About Us


Jama’atu Izatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS) is an Islamic organisation for the eradication of innovation and establishment of the Sunnah of the Holy Prophet (SAW). This group of Muslims and the organisation has been established as far back as 1978 in Nigeria, and its Pioneering Chairman was Late Alhaji Musa Maigandu Muhammad, and also its first Grand patron was Late Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, and Late Sheikh Isma’il Idris bn Zakariyya served as its first National Chairman Ulama'u Council.
The Katsina State Chairman of the Organisation is Sheikh Yakubu Musa Hassan.
The organisation being the first of its kind in the history of Islamic propagation, scholarship, and championing the cause of Islamic religion courageously without fear, set aside tangible, concrete, and strong unambiguous aims and objectives, for the purpose of attaining its targeted goals.
Its regular activities include:

  • Active teaching of Islamic religion base on the true and authentic teaching of the Holy prophet (PBUH), without resorting to following whims and caprices, prejudice and blind following.
  • Massive teaching of true Islamic ideals.
  • An annual/occasional Da'awah outings (State preaching) to villages and towns within the state, for the propagation of Islam.
  • Periodic visits to prison for humanitarian and religious, and to assist in securing the release of Muslim inmates convicted on minor offences through payment of fines and other possible assistance.
  • Periodic visits to hospitals and orphanages to assist indigent patients and inmates respectively
  • Assist in the establishment of mosques and learning centers/schools.
  • maintaining various forms of publications, ranging from books, pamphlets, journals, magazines, newspapers, for enlightenment, teaching and awareness among the Muslim Ummah.
  • Maintaining a strong First Aid organ, for offering help to the Muslim Community.
  • The Organization has produced several scholars and students of knowledge all over the federation of Nigeria and beyond. It has the largest followers, especially those Muslims who truly act, only in accordance to the authentic teachings of the Holy prophet (PBUH).
The aims and objectives of the organisation are:
  • Eradicating and eliminating ignorance from the society in general.
  • Unity and brotherhood of the Muslim Ