah ya kara yarda a gare shi, kautar idin majusawa Nairuz.

Sai ya ce: menene wannan kuma?

Sai suka ce masa, ya Sarkin
Muminai yau ranar idin Nairuz ce.

Sai ya ce, to kullum ma su yi 'Nairuz'.

Wato ya karba, tare da nuna ya ji dadin kyautar.

B) Ibn Abi Shaibah a cikin littafinsa Al-Musannaf 5/126 daga Sahabin nan Abu Barzata Al-Aslamy cewa: yana da makwabta majusawa, kuma a duk
ranar bukukuwansu suna aiko masa da
kyaututtuka a gidansa, sai yakan cewa iyalinsa, yaya abin yake?; idan kayan marmari ne to ku ci,wanda kuma ba kayan maramari bane, to ku mayar musu kayansu.

C) Haka kuma ya ruwaito 5/126 cewa: wata mata ta tambayi Nana A'isha ta ce, muna tare da mata majusawa masu sana'ar shayar da jarirai,to duk ranar idin su suna aiko mana da kyauta.

Sai A'isha, Allah ya kara yarda a gare ta, ta ce mata,abin da aka yanka domin wannan ranar kada kuci.

Ku ci kayan marmari na itatuwa.

Ibn Taimiyya ya ce, wannan ya nuna idinsu ba shi da wani tasiri wajen ya hana a karbi kyautarsu.

Karbar kyautar su a ranar idin su da ranar da ba idin ba duk hukunci daya ne, domin
wannan ba shi ne taimaka musu ba akan aikinsu na kafirci.

Duba Littafinsa Iqtidha' Siratil Mustaqim 2/52.

Sannan a karshe yana da kyau mu fahimci cewa,Ba ya halatta musulmi ya taimaka da yi musu yanka a wannan ranar.

Kuma koda musulmi ne ya yanka musu ba za a ci ba.

Allah ka shiryar da mu tafarkinka madaidaici.

Dr. Sani Umar R/lemo.

Albany Dabai,
08069123479.

SU WANE NE AHLUS-SUNNATI WAL-JAMA'A NA HAKIKA? -Abubakar Umar Rigasa

SU WANENE AHLUS-SUNNATI WALJAMA'A NA HAKIKA ?

مؤتمر الدولى : المفهوم الصحيح لأهل السنة والجماعة وأثره في الوقاية من الغلو والتطرف

TAKARDAR BAYAN TARON MALAMAN DUNIYA WANDA YA GUDANA A KASAR KUWAIT, TARON DA YA SAMU HALARTAR MALAMAI DAGA KASASHEN MUSULMAI HAR GUDA ASHIRIN DA BIYAR (25), MALAMAN SUNYI KOKARI MATUKA WAJEN BAYYANAMA DUNIYA SU WANENE AHLUS-SUNNATI WALJAMA'A NA HAKIKA.

ABUBUWANDA SUKA CIMMA MATSAYA AKAI...

1) Ahlus-sunnati waljama'a sune wad'anda suke biyayya ga littafin Allah da Sunnar Manzonsa (SAW), kuma jagororinsu sune Sahabbai sannan Tabi'ai sannan wad'anda suka biyo bayan Tabi'ai sannan wad'anda suka biyo bayansu suma, kuma suka tafi akan Tafarkinsu tareda kyautatawa.

2) Sannan Manhajin Ahlus-sunnati waljama'a guda dayane tilo babu wasu Manhajojin acikinsa.

3) Kuma Gaskiyane karya bata iya tunkudeshi,

4) Sannan Manhajine tsaka-tsaki babu wuce gona da iri acikinsa (Guluwwi).

5) Sannan kuma sabani acikin mas'alolin ijtihadi tsakanin Malaman Mazhabobi hudu (4), Hanafiyya Malikiyya, Shafi'iyya da kuma Hanabila, baya lizimta fita daga Sunna kuma baya halasta kiran mutane da sunaye mabanbanta da jinginasu ga kungiyoyi da gungu-gungu ko kiransu da yan bid'a.

6) Manhajin Ahlus-sunnati waljama'a bai samo asali daga Imam Ahmad bin Hambal ba ko Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya ko Sheikhul Islam Muhammad Ibnu Abdulwahhab, abin sani ya samo asaline daga Sahabban Annabi (SAW) Da Tabi'ai da wad'anda suka biyo bayansu.

ALLAH YA FIHIMTAR DAMU YA GASKIYA YA KUMA BAMU IKON BIYAYYA GARETA.

Albany Dabai,
08069123479.

Tuesday, 6 December 2016

LABARAI A TAKAICE


*Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da shugabar Laberiya Mrs. Ellen Johnson Sirleaf kan lamuran tsaron yankin Afurka ta yamma.

*Ganawar dai tazo ne gabanin taron lamuran tsaro da zaman lafiya na birnin Dakar din kasar Senegal.

*Laberiya dai na daga kasashen Afurka ta yamma da su ka dandana kudar yakin basasa inda hakan ya yi sanadiyyar zubar da jini har ma ga tsohon shugaban kasar Samuel Doe.

*Najeriya dai ta tallafa wajen dawo da zaman lafiya a Laberiya ta hanyar kafa rundunar taron dangi ta "ECOMOG" da Janar Timothy Shelpidi mai ritaya ya jagoranta.

*Shugabanni a yankin Afurka da manyan jami'ai sun taru a babban birnin Senegal, Dakar don taron wanzar da zaman lafiya da tsaro.

*Taron dai wanda zai kammala a talatar nan,zai samu karfin guiwar cimma muradu daga kungiyar Afurka AU.

*Shugaban Senegal Macky Sall ne ke jagorantar taron.

*Wassu abubuwan da a ke saran taron zai tabo akwai 'yancin dan adam da lamuran jinkai.

*Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya soki majalisar dinkin duniya da sauran kungiyoyin bayar da agaji saboda "zuzuta" halin da 'yan gudun hijirar da Boko Hara suka kora daga gidajensu ke ciki.

*A wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce kungiyoyin suna kambama halin da 'yan gudun hijirar ke ciki ne da zummar samun kudi daga wajen gwamnatoci.

*Ya bayar da sanarwar ce kwanaki kadan bayan majalisar ta dinkin duniya ta ce fiye da mutum 5m da Boko Haram ta raba da muhallansu na fuskantar hatsarin kamuwa da mummunar yunwa.

*Ku gaggauta Gamawa Da 'Yan Boko Haram, Domin Ina So Na Mayar Da Ku Bariki A Shekarar 2017, Sakon Janar Buratai Ga Sojojin Naijeriya

*Gwamnatin jihar Kaduna tace kungiyar Shi'a kungiya ce da ayyukanta gaba daya ya jibinci nuna tawaye ga dokokin kasa saboda haka daga yau ta ajiye ta a matsayin kungiyar yan tawaye.

*Gwamnatin ta ce shugaban 'yan kungiyar Ibrahim El-Zakzaky da yake kulle a yanzu haka, shine za a' dora ma alhakin duk laifukan da mabiya akidar Shi'a din suka aikata domin shine jagoransu.

*Gwamnatin Naijeriya zata haramta shigo da motoci ta iyakokin kasa kamar yadda kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito.
Duk wata mota da za a shigo da ita yanzu, sai dai ta ruwa.

*Wanda duk zai shigo da mota ta iyakokin kasa, zai iya yin hakan nan da zuwa 31 ga Disambar 2016." Inji Adeniyi. 

*Wannan dai yana zuwa ne a lokacin da gwamnatin ta haramta shigo da shinkafa ta iyakokin kasa tun a afrilun 2016. Abin da ya jawo ta yi tashin gwauron zabi.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
06/Rabi-Al'Awwal/1438
06/December/2016

Monday, 5 December 2016

LABARAI A TAKAICE


*Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai sauka a birnin Dakar din kasar Senegal don taron zaman lafiya da tsaro karo na uku na "DAKAR"

*Shugaban Senegal Macky Sall ne zai jagoranci taron.

*Taron dai wanda na kwana biyu ne daga litinin din nan, zai samu bayanai na bunkasa tsaro daga kungiyar hadin kan Afurka AU.

*Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba daidai ba ne kalaman da mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi cewa gwamnatinsa ta karbi N4.5tr, yana mai cewa N1.5tr ta karba.

*A wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Malam Garba Shehu ya fitar, yace ya kamata mai martaba ya tsaya a matsayin sa na Sarki

*Tsofaffin shugabannin hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati, EFCC, Nuhu Ribadu da Farida waziri sun zargi juna da hannu wajen aikata cin hanci da rashawa.

*Wata sanarwa da Farida Waziri ta fitar ta ce ya kamata Malam Nuhu ya yi wa 'yan Najeriya bayani kan biliyoyin kudi da kadarorin da ya kwace daga wurin mutanen da ake zargi da cin hanci lokacin da yake shugabanci hukumar.

*Tana mayar da martani ne kan zargin da Nuhu Ribadu ya yi mata a makon jiya cewa tana cikin mutanen da suka hana ruwa gudu a fafutikar da ya yi ta hukunta mutanen da ake zargi da cin hanci a kasar.

*Tsofaffin manyan jami'an EFCC din dai ba sa jituwa da juna tun bayan da aka maye gurbin Nuhu Ribadu da Farida Waziri a hukumar ta EFCC, matakin da a wancan lokacin, 'yan kasar da dama ke yi wa kallo na yunkurin hana Ribadu hukunta wasu shafaffu da mai.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
05/Rabi-Al'Awwal/1438
05/December/2016

Sunday, 4 December 2016

ANKAI ZIYARAR TA'AZIYYAH GA MAL. NUHU ABDULLAHI SARDAUNA.


A yau ne Tawagar shugabannin kungiyoyin Izala na jihohin Benue, Nasarawa, Plateau, Kogi, Niger da Abuja suka kai ziyarar Ta'aziyya zuwa ga Mal. Nuhu Abdullahi Sardauna, daya daga cikin menbobin Majalisar Agaji ta kasa, bisa rashin mahaifinsa da yayi a yammacin Jiya Asabar.

Tawagar ta kai ziyarar ne bayan tashi daga wa'azin Hadin Gwiwa da Jahohin suka Gabatar a ranakun Asabar da Lahadi da muke ciki.

A yayin ziyarar Ta'aziyyah an gabatat da jabawai daban-daban domin jajantawa wanda yayi rashi, da shi da sauran 'yan Uwansa.

Sheikj Ibrahim Barin Ladi, Sheikh Muhammad Auwal Mai Gaskiya, Sheikh Isah Aliyu Jen, suna daga cikin wadanda sukayi jawabai na ta'aziyya a wurin.

A madadin dukkan Ahlussunnah na Jihar Benue, Da shugaban Kungiyar Izala Na Benue, Alh. Musa Abdullahi Plateau, muna mika sakon Ta'aziyya ga Mal. Nuhu Abdullahi Sardauna bisa rasuwar mahaifinsa. Muna addua'ar Allah ya jikansa.

Jibwis Social Media
Benue State.

LABARAI A TAKAICE


*Manyan malaman musulunci sun taru a babban birnin Najeriya Abuja inda su ka fara gabatar da darussan kyakkyawar akida ga musulmi.

*An ga musulmi maza da mata a taron na wuni biyu da ke gudana a babban dakin taro na kasa da kasa "international conference centre" Abuja.

*Taron dai na gudana a rikunoni daban-daban a duk dakunan taron. Baya ga manyan malaman Ahlussunnah wal jama'a na Najeriya da su ka hada da Sheikh Tajuddeen Adegun, Sheikh Dr. Isa Ali Pantami da Abubakar Sadeeq na masallacin Annur, an samu bakin malamai da su ka hada da Mufti Menk, Sheikh Assim Alhakim da Sheikh Sa'eed Rageh daga kasar Kanada.

*Mahalarta taron kan samu damar yin tambayoyi inda malaman ke amsawa bisa hujjoji masu inganci.

*Mai martaba sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II ya ce kuskure ne gwamnatin Naijeriya tace za ta ciwo bashin kusan dala biliyan talatin, akan cewa za ta biya bashin a cikin shekaru biyu.

*Da yake jawabi a wajen wani taro a Abuja, Sarki Sanusi ya ce ciwo bashin, abu ne mai kyau, amma idan har gwamnatin za ta samu sassauci a yarjejeniyar bashin, sannan kuma a yi amfani da kudin wajen bunkasa bangaren makamashi, da lantarki da gina hanyoyi.

*Shugaban Naijeriya, Muhammadu Buhari ya taya zababben Shugaban kasar Gambiya, Adama Barrow murnar lashe zabe sannan kuma ya yaba wa Shugaba Mai barin Gado bisa dattakon da ya nuna na amincewa da sakamakon zaben.

*A nasa bangare, Shugaban kasar Gambia mai jiran gado, Adama Barrow, ya ce, idan har akwai yiwuwar gurfanar da shugaban kasar mai barin gado, Yahya Jammeh, to za a bi ka'ida wajen hakan.

*Adama Barrow ne dai ya kayar da Yahya Jammeh da tazarar kuri'a fiye da 50,000.
Mutane suna ta yin kira da a gurfanar da Yahya Jammeh bisa ayyukan take hakkin jama'a da ake zargin ya aikata.

*Anga wani faifan Video da ya nuna Shugaban Kasar na Gambiya mai barin gado, Yahya Jamme a lokacin da ya buga waya yana taya abokin takararsa, Adama Barrow murnar lashe zaben kujerar shugabancin kasa da yayi kamar yadda Shugaba Jonathan ya yi a zaben 2015 inda ya buga wa Shugaba Buhari ya taya shi murnar lashe zaben.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
04/Rabi-Al'Awwal/1438
04/December/2016

Saturday, 3 December 2016

LABARAI A TAKAICE


*Cin Hanci Da Rashawa Ne Silar Fadawar Nijeriya Cikin Mawuyancin Hali, Inji Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu

*Za Mu Marawa Hukumar EFCC Baya Domin Yakar Cin Hanci Da Rashawa, Inji Rundunar Sojin Naijeriya

*Rundunar ta bayyana hakan ne a yayin da shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya kai mata ziyara a hedikwatar ta dake Abuja a jiya Juma'a.

*Tsohon shugaban hukumar EFCC Nuhu Ribadu ya ce Farida Waziri na daga cikin wadanda suka yi ruwa sukai tsaki wajen ganin hukumar ba ta cimma burinta ba na ganin duk wanda ya ta ba kudin gwamnati ya dawo dashi.

*Ribadu Ya ce tsohon ministan Shari'a Micheal Aaondoka, da Mai shari'a Ben Nwabueze suma suna gaba gaba wajen ganin ba'a samu nasara ba duk da kokarin da hukumar tayi a wancan lokacin.

*Bai Kamata A Sanya Ido Kan Kayan Lefena Ba, Inji 'yar Shugaban Naijeriya  Zahra Buhari

*Shugaban Kasar Gambia, Yahya Jammeh Ya Fadi Zabe Bayan Ya Yi Shekaru 22 A Kan karagar Mulki

*Yahya Jammeh ya fadi zaben shugabancin kasar ne, inda abokin hamayyarsa Adama Barrow ya doke shi.

*Mista Barrow ya samu kuri'u dubu 263,515, yayin da shi kuma Jammeh ya samu kuri'u dubu 212,099, kamar yadda hukumar zaben kasar ta bayyana.

*Shugaban na Gambia, Adama Barrow wanda aka haifa A Adama Barrow a shekarar 1965 a wani kauye da ke kusa da garin kasuwancin nan na Basse a gabashin Gambia, kuma ya zauna a birnin London a matsayin mai jiran kanti.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
03/Rabi-Al'Awwal/1438
03/December/2016

Friday, 2 December 2016

LABARAI A TAKAICE


*Gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Geidam a jiya Alhamis ya tallafa keyar daya daga cikin kwamishinonin sa zuwa gida sakamakon kama shi da laifin kwarara barci har da munshari a lokacin da gwamnan yake gabatar da kasafin kudi na bana a gaban majalisar dokokin jihar.

*Rahotanni sun nuna cewa kwamishinan ya fara sharara barcin ne a daidai lokacin da gwamnan yake karanto jawabai kan kasafin kudin.

*Kimanin Naira Tiriliyan 7.2 Aka Ware Don Kasafin 2017
Ministan kasafi da tsare-tsare Udoma Udoma, shi ya shaida hakan ga manema labarai.

*Mutane 5000 ne yan gudun hijira a sansanoni dabam dam da ke jihar Borno suke dauke da cutar Kanjamau wato HIV.

*Kamar yadda wani malamin lafiya, Hassan Mustapha ya sanar ma kamfanin Dillancin Labarai, ya ce sama da 1000 daga cikin masu dauke da cutan suna sansanin gdun hijiranne da ke Bama, 3000 kuma suna Gwoza.

*Ya ce mafi yawa daga cikin masu dauke da cutan ba sa so asani. sannan kuma ya koka da yadda gwamnati bata ba su cikakken kula.

*Farfesa Wole Soyinka ya ce ya cika alkawarin lalata katin shaidar sa ta zaman Amurka kamar yadda ya yi alkawari matukar Donald Trump ya lashe zaben kasar.

*Kasar Gambia da ke yankin Afurka ta yamma na gudanar da zaben shugaban kasa inda shugaba Yahaya Jameh ke fuskantar adawar wani dan kasuwar gidaje Adama Barrow.

*Kasar dai da ke iyaka daya da Senegal ta kashe layukan buga waya ketare da na yanar gizo don lamuran zaben.

*Jameh dai ya ce Allah zai ba shi damar lashe zabe a karo na biyar.

*Adama Barrow na da farin jini tsakanin 'yan adawa.
Kasar Ghana ma za ta gudanar da babban zabe a ranar 7 ga watan nan.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
02/Rabi-Al'Awwal/1438
03/December/2016

Thursday, 1 December 2016

LABARAI A TAKAICE


*Dakatar da umurnin kara farashin sayan damar shiga yanar gizo da hukumar kula da kafafen sadarwar Najeriya NCC ta yi, ya kawo ajiyar zuciya ga wadanda na zanta da su.

*Tun farko dai NCC ta umurci manyan kamfanonin sadarwar da ke samarda damar shiga yanar gizo baya ga aika yan gajerun sakonni da buga waya,su kara farashin sayar da maaunin shiga  yanar DATA don ba wa kananan kamfanoni damar cin riba a kasuwar sadarwar Najeriya.

*Shugaban ma'aikatar kula da karban haraji na kasa, 'Federal Inland Revenue Service FIRS' Tunde Fowler ya ce daga yanzu mai neman fasfo din kasar Najeriya sai ya nuna takardar shidan biyan haraji kafin ayi masa fasfo.

*Fowler ya fadi hakan ne ranar Litinin a wani taro da ya gudana a garin Abuja.

*Ya yabi jihar Kano da Legas akan kokarin da sukeyi wajen inganta tara haraji a jihohinsu.

*Shugaban Rundunar Sojan kasa, Janar Tukar Burutai ya bayyana cewa dukkan manyan hafsoshin soja za su tafi Maiduguri don gudanar da bukukuwan Kirismeti da na sabuwar shekara tare da sojojin da ke yaki da Boko Haram.

*Ya kuma tabbatar da cewa sojojin sun fara kutsawa cikin kukurmin dajin Sambisa wanda nan maboya ta karshe na mayakan Boko Haram wanda a cewarsa, wannan shi ne mataki na karshe na murkushe mayakan tare da kwato mutanen da suka yi garkuwa da su

*A zaman jiya Laraba ne Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki ya karanto wasikar da Mista Omogunwa, Sanata mai wakiltar shiyyar Jihar Ondo ta Kudu ya aikawa majalisar na sanar da ficewarsa daga PDP zuwa APC.

*Tun kafin zaben gwamnan jihar da aka yi a ran Asabar da ta wuce, a dalilin rabuwar kai a PDP.

*Daga nan sai shugaban marasa rinjaye na majalisar, Sanata Godswill Akpabio ya mayar da martani da cewar babu wata rabuwar kai a PDP, wannan ya haifar da hayaniya a majalisar tsakanin sanatocin PDP da na APC wanda suke yi wa sabon sanatan maraba.

*Daga nan sai sanatocin PDP karkashin jagorancin Sanata Akpabio suka fice daga zaman majalisar

*Majalisar Dokokin Nijeriya na kokarin yin doka da za ta rage yawan shekarun masu iya tsayawa takara saboda matasa su samu damar taka rawa a harkokin gudanar da Nijeriya.

*Dokar a yanzu haka ta samu karatu na biyu a majalisar dokokin, dokar na neman a rage shekarun mai tsayawa takarar shugaban kasa daga shekaru arba'in, zuwa talatin, na kujeran Gwamna kuma daga shekaru talatin da biyar zuwa talatin, na 'yan majalisar tarayya dana jihohi a rage daga shekaru dalati zuwa ashirin da biyar.

*Binciken da wassu kwararru na duniya su ka gudanar ya gano wani bututun aika makamai da Iran ta shunfuda da ke samawa 'yan tawayen Shi'a na Houthi makamai.

*Bututun dai na shunfude ne daga Iran ya bi ta Somaliya zuwa Yaman.

*Iran dai ta sha musanta taimakawa 'yan tawayen Yaman 'yan Shi'a da ke yakar halattacciyar gwamnatin kasar ta Abed Rabbo Mansur Hadi.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media 
01/Rabi-Al'Awwal/1438
01/December/2016

Wednesday, 30 November 2016

MAULIDI A MAHANGAR MUSULUNCI (II)


Ibrahim Jalo Jalingo

Akwai shubuhohin da masu shar'anta Idin maulidi ke
ambatawa a matsayin hujjojin da ke wajabta Idin maulidi ko
halatta shi, saboda haka In sha Allahu Ta'ala za mu ambaci
uku daga cikinsu a wannan rubutu namu (kashi na 2)
sannan mu ba da amsarsu, saboda burin da muke da shi
na tsarkake addinin Musulunci daga wannan bidi'ah mai
kama da bidi'ar Kirsimeti wacce Kiristoci ke yi cikin ko wace
shekara, haka nan saboda burinmu na cewa: dukkanmu mu
al'ummar Musulmi mu hadu a kan daidai, mu gudu tare mu
tsira tare. Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce cikin
ingantaccen hadithinsa:
(( ﻻ ﻳﺆﻣﻦ ﺍﺣﺪﻛﻢ ﺣﺘﻰ ﻳﺤﺐ ﻻﺧﻴﻪ ﻣﺎ ﻳﺤﺐ ﻟﻨﻔﺴﻪ )).
Ma'ana: ((Dayanku ba zai yi imani ba har sai ya so wa
dan'uwansa abin da yake so wa kansa)).
****************************
SHUBUHA TA FARKO:
Shubuha ta farko: Suka ce: Allah ne da kansa Ya yi umurni
da yin bukin Idin maulidi cikin Suratu Yunus aya ta 58 a
inda ya ce:-
{ ﻗﻞ ﺑﻔﻀﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺑﺮﺣﻤﺘﻪ ﻓﺒﺬﻟﻚ ﻓﻠﻴﻔﺮﺣﻮﺍ ﻫﻮ ﺧﻴﺮ ﻣﻤﺎ ﻳﺠﻤﻌﻮﻥ }.
Ma'ana: {Ka ce: Ku yi farin ciki da falalar Allah da
rahamarSa shi ne mafi alheri daga abin da suke tarawa}.
Suka ce: Annabi shi ne falalar Allah da rahamarSa, Allah
kuwa Ya ce a yi farin ciki da falalarSa da kuma rahamarSa,
farin cikin kuwa yana nufin shirya bukin maulidinsa ne ahi
Annabi mai tsira da amincin Allah, ke nan shirya bukin
maulidi ko wace shekara bin wani umurni ne na musamman
Wanda ya fito daga Allah madaukakin Sarki, rashin bin
wannan umurni kuwa lalle saba wa Shi Allah Madaukakin
Sarki ne!!!
Amsa a kan wannan shubuha tana da rassa da yawa:-
Na farko: sai a ce da su: Fassara wannan ayar da cewa
tana umurni ne da yin bukin maulidi fassara ce da take
Kama da fassarar Baatiniyyah da gulaatus suufiyyah da
suke yi wa wasu nassoshin Alkur'ani mai girma, kamar
yadda suka fassara ayah ta 25 cikin Suratu Nuuhin inda
Allah Yake magana game da mutanen Annabi Nuhu Ya ce:-
{ ﻣﻤﺎ ﺧﻄﻴﺌﺎﺗﻬﻢ ﺃﻏﺮﻗﻮﺍ ﻓﺄﺩﺧﻠﻮﺍ ﻧﺎﺭﺍ ﻓﻠﻢ ﻳﺠﺪﻭﺍ ﻟﻬﻢ ﻣﻦ ﺩﻭﻥ ﺍﻟﻠﻪ
ﺃﻧﺼﺎﺭﺍ}.
Ma'ana: {Saboda laifukansu na ganganci aka nitsar da su
(cikin ruwa) sannan aka sanya su a Wuta. Saboda haka ba
su sama wa kansu wanin Allah a matsayin Mai taimako ba}.
Sai suka ce: ma'anar ayar ita ce: Allah Yana nufin cewa
abin nan da suka yi wa Annabi Nuhu na saba wa umurnin
da Allah ya aiko shi da shi shi ne ya Kai su ga yin nitso cikin
tekunan sanin Allah! Watau dai abin nan da suka yi na saba
wa Annabi Nuhu babu wani zunubi a cikinsa kamar yadda
wasu ke tsammani!!
Suka kuma fassara inda Allah Ya ce cikin Suratul Israa'i aya
ta 23:-
{ ﻭﻗﻀﻰ ﺭﺑﻚ ﺍﻻ ﺗﻌﺒﺪﻭﺍ ﺍﻻ ﺇﻳﺎﻩ }.
Ma'ana: {UbangijinKa Ya hukunta cewa kada ku bauta wa
kowa sai Shi}.
Sai suka ce: Ma'anar ayar ita ce: "Ubangijinka Ya riga ya
kaddara muku cewa ba za ku yi wata bauta ba face Allahn
ne dai kuka bautawa! saboda haka babu wani abu a
duniyan da za ku bautawa face a hakikanin lamari Allah ne
Shi kadanSa kuka bautawa!!
Suka kuma fassara inda Allah ya ce cikin Suratul Hijri aya ta
99 :-
{ ﻭﺍﻋﺒﺪ ﺭﺑﻚ ﺣﺘﻰ ﻳﺄﺗﻴﻚ ﺍﻟﻴﻘﻴﻦ }.
Ma'ana: {Kuma ka bauta wa Ubangijinka har mutuwa ta zo
maka}. Sai suka ce: ma'anarsa shi ne: shi Dan Adam ana
umurtansa da yin ibada ne har zuwa lokacin da ya kai
matsayin Yakini da sanin Allah, da zarar ya kai wannan
matsayi ayyukan ibada sun fadi ke nan a Kansa!!
Reshe na biyu: Sai a ce da su: Wani malami ne cikin
maluman tafsiiri daga magabata Salafus Salih ya fassara
wannan ayar da irin wannan fassara taku ta cewa: Ana
nufin yin bukin maulidi ne da wannan ayah? Lalle muna
tabbatar wa masu karatun wannan rubutu namu cewa: har
abada yan bidi'ar maulidi ba za su iya kawo koda malamin
tafsiiri daya ba daga cikin Salafus Salih da ya fassara
wannan ayar da cewa tana nufin umurni ne da yin bukin
maulidi.
Rashe na uku: Sai a ce da su: In dai har wannan ayar tana
nufin yin bukin maulidi ne to kuwa lazimin hakan shi ne:
Sahabbai da sauran shugabannin Al'ummah kamar su Abu
Hanifah, da Mali, da Shafi'ii da Ahmad, da sauransu
dukkansu ke nan sun nuna kiyayya da rashin kauna ga
Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah, sannan dukkansu
ke nan sun saba wa umurnin Allah da ya zo cikin wannan
aya ta 58 da ta zo cikin Suratu Yunus, domin har suka
gama rayuwarsu babu wani daga cikinsu da ya taba yin
bukin maulidi! Duk kuwa wanda ya ce: Sahabbai, da
Taabi'ai da sauran shugabannin Al'ummah ba sa kaunar
Manzon Allah ko ba sa girmama shi, ba sa bin umurnin
Allah da ya zo cikin Alkur'ani na girmama shi to lalle
wannan ya bace bata bayyananniya! Lazimin wannan kuwa
shi ne: Yan bukin maulidi su ne batattu saboda lazimin
maganarsu ta tabbatar da cewa Sahabban Manzon Allah da
Taabi'ai, da Taabi'utttaabi'ina da sauran Sugabannin
Al'ummah batattu ne, saboda ba su yi aiki da wannan aya
ba:-
{ ﻗﻞ ﺑﻔﻀﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺑﺮﺣﻤﺘﻪ ﻓﺒﺬﻟﻚ ﻓﻠﻴﻔﺮﺣﻮﺍ ﻫﻮ ﺧﻴﺮ ﻣﻤﺎ ﻳﺠﻤﻌﻮﻥ }.
Reshe na hudu: Sai a ce da su: Dukkan abin da bai zama
nuna soyayya ba ne ga Manzon Allah a zamanin Shabbai
da Taabi'ai da sauran Shugabanni kamar Imam Malik, da
Abu Hanifah, da Shaa'i'ii, da Ahmad, to ba zai zama nuna
soyayya ga Manzon Allah ba a wannan zamani namu.
Idan kuma wani daga cikin yan bukin maulidi ya fidda
jahilcinsa a fili ya ce: Ai Suyuutii ya halatta yin bukin
maulidi ! Sai a ce da shi: Ai shi Suyuutii ba ya daga cikin
wadanda ake kira Magabata cikin Musulunci, a'a yana cikin
jerin yan baya ne, domin ya mutu ne a shekara ta 911 na
hijira watau yau shekara 523 ke nan da suka wuce. Kuma
shi Suyuutii a wurin Malamai mutum ne da yake kama da
mai tara kirare cikin dare, ya kan dauki kirare sannan ya kan
dauki macizai da kunamu, saboda wannan idan har ya
halatta bidi'ar bukin maulidi ba wani abin mamaki ba ne a
gurin Malamai, domin ya yi ma abin da ya fi hakan muni da
ban mamaki, saboda Mai littafin Rimaahu Hizbir Rahiim ya
ce a cikin wannan littafi nasa wanda aka buga tare da
littafin Jawaahirul Ma'aa'nii 1/199 ya ce shi Suyuutii ya ce
cikin littafinsa mai suna :-
ﺗﻨﻮﻳﺮ ﺍﻟﺤﻠﻚ ﻓﻲ ﺇﻣﻜﺎﻥ ﺭﺅﻳﺔ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﻭﺍﻟﻤﻠﻚ
"Ya ga Annabi kuma ya yi taro da shi a farke har sau
saba'in da wani abu"! Mai irin wannan magana mara tushe
don ya ce bukin maulidi halal ne mene abin mamaki a cikin
maganarsa? Allah Ya tsare daga fadawa cikin ko wace irin
halaka. Ameen.
SHUBUHA TA BIYU:
Shubuha ta biyu suka ce: Duk wata ni'ima da Allah Ya yi wa
mutum, to dole ne ya gode aw Allah a kanta, saboda lokacin
da Annabi ya dawo Madinah ya ga Yahudawa suna azumi a
ranar goma ga watan Muharram sai shi Annabi mai tsira da
amincin Allah ya tambaye su ya ce: Me ya sa kuke azumin
wannan rana? Sai suka ce masa: Wannan rana ce da Allah
Ya tsirar da Annabi Musa tare da jama'arsa, kuma Ya
halakar da Fir'auna tare da mutanensa cikin teku, shi ya sa
Annabi Musa yake azumin wannan rana saboda gode wa
Allah mu ma shi ya sa muke yin azuminsa, sai Annabi mai
tsira da amincin Allah Ya ce: Mun fi ku cancantar yin abin
da Annabi Musa ya yi, saboda haka ya yi azumin wannan
ranar kuma ya umurci Musulmi da su yi azuminsa. A nan
muna ganin babu wata ni'ima da ta kai haihuwar Annabi
Muhammad mai tsira da amincin Allah, kuma ko shakka
babu wannan ni'ima za ta wajabta mana gode aw Allah,
wannan kuwa shi ya sa muke yin bukin maulidi saboda
nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki.
Amsa a kan wannan shubuha tasu sai a ce da su: Lalle
gaskiya ne ni'imomin Allah suna wajabta godiyar Allah a
kan bayinSa, to amma hakika ni'ima mafi girma a cikin
Musulunci ita ce:Ni'imar ba wa Annabi mai tsira da amincin
Allah Manzanci, ba. Wai ni'imar haihuwar sa ba, domin
Alkur'ani mai girma bai yi nuni da ishara zuwa haihuwarsa
koda sau daya ba, to amma ya yi nuni da ishara zuwa ga
manzancinsa ba sau daya ba ba sau biyu ba! Allahl
Madaukakin Sarki Ya ce cikin Suratu Aa'li Imraan aya ta
164:-
{ ﻟﻘﺪ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﺇﺫ ﺑﻌﺚ ﻓﻴﻬﻢ ﺭﺳﻮﻻ ﻣﻦ ﺍﻧﻔﺴﻬﻢ ﻳﺘﻠﻮ
ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺁﻳﺎﺗﻪ ﻭﻳﺰﻛﻴﻬﻢ ﻭﻳﻌﻠﻤﻬﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺤﻜﻤﺔ }.
Ma'ana: {Hakika Allah Ya yi babbar falala ga muminai
domin Ya aika da Manzo daga ainihinsu yana karanta musu
ayoyinSa Yana tsarkake su yana karantar da su Littafi da
Hikima}. A nan Allah bai ce: domin an haifi wani Manzo
daga cikinsu ba, a'a sai Ya ce: Domin an aiko wani manzo.
Wannan shi ne halin da za ku tarar game da ko wane Manzo
daga cikin manzannin Allah Madaukakin Sarki, watau abin
himmantuwa game da shi shi ne aiko shi ba wai ranar
haihuwarsa ba, kamar dai yadda Allah Madaukakin Sarki ya
ce cikin Suratul Bakara aya ta 213:-
{ ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺃﻣﺔ ﻭﺍﺣﺪﺓ ﻓﺒﻌﺚ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻨﺒﻴﻴﻦ ﻣﺒﺸﺮﻳﻦ ﻭﻣﻨﺬﺭﻳﻦ ﻭﺍﻧﺰﻝ
ﻣﻌﻬﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﺑﺎﻟﺤﻖ ﻟﻴﺤﻜﻢ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻴﻤﺎ ﺍﺧﺘﻠﻔﻮﺍ ﻓﻴﻪ }.
Ma'ana: {A da mutane sun kasance al'umm ce guda daya,
sai Allah Ya aiko Annabawa suna masu bishara suna masu
gargadi, kuma Ya saukar da Littafi da gaskiya tare da su'
domin ya yi hukunci tsakanin mutane cikin abin da suka
Saba aw juna cikinsa}. Kun gani a nan' da dai mayar da
wata rana Idi da sunan addini halal ne cikin addinin
Musulunci, to da kuwa marar da aka aiko Manzon Allah mai
tsira da amincin Allah Idi shi ne ya fi.
Sannan kuma game da azumin da shi Annabi mai tsira da
amincin Allah ya yi na ranar Aashuuraaa to fa dole ne mu
sani cewa: Shi fa Annabi mai tsira da amincin Allah shi ne
mai shar'antawa kuma mai isar da sako daga Ubangijinsa
zuwa ga sauran mutane, saboda haka ba ya halatta a gare
mu mu yi kiyasin wani mutum a kan shi, har na mu fada
cikin wata bidi'a, domin abin da ake bukata ga dukkan
al'ummar Musulmi shi ne: Su zama masu bi a koda yaushe
ba wai masu kirkiro bidi'o'i ba. Sannan kuma shi azumi ai
kishiyar bukin Idi ne saboda azumi yana nufin hana sa kai
cin abinci shi kuwa bukin Idi yana nufin ciyar da kai abinci
ne, saboda haka ta kaka za a kira yin azumi bukin Idi?
SHUBUHA TA UKU:
Shubuha ta uku: suka ce: Annabi mai tsira da amincin Allah
ya kasance yana azumi a ko wane ran litinin, a lokacin da
Sahabbai suka tambaye shi: Don me yake azumi a wannan
rana? Sai ya ce: yana azumtar ko wace litinin ne saboda a
ran litinin ne aka haife shi.
Yan maulidi suka ce wannan yana nufin ke nan Annabi mai
tsira da amincin Allah shi ma yana bukin maulidi watau
yana bukin ranar haihuwarsa.
Amsa a kan wannan shubuha ta yan maulidi sai a ce da su:-
Na daya: Musulmi ba sa musun halaccin azumin ranar
litinin da kuma falalarsa, haka ma azumin ranar alhamis da
falalarsa, to amma shi wannan azumin aka yi shi ne cikin
dukkan kwanakin litinin da alhamis na shekara, ba wai sau
daya ne ba kawai ake yin shi cikin shekara, kamar yadda
masu yin bidi'ar maulidi suke yin shi sau daya cikin
shekara.
Na biyu: lalle kiyasta bukin maulidi a kan azumin ranar
litinin da ake yi cikin ko wane mako, kiyasin abin da yake
bidi'ah ne a kan bin da yake Sunnah, wannan kuwa Kiyasi
ne batacce.
Na uku: lalle inda su masu bukin maulidi suna son koyi ne
da Annabi mai tsira da amincin Allah cikin abin da shi
Annabin ya yi a ranar haihuwarsa, to da sai su wadatu da
abin da shi Annabi mai tsira da amincin Allah ya wadatu da
shi, watau sai su rika yin azumi cikin ko wace ranar litinin,
ba wai su rika bukin maulidi cikin ko wace ranar gama sha
biyu ga watan Rabi'ul Awwal ba, saboda shi Manzon Allah
mai tsira da amincin Allah bai yi maulidi a ranar goma sha
biyu ga watan Rabi'ul Awwal ba duk kuwa da cewa yana
damar yin hakan in da yin hakan ya dace da Shari'ar
Musulunci, to amma da yake hakan bai dace da Shari'ar
Musulunci sam bai yi hakan ba, abin kawai aka sani ya yi
shi ne: Azumin ranar litinin cikin ko wane mako. Ke nan
wannan zai wajabta wa yan bukin maulidi in har dai suna
son Annabi suna kuma girmama shi suna kaunar bin
hanyar da ya bi, su bar yin bukin maulidi a ranar goma sha
biyu ga watan Rabi'ul Awwal su koma yin azumin ranar
litinin ko wane mako, da kuma ranar alhamis ko wane
mako.
Allah Madaukakin Sarki muke roko da Ya tausaya wa
al'ummarmu Ya cusa musu son AnnabinSa mai tsira da
amincin Allah tare da son bauta maSa ta hanyar sunnar
Annabin naSa ba wai ta hanyar bidi'ar da Shaidan ya
kawata musu ba. Ameen.

LABARAI A TAKAICE


*Hafsan Hafsoshin sojojin kasan Najeriya Laftanar Janar Yusuf Buratai ya ce dakarun sojan Najeriya na dannawa cikin dajin Sambisa don rugurguza tungar 'yan Boko Haram.

*Buratai da ke magana a Abuja wajen wani taro yabawa yunkurin sojoji,ya ce wannan yunkuri na da zummar kakkabe burbudin 'yan Boko Haram da ke makale a dajin.

*Dama an samu kwato duk garuruwan da a da Boko Haram su ka kwace da kafa haramtacciyar daular 'yan ta'adda masu zubar da jinin al'umma ba bisa ka'idar kowacce shari'a ba.

*Majalisar dokokin jihar Katsina ta kafa wani kwamiti wanda zai bincike zargi zargen da ake yi na karuwar ayyukan luwadi da madigo a tsakanin daliban da ke makarantun kwana a duk fadin jihar.

*Haka ma, majalisar za ta fadada binciken a kan kwalejin kimiyya da fasaha ta Hassan Usman Katsina mallakar gwamnatin jihar inda majalisar ta kuma tsara bullo da wani shiri na wayar da kan dalibai kan illar dabi'ar Luwadi da madigo.

*Majalisar tarayya ta amincewa Shugaban. Kasa, Muhammad Buhari kan bukatar da ya gabatar majalisar na neman yin Sauyi a kasafin kudin 2016 ta yadda zai karkatar da wasu kudi da aka tanada tun farko don shirin tallafi na musamman zuwa wajen manyan ayyuka.

*A makon da ya gabata ne majalisar ta ki amincewa da bukatar bisa hujjar cewa Shugaban bai bi hanyar da ta dace ba wajen gabatar da bukatar. Sai dai kuma majalisar ta yi karin Naira Bilyan 33 daga bukatar shugaban na shirin yin amfani da Naira Bilyan 180 daga cikin Bilyan 500 da aka ware don shirin tallafawa marasa galihu.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
01/Rabi-Al Awwal/1438
30/November/2016

Tuesday, 29 November 2016

MAULIDI A MAHANGAR MUSULUNCI [1]

Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

Yau Talata 29/2/1438 H wanda ya dace da 29/11/2016 M
muna dab da kaiwa goma sha biyu ga watan Rabii'ul
Awwal, kuma kamar yadda aka sani ne cewa wannan rana
ta sha biyu ga Watan Shawwal ita ce ranar da wasu ke
bukin ranar haifuwar Annabi Muhammad mai tsira da
amincin Allah, saboda neman lada da falala a wurin Allah,
duk kuwa da cewa rikon wannan rana a matsayin Idi bidi'a
ce wurin dukkan Maluman Musulunci! Haka dai Shaidan
yake batar da mutane ta hanyar kawata musu wani abin da
ba Shari'ah ba ne har su rika ganin shi tamkar abin da yake
Shari'ah ne! Allah yana cewa cikin Suratu Faatir aya ta 8:-
(( ﺃﻓﻤﻦ ﺯﻳﻦ ﻟﻪ ﺳﻮﺀ ﻋﻤﻠﻪ ﻓﺮﺍﻩ ﺣﺴﻨﺎ ﻓﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻀﻞ ﻣﻦ ﻳﺸﺎﺀ ﻭﻳﻬﺪﻱ
ﻣﻦ ﻳﺸﺎﺀ ﻓﻼ ﺗﺬﻫﺐ ﻧﻔﺴﻚ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺣﺴﺮﺍﺕ ﺍﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻢ ﺑﻤﺎ
ﻳﺼﻨﻌﻮﻥ)).
Ma'ana: ((yanzu wanda aka kawata masa mummunan
aikinsa har ya gan shi wani abu Mai kyau "yana daidai da
waninsa?" saboda haka lalle Allah yana batar da wanda
yake so, kuma ya shiryar da wanda yake so, kada ranka ya
halaka a kansu saboda bakin ciki. Lalle Allah Masani ne ga
abin da suke sana'antawa)).
Mu a nan, a bisa dogara da ayah ta 104 a cikin Suratu Aali
inda Allah Ya ce:-
(( ﻭﻟﺘﻜﻦ ﻣﻨﻜﻢ ﺃﻣﺔ ﻳﺪﻋﻮﻥ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﻭﻳﺄﻣﺮﻭﻥ ﺑﺎﻟﻤﻌﺮﻭﻑ ﻭﻳﻨﻬﻮﻥ ﻋﻦ
ﺍﻟﻤﻨﻜﺮ ﻭﺃﻭﻟﺌﻚ ﻫﻢ ﺍﻟﻤﻔﻠﺤﻮﻥ )).
Ma'ana: ((A samu wata al'umma daga cikinku da za ta yi
kira zuwa ga alheri, sannan ta umurni da abin da Shari'ah ta
sani, kuma ta yi hani ga abin da Shari'ah bata sani ba. To
su wadannan Al'umma sune masu rabauta)). Da kuma
dogara kan aya ta 78, da 79 cikin Suratul Maa'idah inda
Allah Madaukaki ya yi maga a kan Banuu Isaraa'iil ya ce:-
(( ﻟﻌﻦ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻛﻔﺮﻭﺍ ﻣﻦ ﺑﻨﻲ ﺍﺳﺮﺍﺋﻴﻞ ﻋﻠﻰ ﻟﺴﺎﻥ ﺩﺍﻭﺩ ﻭﻋﻴﺴﻰ ﺍﺑﻦ
ﻣﺮﻳﻢ ﺫﻟﻚ ﺑﻤﺎ ﻋﺼﻮﺍ ﻭﻛﺎﻧﻮﺍ ﻳﻌﺘﺪﻭﻥ . ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻻ ﻳﺘﻨﺎﻫﻮﻥ ﻋﻦ ﻣﻨﻜﺮ
ﻓﻌﻠﻮﻩ ﻟﺒﺌﺲ ﻣﺎ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻳﻔﻌﻠﻮﻥ )).
Ma'ana: ((An la'anci wadanda suka kafirta daga Banu
Isaa'iil a bisa harshen Daawuuda da Isa Dan Maryam,
saboda irin yadda suka yi sabo, suka kasance suna ketare
iyaka. Suka kasance ba sa hana juna yin mummunan aikin
da suke aikatawa. Wallahi abin da suka kasance suna
aikatawa ya yi muni)). Da kuma dogara kan hadithin da
Imam Muslim ya ruwaito hadithi na 49 inda Annabi mai tsira
da amincin Allah yake cewa:-
(( ﻣﻦ ﺭﺃﻯ ﻣﻨﻜﻢ ﻣﻨﻜﺮﺍ ﻓﻠﻴﻐﻴﺮﻩ ﺑﻴﺪﻩ ﻓﺎﻥ ﻟﻢ ﻳﺴﺘﻄﻊ ﻓﺒﻠﺴﺎﻧﻪ ﻓﺎﻥ ﻟﻢ
ﻳﺴﺘﻄﻊ ﻓﺒﻘﻠﺒﻪ ﻭﺫﻟﻚ ﺍﺿﻌﻒ ﺍﻻﻳﻤﺎﻥ )).
Ma'ana: ((Wanda duk ya ga munkari daga cikinku sai ya
jirkita shi da hannunsa, in kuma ba zai iya ba, sai ya jirkita
shi da harshensa, in kuma ba zai iya ba sai ya jirkita shi da
zuciyarsa, wannan shi ne mafi raunin Imani)). Da kuma
dogara kan maganar Sahabin Annabi Abdullahi Dan Mas'ud
Allah ya kara masa yarda, wacce ta zo cikin littafin Ibnu
Wadh,dhah shafi na 11 da littafin Ali'itisaam na Imamush
Shaatibii 1/107 inda ya ce:-
(( ﺍﺗﺒﻌﻮﺍ ﻭﻻ ﺗﺒﺘﺪﻋﻮﺍ ﻓﻘﺪ ﻛﻔﻴﺘﻢ )).
Ma'ana: ((Ku bi -abin da Annabi ya zo da shi- kada ku kirkiri
bidi'ah, domin an gama muku kome -na addini-)). Dankuma
dogara har yanzu a kan maganar shi Sahabi Abdullahi Dan
Mas'uud wacce ta zo cikin littafin Ibnu Wadh'dhah shafi na
11 da kuma Sunanud Daarami 1/68-69 a inda ya ce lokacin
da ya wuce wani mai wa'azi a cikin masallaci yana ce wa
mutane: ku yi Subhanallah kafa goma, ku yi la'laha illalah
kafa goma, sai ya ce da su:-
(( ﻭﻳﺤﻜﻢ ﻳﺎ ﺃﻣﺔ ﻣﺤﻤﺪ ﻣﺎ ﺍﺳﺮﻉ ﻫﻠﻜﺘﻜﻢ ! ﻫﺆﻻﺀ ﺻﺤﺎﺑﺔ ﻧﺒﻴﻜﻢ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻣﺘﻮﺍﻓﺮﻭﻥ ﻭﻫﺬﻩ ﺛﻴﺎﺑﻪ ﻟﻢ ﺗﺒﻞ ﻭﺃﺗﻴﺘﻪ ﻟﻢ ﺗﻜﺴﺮ ﻭﺍﻟﺬﻱ
ﻧﻔﺴﻲ ﺑﻴﺪﻩ ﺍﻧﻜﻢ ﻟﻌﻠﻰ ﻣﻠﺔ ﻫﻲ ﺃﻫﺪﻯ ﻣﻦ ﻣﻠﺔ ﻣﺤﻤﺪ ﺍﻭ ﻣﻔﺘﺘﺤﻮﺍ ﺑﺎﺏ
ﺿﻼﻟﺔ . ﻗﺎﻟﻮﺍ ﻳﺎ ﺃﺑﺎ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﻣﺎ ﺍﺭﺩﻧﺎ ﺍﻻ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﻗﺎﻝ ﻭﻛﻢ ﻣﺮﻳﺪ
ﻟﻠﺨﻴﺮ ﻟﻦ ﻳﺼﻴﺒﻪ ﺍﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺍﻥ ﻗﻮﻣﺎ
ﻳﻘﺮﺀﻭﻥ ﺍﻟﻘﺮﺍﻥ ﻻ ﻳﺠﺎﻭﺯ ﺗﺮﺍﻗﻴﻬﻢ ﻭﺍﻳﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﺎ ﺍﺩﺭﻱ ﻟﻌﻞ ﺍﻛﺜﺮﻫﻢ ﻣﻨﻜﻢ
ﺛﻢ ﻭﻟﻰ ﻋﻨﻬﻢ )).
Ma'ana: ((kaitonku ya ku al'ummar Muhammad mamakin
saurin halakarku! Wadannan Sahabban annabinku ne mai
tsira da amincin Allah ga su nan da yawa, wadannan
tufafinsa ne ba su gama yagewa ba, wadannan butocinsa
ne ba su gama fashewa ba. Ina rantsuwa da Wanda raina
yake hannunsa lalle ne ku ko dai kuna kan wani addini ne
da ya fi addinin Muhammad shiriya ko kuwa ku masu bude
kofar bata ne. Sai suka ce wallahi baban Abdurrahman
babu abin da muke nufi sai alheri. Sai ya ce ai da yawa mai
son alheri ba zai taba samun sa ba. Lalle Manzon Allah mai
tsira da amincin Allah ya gaya mana cewa akwai wasu
mutane da za su rika karanta Alkur'ani amma kuma ba zai
wuce makogoronsu ba, Ina rantsuwa da Allah watakila mafi
yawansu daga cikinku suke. Daga nan sai ya juya ya bar
su)). Intaha. Da kuma dogara kan maganar babban Taabi'ii
Hasanul Basarii wacce ta zo cikin littafin Ibnu Wadh'dhah,
da littafin Alitisam na Shaatibii 1/111 inda ya ce: ((Mai yin
bidi'ah ba zai Kara kokari cikin azuminsa na bidi'ah ba, ko
sallarsa ta bidi'ah ba, face hakan ya nisantar da shi daga
Allah)).
Dogara kan wadannan ayoyi da hadithai da maganganun
Sahabbai da Taabi'ai da kuka ji su yanzu ne ya sa muke
gargadin Al'ummar Musulmi, muke hana su rikon ranar
haihuwar Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah a
matsayin ranar Idi, muke musu gargadin rikon bukin maulidi
a matsayin wani abu na addini da ake neman lada da shi a
wurin Allah Madaukakin Sarki!
Saboda abu ne tabbatacce wurin Maluman Musulunci cewa
Annabi Mai tsira da amincin Allah bai yi bukin maulidi ba,
Sahabbai ba su yi bukin maulidi ba, Taabi'ai ba su yi bukin
maulidi ba, Taabi'ut Taabi'in ba su yi bukin maulidi ba. Duk
kuwa abin da ba zama addini ba a zamanin Sahabbai, da
Taabi'ai, da Taabi'ut Taabi'in tare da kasancewar sababin
yin sa a lokacin nasu' da kuma ikon yin sa daga gare su
yana nan' amma kuma babu Wanda ya yi shi daga cikinsu,
to lalle wannan abin babu ta yadda za a yi ya zamanto
addini karbabbe a wurin na bayansu har zuwa tashin
Kiyama.
Yan'uwa Musulmi! Lalle shi rikon ranar maulidi a matsayin
Idi, da maida shi ranar buki, ba a fara yin shi ba cikin
wannan Al'umma sai cikin karni na hudu na hijirar Annabi
Mai tsira da amincin Allah' watau sai a cikin shekara ta dari
uku da settin da biyu (362). Sannan mutumin da ya fara yin
wannan buki na maulidi shi ne wani sarki dan Shi'ah
Fadimiyyah Mai suna Almu'izzu li Dininl Lah a garin
Alkahira' kamar yadda yake rubuce cikin littattafan
Musulunci da tarihi, da wasunsu, kuna iya duba wadannan
littattafan:-
ﺍﻟﻤﻮﺍﻋﻆ ﻭﺍﻻﻋﺘﺒﺎﺭ ﺑﺬﻛﺮ ﺍﻟﺨﻄﻂ ﻭﺍﻻﺛﺎﺭ ﻟﻠﻤﻘﺮﻳﺰﻱ ١/ ٤٩٠، ﻭﺻﺒﺢ
ﺍﻷﻋﺸﻰ ﻓﻲ ﺻﻨﺎﻋﺔ ﺍﻹﻧﺸﺎﺀ ﻟﻠﻘﻠﻘﺸﻨﺪﻱ ٣/ ٤٩٨، ﻭﺗﺎﺭﻳﺦ ﺍﻻﺣﺘﻔﺎﻝ
ﺑﺎﻟﻤﻮﻟﺪ ﺍﻟﻨﺒﻮﻱ ﻟﻠﺴﻨﺪﻭﺑﻲ ﺹ٦٩، ﻭﺃﺣﺴﻦ ﺍﻟﻜﻼﻡ ﻓﻴﻤﺎ ﻳﺘﻌﻠﻖ ﺑﺎﻟﺴﻨﺔ
ﻭﺍﻟﺒﺪﻋﺔ ﻣﻦ ﺍﻷﺣﻜﺎﻡ ﻟﻤﺤﻤﺪ ﺑﺨﻴﺖ ﺹ٤٤، ٤٥، ﻭﺍﻟﻤﺤﺎﺿﺮﺍﺕ ﺍﻟﻔﻜﺮﻳﺔ
ﻟﻠﺸﻴﺦ ﻋﻠﻲ ﻓﻜﺮﻱ ﺹ٨٤، ﻭﺍﻹﺑﺪﺍﻉ ﻓﻲ ﻣﻀﺎﺭ ﺍﻻﺑﺘﺪﺍﻉ ﻟﻠﺸﻴﺦ ﻋﻠﻲ
ﻣﺤﻔﻮﻅ ﺹ١٢٦، ﻭﺍﻟﺘﺎﺭﻳﺦ ﺍﻟﻌﺒﺎﺳﻲ ﻭﺍﻟﻔﺎﻃﻤﻲ ﻟﻠﺸﻴﺦ ﺍﺣﻤﺪ ﻣﺨﺘﺎﺭ
ﺍﻟﻌﺒﺎﺩﻱ ﺹ٢٦١، ٢٦٢ .
Almawaa'izu wa Litibaar na Maqriizii 1/490, da Subhul
A'ashaa na Qalqashandii 3/498, da Taariikhu Lihtifaali Bil
Maulidin Nabawii na Sanduubii shafi na 69, da Ahsanul
Kalam fi ma yataallaqu bis Sunnati wal Bidi'ati minal Ahkam
na Muhammad Bakhiit shafi na 44,45, da Almuhadharaatul
Fikriyyah na Ali Fikrii shafi na 84, da Al'ibdaa fi Madharri
Libtidaa na Ali Mahfuuz shafi na 126, da Taarikhul Abbaasii
wal Faatimii na Ahmad Mukhtaar Al'abbadii shafi na
261,262.
MALUMAN MUSULUNCI DABAN DABAN SUN HANA YIN
BUKIN MAULIDI:
Yan'uwa Musulmi! Lalle da yawa daga cikin maluman
Musulunci sun gargadi Al'umma sun hana su yin bukin
maulidi da rikon shi a matsayin wata ibadah da za a nemi
lada wurin Allah da ita, kuma sun bayyanar da cewa yin
bukin maulidi bidi'a ce kuma bata.
Daga cikin wadannan malamai akwai manya manyan
malumanmu na mazhabar Malikiyyah, kamar Ibnul Hajj
wanda ya rasu a shekarar hijira ta 732 watau yau da
rasuwarsa shekaru 702 ke nan da suka wuce, da kuma
Umarul Faakihaanii wanda ya rasu a shekarar hijira ta 734
watau yau da mutuwarsa shekara 700 ke nan da suka
wuce, da kuma Ibraahimush Shaatibii wanda ya rasu a
shekarar hijira ta 690 watau yau da rasuwarsa shekara 744
ke nan da suka wuce, da kuma uwa-uba Sheik Uthmanu
Dan Fodiyo wanda ya rasu a shekarar hijira ta 1234 watau
yau shekara 201 ke nan da rasuwarsa.
Amma Sheik Ibnul Hajj ga abin da yake cewa cikin littafin
Almudkhal 2/2, da 2/10-11 :-
(( ﻭﻣﻦ ﺟﻤﻠﺔ ﻣﺎ ﺍﺣﺪﺛﻮﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﻣﻊ ﺍﻋﺘﻘﺎﺩﻫﻢ ﺍﻥ ﺫﻟﻚ ﻣﻦ ﺍﻛﺒﺮ
ﺍﻟﻌﺒﺎﺩﺍﺕ ﻭﺍﻇﻬﺮ ﺍﻟﺸﻌﺎﺋﺮ ﻣﺎ ﻳﻔﻌﻠﻮﻧﻪ ﻓﻲ ﺷﻬﺮ ﺭﺑﻴﻊ ﺍﻻﻭﻝ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ
ﻭﻗﺪ ﺍﺣﺘﻮﻯ ﻋﻠﻰ ﺑﺪﻉ ﻭﻣﺤﺮﻣﺎﺕ ﺟﻤﻠﺔ ﻓﻤﻦ ﺫﻟﻚ ﺍﺳﺘﻌﻤﺎﻟﻬﻢ ﺍﻟﻤﻐﺎﻧﻲ
ﻭﻣﻌﻬﻢ ﺁﻻﺕ ﺍﻟﻄﺮﺏ(( ﺍﻟﻰ ﺍﻥ ﻗﺎﻝ: )) ﻭﺍﻥ ﺧﻼ ﻣﻨﻪ ﻭﻋﻤﻞ ﻃﻌﺎﻣﺎ ﻓﻘﻂ
ﻭﻧﻮﻯ ﺑﻪ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﻭﺩﻋﺎ ﺍﻟﻴﻪ ﺍﻻﺧﻮﺍﻥ ﻭﺳﻠﻢ ﻣﻦ ﻛﻞ ﻣﺎ ﺗﻘﺪﻡ ﺫﻛﺮﻩ ﻓﻬﻮ
ﺑﺪﻋﺔ ﺑﻨﻔﺲ ﻧﻴﺘﻪ ﻓﻘﻂ ﺇﺫ ﺍﻥ ﺫﻟﻚ ﺯﻳﺎﺩﺓ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻭﻟﻴﺲ ﻣﻦ ﻋﻤﻞ
ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺍﻟﻤﺎﺿﻴﻦ ﻭﺍﺗﺒﺎﻉ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺍﻭﻟﻰ ﺑﻞ ﺃﻭﺟﺐ ﻣﻦ ﺍﻥ ﻳﺰﻳﺪ ﻧﻴﺔ
ﻣﺨﺎﻟﻔﺔ ﻟﻤﺎ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻋﻠﻴﻪ ﻷﻧﻬﻢ ﺍﺷﺪ ﺍﺗﺒﺎﻋﺎ ﻟﺴﻨﺔ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺗﻌﻈﻴﻤﺎ ﻟﻪ ﻭﺳﻨﺘﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﻟﻬﻢ ﻗﺪﻡ ﺍﻟﺴﺒﻖ
ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺒﺎﺩﺭﺓ ﺍﻟﻰ ﺫﻟﻚ ﻭﻟﻢ ﻳﻨﻘﻞ ﻋﻦ ﺍﺣﺪ ﻣﻨﻬﻢ ﺍﻧﻪ ﻧﻮﻯ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﻭﻧﺤﻦ
ﻟﻬﻢ ﺗﺒﻊ ﻓﻴﺴﻌﻨﺎ ﻣﺎ ﻭﺳﻌﻬﻢ )).
Ma'ana: ((Yana daga cikin jumlar abin da suka kirkira na
bidi'o'i tare da akidar cewa hakan yana daga cikin manyan
ibadodi, kuma yana daga cikin alamomin Musulunci mafi
fita fili: abin nan da suke aikatawa cikin watan Rabii'ul
Awwal na bukin maulidi. Shi dai maulidi ya tattari
abubuwan haramun da yawa a dunkule, daga cikinsu akwai
wake-wake da suke yi tare da Kayan kade-kade .... To
amma idan yin maulidi ya wifinta daga yin wake-wake tare
da kayan kade-kade mai yin maulidin ya yi abinci kawai ya
yi nufin maulidi da shi ya kira yan'uwa zuwa cin abincin, to,
yin hakan ya zama bidi'ah saboda niyyar maulidin da ya yi,
domin niyyar maulidin kari ne a cikin Addini ba ya kuma
daga cikin ayyukan Salaf Magabata ba, bin Magabata kuwa
shi ne ya fi dacewa, kai shi ne ma wajibi da a ce mutum zai
kara wani abu sabanin abin da suka kasance a kansa,
domin su Magabata su ne suka fi kowa yin koyi da Manzon
Allah, kuma su ne suka fi kowa girmama shi da girmama
sunnarsa, kuma su suke da kafar rigaya wajen takawa
zuwa ga abin da yake alheri ne, babu kuma mutum daya da
ya ciro yin niyyar maulidi daga dayansu, mu kuwa sauran
Musulmi mabiya ne gare su, dukkan abin da ya wadatar da
su na addini shi ne zai wadatar da mu)).
Sannan Imamul Faakihaanii ya ce cikin Risalarsa ta maulidi
mai suna Almurid fil Kalaami alaa Hukmil Maulid :-
(( ﻻ ﺍﻋﻠﻢ ﻟﻬﺬﺍ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﺍﺻﻼ ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺏ ﻭﻻ ﺳﻨﺔ ﻭﻻ ﻳﻨﻘﻞ ﻋﻤﻠﻪ ﻋﻦ ﺍﺣﺪ
ﻣﻦ ﻋﻠﻤﺎﺀ ﺍﻻﻣﺔ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻫﻢ ﺍﻟﻘﺪﻭﺓ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﺍﻟﻤﺘﻤﺴﻜﻮﻥ ﺑﺂﺛﺎﺭ
ﺍﻟﻤﺘﻘﺪﻣﻴﻦ ﺑﻞ ﻫﻮ ﺑﺪﻋﺔ ﺍﺣﺪﺛﻬﺎ ﺍﻟﺒﻄﺎﻟﻮﻥ ﻭﺷﻬﻮﺓ ﻧﻔﺲ ﺍﻋﺘﻨﻰ ﺑﻬﺎ
ﺍﻻﻛﺎﻟﻮﻥ ﺑﺪﻟﻴﻞ ﺍﻧﺎ ﺍﺫﺍ ﺃﺩﺭﻧﺎ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻷﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﺨﻤﺴﺔ ﻗﻠﻨﺎ ﺍﻣﺎ ﺍﻥ ﻳﻜﻮﻥ
ﻭﺍﺟﺒﺎ ﺍﻭ ﻣﻨﺪﻭﺑﺎ ﺍﻭ ﻣﺒﺎﺣﺎ ﺍﻭ ﻣﻜﺮﻭﻫﺎ ﺍﻭ ﻣﺤﺮﻣﺎ ﻭﻫﻮ ﻟﻴﺲ ﺑﻮﺍﺟﺐ
ﺇﺟﻤﺎﻋﺎ ﻭﻻ ﺑﻤﻨﺪﻭﺏ ﻻﻥ ﺣﻘﻴﻘﺔ ﺍﻟﻤﻨﺪﻭﺏ ﻣﺎ ﻃﻠﺒﻪ ﺍﻟﺸﺮﻉ ﻣﻦ ﻏﻴﺮ ﺫﻡ
ﻋﻠﻰ ﺗﺮﻛﻪ ﻭﻫﺬﺍ ﻟﻢ ﻳﺄﺫﻥ ﻓﻴﻪ ﺍﻟﺸﺮﻉ ﻭﻻ ﻓﻌﻠﻪ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﻭﻻ ﺍﻟﺘﺎﺑﻌﻮﻥ ﻭﻻ
ﺍﻟﻌﻠﻤﺎﺀ ﺍﻟﻤﺘﺪﻳﻨﻮﻥ ﻓﻴﻤﺎ ﻋﻠﻤﺖ ﻭﻫﺬﺍ ﺟﻮﺍﺑﻲ ﻋﻨﻪ ﺑﻴﻦ ﻳﺪﻱ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻥ ﻋﻨﻪ
ﺳﺌﻠﺖ ﻭﻻ ﺟﺎﺋﺰ ﺍﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﻣﺒﺎﺣﺎ ﻻﻥ ﺍﻻﺑﺘﺪﺍﻉ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻟﻴﺲ ﻣﺒﺎﺣﺎ
ﺑﺈﺟﻤﺎﻉ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﻓﻠﻢ ﻳﺒﻖ ﺍﻻ ﺍﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﻣﻜﺮﻭﻫﺎ ﺍﻭ ﺣﺮﺍﻣﺎ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma'ana: ((Ban san wata hujja da za ta halatta yin maulidi
ba a cikin Alkur'ani da Sunnah, kuma ba a nakalto yin bukin
maulidi koda daga mutum daya ba cikin maluman Al'umma
wadanda su ne abin koyi a cikin Addini , kuma su ne ke riko
da maganganun magabata, kai, abin da dai yake ciki shi ne:
shi dai maulidi wata biri'ah ce da marasa aikin yi suka
kirkira kuma sha'awar son rai ce da masu cin dukiyar
mutane cikin karya suka runguma, saboda shi dai bukin
maulidi idan muka shimfida shi a kan hukunce-hukuncin
nan guda biyar sai mu ce: ko dai ya zama wajibi, ko kuwa
ya zama mustahabbi, ko kuwa ya zama mubaahi, ko kuwa
ya zama makruuhi, ko kuwa ya zama haraamun, to in mun
yi hakan za mu ga cewa shi dai ba wajibi ba ne bisa
Ijmaa'in Malamai, shi kuwa ba mustahabbi ba ne domin
abin da ake nufi da mustahabbi shi ne abin da Shari'ah ta
ce a yi ba tare da an zargi Wanda ya ki yi ba, shi kuwa
maulidi Shari'ah ba ta ce a yi shi ba, kuma ni a sanina
Sahabbai, da Taabi'ai, da malamai masu riko da Addini ba
su yi shi ba, wannan shi ne jawabina a gaban Allah a kan
bukin maulidi in har aka tambaye ni. Kuma ba zai halatta
ba a ce Maulidi ya zama mubaahi saboda kirkiran wani abu
cikin addini ba zai zama mubaahi ba a bisa Ijmaa'in
Musulmi, saboda haka babu abin da ya rage face maulidi ya
zama makruuhi ko kuwa haramun)). Intaha.
Sannan Imamush Shaatibii ya ce -a lokacin da yake yin
bayanin ma'anar bidi'ah- cikin littafinsa mai suna Alitisam
1/50,53 :-
(( ﻋﺒﺎﺭﺓ ﻋﻦ ﻃﺮﻳﻘﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻣﺨﺘﺮﻋﺔ ﺗﻀﺎﻫﻲ ﺍﻟﺸﺮﻋﻴﺔ ﻳﻘﺼﺪ
ﺑﺎﻟﺴﻠﻮﻙ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﺍﻟﻤﺒﺎﻟﻐﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﺘﻌﺒﺪ ﻟﻠﻪ ﺳﺒﺤﺎﻧﻪ .... ﻳﻌﻨﻲ ﺍﻧﻬﺎ ﺗﺸﺎﺑﻪ
ﺍﻟﻄﺮﻳﻘﺔ ﺍﻟﺸﺮﻋﻴﺔ ﻣﻦ ﻏﻴﺮ ﺍﻥ ﺗﻜﻮﻥ ﻓﻲ ﺍﻟﺤﻘﻴﻘﺔ ﻛﺬﻟﻚ ﺑﻞ ﻫﻲ ﻣﻀﺎﺩﺓ
ﻟﻬﺎ ﻣﻦ ﺃﻭﺟﻪ ﻣﺘﻌﺪﺩﺓ .... ﻣﻨﻬﺎ ﺍﻟﺘﺰﺍﻡ ﺍﻟﻜﻴﻔﻴﺎﺕ ﻭﺍﻟﻬﻴﺌﺎﺕ ﺍﻟﻤﻌﻴﻨﺔ
ﻛﺎﻟﺬﻛﺮ ﺑﻬﻴﺌﺔ ﺍﻻﺟﺘﻤﺎﻉ ﻋﻠﻰ ﺻﻮﺕ ﻭﺍﺣﺪ ﻭﺍﺗﺨﺎﺫ ﻳﻮﻡ ﻭﻻﺩﺓ ﺍﻟﻨﺒﻲ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻋﻴﺪﺍ ﻭﻣﺎ ﺃﺷﺒﻪ ﺫﻟﻚ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma'ana: ((Bidi'ah wata kirkirarriyar hanya ce cikin addini
mai kama da addinin gaskiya ana nufin kaiwa matuka
matuka cikin bautar Allah da yin ta .., ina nufin ita bidi'ah
tana kama da hanyar Shari'ah ba tare da ta kasance hanyar
Shari'ah ta hakika ba, kai a gaskiya ma tana karo ne da
hanyar Shari'ah ta fiskoki da yawa ... Daga cikinsu akwai
lazimtar wasu irin siffofi ayyanannu, kamar zikirin da ake yi
a bisa tsarin haduwa a kan sauti daya' da kuma rikon ranar
haihuwar Manzon Allah mai tsira da amincin Allah a
matsayin idi, da abin da yake Kama da haka)).
Sannan Shehu Uthmanu Dan Fodiyo ya ce cikin littafinsa
mai suna Ihyaaus Sunnah wa Iqmaadul Bid'ah shafi na
104 :-
(( ﻓﺎﻥ ﻗﻠﺖ ﻣﺎ ﺣﻜﻢ ﻣﺎ ﻳﻔﻌﻞ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻲ ﺷﻬﺮ ﺭﺑﻴﻊ ﺍﻻﻭﻝ ﻓﻲ ﻳﻮﻡ
ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﺍﻭ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺍﻟﺴﺎﺑﻊ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﻣﻦ ﺍﺟﺘﻤﺎﻉ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻟﻠﺬﻛﺮ ﻭﺍﻟﻄﻌﺎﻡ
ﺍﻟﺬﻱ ﻳﻌﻤﻠﻮﻧﻪ ﻟﺬﻟﻚ؟ ﻗﻠﺖ: ﺍﻧﻪ ﺑﺪﻋﺔ ﻣﻜﺮﻭﻫﺔ ﺍﻥ ﺧﻼ ﻋﻦ ﻛﻞ ﻣﻌﺼﻴﺔ .
ﻭﻗﻴﻞ: ﺍﻥ ﺍﻟﺼﻮﺍﺏ ﺍﻥ ﻋﻤﻞ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﺍﻟﺸﺮﻳﻒ ﺍﻟﻨﺒﻮﻱ ﻣﻦ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﺍﻟﺤﺴﻨﺔ
ﺍﻟﻤﻨﺪﻭﺑﺔ ﺍﺫﺍ ﺧﻼ ﻋﻦ ﻣﻌﺼﻴﺔ . ﻭﺃﻣﺎ ﻣﺎ ﻳﻌﺘﺎﺩﻩ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻲ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﺰﻣﺎﻥ
ﻓﻲ ﺫﻟﻚ ﻣﻦ ﺍﺧﺘﻼﻁ ﺍﻟﺮﺟﺎﻝ ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﻓﻤﻌﺎﺫ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻥ ﻳﻘﻮﻝ ﺍﺣﺪ
ﺑﺠﻮﺍﺯﻩ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma'ana: ((Idan ka ce: Mene ne hukuncin abin da mutane
suke yi a cikin watan Rabii'ul Awwal a ranar maulidi ko
kuwa a ranar bakwai ga maulidi na taruwar jama'a saboda
yin zikiri da cin abincin da aka yi tanadinsa saboda hakan?
Sai in ce: Wannan bidi'ah ce makruuhiyah in yin maulidin ya
wofinta daga dukkan sabon Allah. Amma kuma wasu sun
ce: Abin da yake daidai shi ne shi bukin maulidin Annabi
yana daga cikin bidi'o'i masu kyau matukar dai ya wofinta
daga ko wane sabon Allah. To amma abin da mutane suka
Saba yin shi a maulidi a wannan zamani na cakuda
tsakanin maza da mata a'uuzu billahi da wani mutum zai ce
halal ne)).
Wannan shi ne abin da malumanmu na mazhabar
Malikiyyah suka fada game da bukin maulidi.
Sannan Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah wanda ya rasu a
shekarar hijira ta 728 watau shekaru 706 ke nan da suka
wuce shi ya yi maganar maulidi ya kuma tabbatar da cewa
maulidi bidi'ah ce, ya rubuta cikin littafinsa mai suna
Iqtidhaa'us Siraa'til Mustaqiim 2/123-124 :-
(( ﻭﻛﺬﻟﻚ ﻣﺎ ﻳﺤﺪﺛﻪ ﺑﻌﺾ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺍﻣﺎ ﻣﻀﺎﻫﺎﺓ ﻟﻠﻨﺼﺎﺭﻯ ﻓﻲ ﻣﻴﻼﺩ
ﻋﻴﺴﻰ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻭﺍﻣﺎ ﻣﺤﺒﺔ ﻟﻠﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺗﻌﻈﻴﻤﺎ
ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻗﺪ ﻳﺜﻴﺒﻬﻢ ﻋﻠﻰ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﻤﺤﺒﺔ ﻭﺍﻻﺟﺘﻬﺎﺩ ﻻ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﻣﻦ ﺍﺗﺨﺎﺫ
ﻣﻮﻟﺪ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻋﻴﺪﺍ ﻣﻊ ﺍﺧﺘﻼﻑ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻲ ﻣﻮﻟﺪﻩ
ﻓﺎﻥ ﻫﺬﺍ ﻟﻢ ﻳﻔﻌﻠﻪ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﻣﻊ ﻗﻴﺎﻡ ﺍﻟﻤﻘﺘﻀﻲ ﻟﻪ ﻭﻋﺪﻡ ﺍﻟﻤﺎﻧﻊ ﻣﻨﻪ ﻟﻮ
ﻛﺎﻥ ﺧﻴﺮﺍ ﻭﻟﻮ ﻛﺎﻥ ﻫﺬﺍ ﺧﻴﺮﺍ ﻣﺤﻀﺎ ﺍﻭ ﺭﺍﺟﺤﺎ ﻟﻜﺎﻥ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻨﻬﻢ ﺍﺣﻖ ﺑﻪ ﻣﻨﺎ ﻓﺎﻧﻬﻢ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﺍﺷﺪ ﻣﺤﺒﺔ ﻟﺮﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺗﻌﻈﻴﻤﺎ ﻟﻪ ﻣﻨﺎ ﻭﻫﻢ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﺍﺣﺮﺹ ﻭﺍﻧﻤﺎ ﻛﻤﺎﻝ ﻣﺤﺒﺘﻪ
ﻭﺗﻌﻈﻴﻤﻪ ﻓﻲ ﻣﺘﺎﺑﻌﺘﻪ ﻭﻃﺎﻋﺘﻪ ﻭﺍﺗﺒﺎﻉ ﺃﻣﺮﻩ ﻭﺇﺣﻴﺎﺀ ﺳﻨﺘﻪ ﺑﺎﻃﻨﺎ
ﻭﻇﺎﻫﺮﺍ ﻭﻧﺸﺮ ﻣﺎ ﺑﻌﺚ . ﺑﻪ ﻭﺍﻟﺠﻬﺎﺩ ﻋﻠﻰ ﺫﻟﻚ ﺑﺎﻟﻘﻠﺐ ﻭﺍﻟﻴﺪ ﻭﺍﻟﻠﺴﺎﻥ
ﻓﺎﻥ ﻫﺬﻩ ﻃﺮﻳﻘﺔ ﺍﻟﺴﺎﺑﻘﻴﻦ ﺍﻷﻭﻟﻴﻦ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻬﺎﺟﺮﻳﻦ ﻭﺍﻷﻧﺼﺎﺭ ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ
ﺍﺗﺒﻌﻮﻫﻢ ﺑﺈﺣﺴﺎﻥ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma'ana: ((Haka nan abin da sashin mutane ke kirkira ko dai
saboda koyi da Kiristoci cikin bukin Kirsimeti' ko kuwa
saboda son Annabi mai tsira da amincin Allah da girmama
shi, zai yiwu Allah ya ba su lada a kan nuna kokari da
soyayya' amma ba zai ba su lada a kan bidi'o'in rikon
maulidin Annabi mai tsira da amincin Allah a matsayin idi
ba duk da yake ma masu tarihi sun yi sabani a kan wace
rana ce da wani wata ne aka haife shi! Shi dai bukin maulidi
babu wani daga cikin magabata da ya yi shi duk kuwa da
cewa dukkan dalilan da ake bayarwa na yin bukin a yanzu
akwai su a wancan lokacin ma, kuma babu wani abu da zai
hana su yin bukin inda yin shi alheri ne. Lalle ne da yin
bukin maulidi tsantsar alheri ne to da Salaf Magabata su
suka fi cancantar yin sa a kanmu, saboda sun fi mu son
Manzon Allah mai tsira da amincin Allah da girmama shi,
kuma sun fi kowa son aikata alheri. Lalle cikar soyayya da
girmamawa ga Annabi tana cikin bin shi ne da yi masa
da'ah da bin umurnin shi, da raya sunnar shi ciki da waje,
da yada abin da aka aiko da shi, da yin jihadi da zuciya, da
hannu, da harshe a kan hakan wannan ita ce hanyar
Magabata na farko daga cikin Muhajirai da Ansarawa da
wadanda suka bi su da kyautayi)).
Yan'uwa Musulmi! Wannan shi ne matsayin bukin maulidi
daga bakunan wadannan gagga-gaggan maluman
Musulunci, tare ma kuma da cewa Maluman tarihi da siiirah
sun yi sabani game da ranar haihuwar shi Annabi mai tsira
da amincin Allah, a inda wasu suka ce:
1- An haife shi ne a ran biyu ga watan Rabii'ul Awwal.
2- Wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran takwas ga
watan Rabii'ul Awwal.
3- Wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran goma ga watan
Rabii'ul Awwal.
4- Wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran goma sha
biyumga watan Rabii'ul Awwal.
5- wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran goma sha
bakwai ga watan Rabii'ul Awwal.
6- Wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran ashrin ga watan
Rabii'ul Awwal.
7- Wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran goma sha biyu
ga watan Ramadhan.
Domin ganin wannan sabanin sai ku dubi littafin Taariikhul
Islam na Imamuz Zahbii a Juz'in Siirah shafi na 25-27, da
kuma littafin Albidaayatu wan Nihaayatu na Alhaafiz Ibnu
Katheer 2/662.
Yan'uwa Musulmi! Kauli daidai har bakwai a kan ranar
haihuwar Annabi mai tsira da amincin Allah babu kuma
wani wanda ya isa ya ce: wannan kauli shi ne hakikanin
gaskiya wancan kaulin kuma ba gaskiy ba ne, saboda abu
ne da ya faru kafin zuwan Musulunci kuma bayan shi
Musulunci ya zo bai tabbatar da ranar haihuwar ba ta
hanyar wahayi saboda rashin muhimmancin yin hakan a
cikin Addini.
Ke nan ware wata rana daga cikin ranakun nan da aka
ambata da riyawar cewa ita ce ranar da aka haifi Manzon
Allah mai tsira da amincin Allah akwai nau'i na karya da
shedan zur a cikin yin hakan. Allah ya tsare mu da son
zuciya.
Wannan shi ne kashi na farko game da bayananmu a kan
bukin maulidi, kashi biyu na tafe in sha Allahu Ta'ala, kuma
zai yi bayani ne game da shubuhohin da yan bidi'ah ke
ambatawa domin tabbatar da bidi'ar maulidi.
Allah Madaukakin Sarki muke roko da Ya nuna mana
gaskiya gaskiya ce ya ba mu ikon bin ta Ya nuna mana
karya karya ce Ya ba mu ikon kin ta. Ameen.

LABARAI A TAKAICE


*Gwamnan Ondo mai barin gado Olusegun Mimiko ya taya gwamna mai jiran gado Rotimi Akeredolu murnar lashe zaben gwamnan jihar da ke kudu maso yammacin Najeriya.

*Wannan dai wani ci gaba ne don Mimiko na jam'iyyar PDP ya taya dan APC murna wanda ya kada dan takarar sa Eyitayo Jegde.

*A gefe guda PDP mai adawa ta ki amincewa da sakamakon zaben da bukatar a soke shi.

*Kakakin bangaren Ahmed Makarfi na jam'iyyar ta PDP Dayo Adeyeye ya ce jam'iyyar ta umurci reshen ta na Ondo ya shigar da kara a kotun sauraron karar zaben jihar.

*Hukumar zaben Najeriya INECta bakin daraktan ta na labaru Barista Osaze Uzi ta ce an gudanar da zaben gaskiya  kuma sakamakon zaben shine ainihin abun da al'ummar jihar Ondo su ka zaba.

*Ina shawartar 'yan Nijeriya da su goyi bayan kokarin da gwamnatin Buhari take yi domin shawo kan matsalolin da take fama da su a Nijeriya, Inji tsohon shugaban Naijeriya Yakubu Gowon

*A wani mataki na wanke kansa, Tsohon Shugaban Kwamitin Dattawa na jam'iyyar PDP, Cif Tony Anenih ya bayyana cewa zamanin da Shugaba Buhari ya yi Shugaban mulkin soja a shekarar 1985 ya bayar da umarnin garkame shi saboda kawai ya mallaki tarin dukiya.

*A cewar Tony Anenih a iya saninsa babu wani laifi da ya yi a wancan lokaci illa kawai wasu makiyansa ne suka kai kokensa a matsayinsa na Shugaban jam'iyyar NPN na jihar Bendel inda ya ce an kai shi gidan kurkuku na Kirikiri wanda a can ya hadu da wasu gwamnonin farar hula wadanda suka taba bayar da umarnin zartar da hukuncin kisa a kan wasu masu laifi a lokacin suna kan mulki.

*Duk Mutanen Dake Kusa Da Buhari Ba sa Iya Fada Masa Gaskiya, Cewar Buba Galadima

*Buba Galadima ya kuma kara da cewa idan har shugaba Buhari na bukatar ya fitar da kansa daga kunya a wurin 'yan Nijeriya, dole sai ya yi tankade rairaya a cikin mukarrabansa.

*Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ba gaskiya bane maganganun da ya ke ji ana ta yawo da shi cewa wai yana da matsala da Tinubu ko kuma jam'iyyar APC na da matsala da Tinubu.

*Buhari ya ce Tinubu ba mutum bane wanda jam'iyyar APC za ta tayi wasa dashi musamman ganin irin dimbin gudunmawar da ya ke ba jam'iyyar tun kafuwarta.
Buhari ya ce zantukan da ake ta yadawa na kanzon kurege ne domin basu da wata madafa.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
29/Safar/1438
29/November/2016

Friday, 25 November 2016

LABARAI A TAKAICE


*Shugaban kungiyar JIBWIS Imam Abdullahi Bala Lau ya nuna matukar mamakin wani faifan bidiyo da a ke yayatawa a kafar labarun yanar gizo cewa ya tura Sheikh Hussaini Zakariyya zuwa wajen Sheikh Dahiru Bauchi ya ba shi hakuri da ma nuna shehin na darikar tijjaniyya tamkar uba ya ke a gare shi.

*Imam Bala Lau ya ce sam bai aiki kowa ya je ba da hakuri a kan laifin da bai ma san menene ba ne in ka debe wa'azin da kungiyar ta ke yi na kira tsaida SUNNAH DA TURE BIDI'A.

*Sanarwar da ta fito ta kafafen yanar gizo na "JIBWIS NIGERIA" na nuna ko ma da Imam Bala Lau zai aika wata tawaga to da zai zama cikin daya daga jami'an ofishin sa ko daya daga shugabannin kungiyar na Izala kama daga matakin tarayya, jihohi har zuwa kananan hukumomi.

*Shehin malamin ya ce kungiyar JIBWIS ba za ta daina yaki da bidi'o'I ba har abada.

*Faifan bidiyon dai ya nuna Sheikh Hussaini Zakriyya wanda mai tafsiri ne a masallacin Othman Ben Affan a Abuja da wassu malaman da su ka hada da na darika har ma da jami'ar asusun BIL GATES a Najeriya Dr. Mairo Mandara.

*Da alamu wannan tawaga ta malamai ne da likitoci masu wayar da kan al'umma kan cutar shan inna da sauran su amma ba tafiyar kungiyar JIBWIS BA CE

*Kwamitin amintattu na jam'iyyar adawa ta PDM a Najeriya ya tsige shugaban jam'iyyar Bashir Ibrahim Yusuf daga mukamin sa da zargin aikata laifuka da barin jam'iyyar ta zama kara zube.

*Jam'iyyar a taron ta a Abuja ta nada kwamitin riko karkashin Munir Garba Waziri da zai yi aiki tsawon wata 3 gabanin sabon zaben sabbin shugabanni.

*Da yake maida martani, Bashir Yusuf yayi watsi da tsigewar da zargin wani babban dan siyasa ne ya iza wutar don samun madafar tsayawa takarar shugaban kasa a 2019.

*Yusuf ya ce da an bi ta lalama da zai iya sarayar da mukamin na sa amma tun da an nuna abun da ya fassara da karfi,ya ce a zuba a ga wanda ke da gaskiya.

*Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan Ondo ranar asabar din nan 26 ga wata, Eyitayo Jegede ya bukaci hukumar zabe ta dage zaben da tsawon kwana 30.

*Jegede wanda ya samu nasarar takarar a kotu da maye gurbin Jimoh Ibrahim,ya ce dage zaben zai ba shi damar mika wakilan da za su kula ma sa da kuri'u.

*Dan takarar ya nuna kara wa'adin ne zai dace da dokar zabe.

*Shugaban kwamitin amintattun PDP Sanata Walid Jibrin ya yabawa kotu da ta ba wadan takarar nasara ya na mai cewa zai lashe zaben gwamnan Ondo….

*A bangaren ta jam'iyya mai mulki a Najeriya APC na mara baya ga dan takarar ta Ekeredelu don samun nasarar lashe kujerar gwamnan.

*Duk da uban jam'iyyar Sanata Bola Ahmed Tinibu ba ya mara baya ga dan takarar da sa kafar wando daya da shugaban jam'iyyar John Oyegun; hakan bai hana shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tattaki zuwa birnin Akure ba inda ya daga hannun Ekeredelu da yi ma sa fatar samun nasara.

Ibrahim Baba Suleiman
JIBWIS Social Media
25/Safar/1438
25/November/2016

Thursday, 24 November 2016

LABARAI A TAKAICE


*Kotun daukaka ta Najeriya ta ayyana dan takarar bangaren Makarfi na jam'iyyar PDP a Eyitayo Jegede a matsayin sahihin dan takarar jam'iyyar a zaben gwamnan jihar Ondo wanda za'ayi ranar asabar din nan mai zuwa 26 ga wata.

*Wannan hukuncin dai ya ture takarar Jimoh Ibrahim na bangaren PDP karksahin sanata Ali Modu Sherif.

*Yanzu dai za a jira a ga yadda hukumar zabe za ta sauya sunan Jimoh Ibrahim da na Jegde don zaben.

*Kazalika bangaren Ali Sherif na da hurumin daukaka kara zuwa kotun koli.

*Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya ba Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu umarnin haramta koyarwa ga duk wani malamin da ba ya da kwarewa da kuma wadanda ba su yi rajista ta hukumar yi wa malamai rajista ta kasa ( TRCN).

*Da yake karin haske kan haramcin, Ministan Ilimi, Adamu ya ce duk wanda bai da rajista da hukumar TRCN ba zai samu cin gajiyar shirin gwamnati na daukar malamai 500,000 da aka fara yi a yanzu ba inda ya kalubalanci duk wani Malami da bai yi rajista ba da ya gaggauta yin hakan.

*Tunda Buhari Ya San Cewa An Zabe Shi Ne Domin Kawo Canji A Kasar Nan, To Ya Kamata Ya Daina Duba Kura-kuran Da Shugabannin Baya Suka Yi, Ya Yi Kokarin Mayar Da Hankali Kan Yadda Za A Shawo Kan Matsalolin Kasar Nan, Inji Tsohon Shugaban Naijeriya  Obasanjo

*Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya ya ce jami'ansa 128 ne suka mutu sakamakon hare-haren da masu tsattsauran ra'ayi suka kai musu a bakin-aikinsu.

*Wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan kasar DCP Don N Awunah ya aike wa manema labarai ta ce an kashe jami'an 'yan sandan ne a sassa daban-daban cikin wata uku.

*Hukumomi a jihar Zamfara sun ce an saki mutane sama da 40 da masu fashin shanu suka sace a farkon a makon jiya.

*Tsohon shugaban Naijeriya Oludegun Obasanjo ya ce abin kunya ne a ce wai duka 'yan majalisar wakilai su taru akan Abdulmumini Jibrin mai makon su duba abinda yake kira akai ne domin a gyara irin tabargazan da ake tafkawa a majalisar.

*Obasanjo Yace Abdulmumini Jibrin ya na da gaskiya akan abubuwan da yake fadi amma maimakon su bi hakan domin a gyara sai gaba dayansu suka taru masa akai domin wulakantashi saboda basu da gaskiya.

*Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ya nuna fushinsa akan yadda jami'an hukumar tsaro na sirri wato SSS suka far ma gidajen wadansu alkalai domin bincikansu akan zargin cin hanci da ake musu.

*Kakakin majalisar ya fadi hakanne yau lokacin da ya ke kaddamar da wata kwamiti da ya kafa domin binciken ayyukan hukumar SSS din.

*Ya ce abinda hukumar SSS ta keyi yanzu bai da ce ba saboda ta na irin aikin hukumar EFCC ne.

*Shi kuwa tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo cewa yayi abinda gwamnatin Buhari take yi domin tsaftace fannin shari'a na kasa yayi dai-dai soboda irin lalacewan da fannin tayi.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
24/Safar/1438
24/November/2016

Sent from my Windows Phone

Wednesday, 23 November 2016

LABARAI ATAKAICE


*Hukumar zaben Najeriya ta ce ta kammala shirin gudanar da zaben gwamnan jihar Ondo ranar asabar 26 ga watan nan.

*Kiran da bangaren PDP da Sanata Ahmed Makarfi ke jagoran ta ya yi na a dage zaben don hakan ya ba da damar kammala shari'ar dan takarar jam'iyyar da ke gaban kotun daukaka kara.

*Hukumar dai ta yi zama da masu ruwa da tsaki na zaben a babban birnin jihar Ondo, Akure.

*Kotun koli ta ba wa kotun daukaka kara ta Najeriya umurnin ci gaba da shari'ar samun sahihin dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan Ondo.

*Tun farko babbar kotun tarayyar Najeriya ta ba wa Jimoh Ibrahim takarar wanda zuwa yanzu shi hukumar zabe ta amince da sunan sa don takarar bisa umurnin kotu.

*Dan takarar bangaren gwamna Olusegun Mimiko na Ondo wato Eyitayo Jegede na bukatar kotun ta tabbatar ma sa takarar.

*Wassu sakonni na wayar salula sun yayata wani labarai, da alamu ke nuna neman firgita jama'a ne inda su ke baiyana wai 'yan ta'addan Boko Haram sun fantsama har zuwa yankunan kudancin Najeriya.

*Sakon dai ya nuna ya fito ne daga jami'an tsaron Najeriya don ba wa jita-jitar karfin tasiri.

*Duk binciken da mu ka gudanar ya nuna labarin ba gaskiya ba ne.

*A kan samu irin wadannan sakonnin da kan nuna wa imma daga jami'an tsaro ne ko daga ofishin jakadancin Amurka a Najeriya da ke da zummar razana jama'a.

*Babbar kotun tarayyar Najeriya ta ba da belin alkalin kotun koli Jostis Ngwuta kan naira miliyan 100 wanda hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta gurfanar da shi gaban kotun bisa tuhumar cin hanci da rashawa.

*Jostis Ngwuta da sauran alkalai 6 na fuskantar irin wannan tuhuma bayan samame da hukumar tsaron farin kaya ta kai gidajen su.

*Tuni dai alkalai su ka dakata daga jagorantar shari'u a kotuna sai bayan kammala shari'ar su da gano sun a da laifi ne koko a'a.

*Garin Aleppo a kasar Sham na ci gaba da dandana barin wuta biyo bayan kin amincewar da gwamnatin Shugaba Bashar Al-Asad ta yin a yarjejeniyar tsagaita bude wuta da majalisar dinkin duniya ke jagoranta.

*Baya ga hare-hare daga gwamnatin Asad,Kasar Rasha da kungiyar 'yan shi'a ta Hezbollah da ke Lebanon na tayawa wajen wannan yakin da hakan ya hana garin zaman lafiya.

*Rayuwa a Aleppo ba ta da tabbas don komai ya na iya faruwa koyaushe ta hanyar barin boma-bomai.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
23/Safar/1438
23/November/2016

Tuesday, 22 November 2016

LABARAI A TAKAICE


*Hukumomin Kasar Saudiya tare da hadin gwiwar hukumar mahajjatan Najeriya sun mikawa magadan Alhazai goma sha biyu na jihar Adamawa da suka rasa ransu a turairainiyar da ta abku lokacin akin hajjin 2015

*Tun a bara Hukumar Alhazan ta baiwa ko wace jiha kayan Alhazan na wadanda suka rasa rayukan su a turmutsitsin Mina, kusan dukkan jihohin da abun ya shafa sun raba nasu, illa Jihar Adamawa wanda sai a wannan karo ta samu damar rabawa 'yan uwan mamatan kayayyakin su.

*Rundunar sojin kasa a Naijeriya ta musanta cewa ta rage yawan sojojinta a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

*Rundunar sojin na mayar da martani ne akan fargabar da wasu mazauna birnin Maiduguri ke yi cewa, karuwar hare-haren kunar bakin wake daga 'yan kungiyar Boko Haram yasa gwiwar su ta yi sanyi.

*Hukumar ta ce tattalin arzikin ya kara samun koma baya ne da sama da kashi 2.

*Najeriya dai ta fada cikin matsalar tattalin arziki ne sakamakon faduwar farashin danyen mai a kasuwar duniya inda farashin ya yi mugunyar faduwa daga dala 100 zuwa kasa da 50.

*Barayin da suka sace Minista Bagudu Hirse sun dauka shine MAMMAN DAURA domin shi suka zo nema - Inji wanda suke tare da Minista Bagudu Hirse a lokacin da aka sace shi.

*Pukat yace Jami'an tsaron gidan Mamman Daura sun bashi kunya domin gaba dayansu sun ari na kare a lokacin da sukaji Mutanen suna harbi sama.

Ya ce wani maigadi ne ma ya zo ya rufe kofar gidan bayan sun tafi.

*Alkalumman da hukumar Kiddidiga a Najeriya ta fitar na cewa tattalin arzikin kasar ya sake samun koma baya a cikin watanni uku da suka gabata sakamakon hare-hare da ake kai wa kan bututun mai a yankin Neja Delta da kuma karanci kudaden waje a hannun 'yan kasuwa.

*Samamen da hukumar tsaron farin kaya DSS ta kai kasuwannin canjin kudi a Najeriya don tilasta saukar da farashin dala ,ya jefa tsoro a zukatan 'yan canjin.

*A kasuwar canjin ta babban birnin Najeriya Abuja Zone 4, 'yan canjin na zukewa zantawa da manema labaru don ka da allura ta tono garma.

Jibrin Zakar na daga kalilan daga 'yan canjin da ya bayyana cewa matakin da a ka dauka a kan 'yan canjin ya yi tsauri don in za a bi ta tattaunawa za a gane inda matsalar ta ke.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
22/Safar/1438
22/November/2016

Monday, 21 November 2016

LABARAI A TAKAICE


*'Yan ta'adda sun kai wani sabon hari a jihar Zamfara inda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 9.
Biyu daga cikin wadanda su ka rasa ran su 'yan sanda ne.

*Kakakin rundunar 'yan sanda ta Najeriya Don Awunah ya ce an tura jami'an 'yan sanda na kwantar da tarzoma yankin.

*Ta'addancin dai daga 'yan fashi da makami da barayin shanu ya fi muni gabanin tura sojoji yankin don murkushe 'yan ta'addan.

*Masu satar mutane sun sace tsohon ministan harkokin wajen Najeriya Ambasada Bagudu Hirse.
Hirse dai ya shiga Kaduna don ta'aziyyar rasuwar tsohon sarkin musulmin Najeriya Sultan Ibrahim Dasuki inda ya gamu da akasin.

*'Yan bindiga matasa uku da fuska rufe sun tilasta Hirse ya shiga motar su daidai gidan dan uwan shugaba Buhari, Mamman Daura.

*Rahotanni sun nuna Hirse ya so ya ratse don ya gaisa da Mamman Daura inda wannan akasin ya auku.

*Sace mutane ya ta'azzara a yankin Kaduna da kewaye inda miyagun ke neman kudin fansa.

*Gwamna Kashim Shettima ya ba wa matar marigayi hazikin sojan Najeriya Laftanar Kanar Abu Ali tallafin Naira miliyan 10.

*Muhammad Abu Ali wanda dan tsohon gwamnan soja na jihar Bauchi ne Laftanar Janar Abu Ali ya rasu a kwantan bauna da 'yan Boko Haram su ka yi wa sojojin da ya ke yi wa jagoranci a Mallam Fatori da ke jihar Borno.

*Wani jirgin kasa ya subuce daga kan layin dogo a arewacin Indiya inda hakan ya haddasa asarar rayuka da samun raunuka.

Zuwa rubuta wannan labari fiye da mutum 116 su ka rasa ran su inda jami'ai ke ta kokarin ceto rayuka.
Fiye da mutum 150 su ka samu raunuka.

*Tsohon dan takarar shugabancin Amurka Mit Romney da sauran manyan 'yan jam'iyyar Republican sun gana da shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump don tattaunawa kan shirya sabuwar gwamnati.

*A na rade-radin nada Romney a matsayin sakataren wajen Amurka .

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
21/Safar/1438
21/November/2016

Sunday, 20 November 2016

LABARAI A TAKAICE


*Kungiyar Ahlussunnah Wal Jama'a JIBWIS ta yi gagarumin taron wa'azi a Sokoto cibiyar daular Usmaniyya da ke arewa maso yammacin Najeriya.

*Wa'azin dai ya ta'allaka ne kan yaki da cin hanci da rashawa da kuma baiyana yadda daular Usmaniyya ta Shehu Usmanu Dan Fodio ta ba da gudunmawar yada Sunnah a nahiyar Afurka.

*Manyan malamai da alarammomi ne suka gabatar da kasidu tare da wa'azi a  daidai lokacin da kungiyoyin Ahlussunnah ke kara dagewa wajen cusawa al'umma sahihiyar akidar Islama da kiyaye doka da oda.

*Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ba da labarin sake dakile harin da wani dan kunar bakin wake ya so kai wa kan sansanin 'yan gudun hijira na gidan kwastam da ke kan hanyar Gamborun Ngala a Maiduguri.

*Labarin dai ya nuna dan kunar bakin waken ya ki tsayawa a bincike shi da kan ya sanya a ka bude ma sa kuma damarar sa ta bom ta fashe ta hallaka shi.
Dan kunar bakin waken dai shi kadai ya rasa ran sa.

*Bangaren Sanata Makarfi na babbar jam'iyyar adawar Najeriya PDP na ci gaba da fatar kotu za ta musanya dan takarar jam'iyyar Jimoh Ibrahim da Eyitayo Jegede.

*Jimoh Ibrahim dai wanda babbar kotun tarayya ta ba shi takarar na bangaren jam'iyyar ne da Sanata Ali Modu Sherif ke jagoranta.

*Yanzu dai lamarin na kotun daukaka kara mako daya gabanin gudanar da zaben a ranar asabar 26 ga watan nan.

*Wassu 'yan ta'adda a yankin Dammam na Saudiyya sun hallaka wani Jami'in sojan Saudiyya.
Irin wannan kisan gilla shine na biyu a kasa da wata daya da 'yan bindigar da ba a san ko su waye ne ba su ka kai.

*'Yan sandan Saudiyya na ci gaba da binciken wannan ta'addancin.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
20/Safar/1438
20/November/2016

Saturday, 19 November 2016

LABARAI A TAKAICE


*Babban hafsan rundunar sojan kasan Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya gana da jakadan babban sakataren majalisar dinkin duniya Muhammad Ibn Chambers a helkwatar yaki da Boko Haram a Maiduguri da ke da taken " Operation lafiya dole "

*Buratai ya ce yawancin 'yan Boko Haram da su ka yi saranda ba 'yan Najeriya ba ne.

*Buratai ya shaidawa Chambers cewa rundunar ta gano kashi 60% na 'yan ta'addan ba ma 'yan Najeriya ba ne.

*Babban hafsan ya ce rundunar ba za ta daina fafatawa ba sai ta gama da 'yan ta'addan.

*Chambers ya yi amfani da damar wajen ta'aziyya ga rundunar bisa rasuwar Laftanar Kanar Abu Ali da wassu dakaru 6 a fagen daga a Malam Fatori.

*Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya nuna da abun da ya ce arangamar 'yan sanda da 'yan Shi'a a Kano da ofishin ya ce hakan ya yi sanadiyyar mutuwar rubin sha bibbiyu na 'yan an Shi'an.

*A sakon da ofishin ya aikawa gidajen labaru,ya bukaci gudanar da bincike da kira ga gwamnatin Najeriya ta ke tattaunawa da 'yan shi'an da mutunta 'yancin gudanar da ibada ta kowacce kungiya.

*Hakanan ofishin ya bukaci yin adalci kan arangamar 'yan Shi'a da rundunar sojan Najeriya a Zaria a Disambar bara.

*Ofishin dai na nuna tamkar 'yan sandan sun yi amfani da karfin da ya wuce kima kan 'yan Shi'a.

*A nasu bangaren 'yan Shi'an da shugaban Ibrahim Elzakzaky na aza alhakin akasin da ke samun su kan Amurka da Isra'ila.

*Mataimakin shugaban 'yan Shi'an Yakubu Yahaya ya ce gwamnatin Najeriya na biyewa bukatun kasashen turai ne irin Amurka wajen takurawa 'yan shi'an.

*Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ba da tabbacin mutuwar wata 'yar kunar bakin wake daya da ta tada bom din da ke jikin ta da hakan ya kuma yi sanadiyyar mutuwar abokin tafiyar ta daya.Baya ga mutuwar 'yan kunar bakin waken biyu daf da buhunan yashin bigiren tsaron 'yan sanda, an samu nasarar damke mace daya da ran ta da a yanzu a ke gudanar da bincike.

*Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewacin Nigeria sun ce 'yan bindiga masu fashin shanu sun sace mutane fiye da arba'in a jihar.
A ranar Juma'a ne da dai masu fashin shanun suka sace mutanen a lokaci guda domin yin garkuwa da su.

*Akasarin mutanen da suka yi awon gaba dasu dai 'yan kasuwa ne da ke kan hanyarsu ta zuwa cin kasuwa daga kauyukansu.

*Wata tankar man fetur ta fadi a kasar Muzambik inda ta kama da gobara da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 73 fiye da 100 su ka samu raunuka.

*Mutanen dai sun gamu da akasin ne a yayin da su ke kamfatar man da ke malala daga motar wacce daga bisani ta kama da wuta.
Lamarin ya auku ne a yankin Tete da ke kan iyakar Muzambik da Malawi.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
19/Safar/1438
19/November/2016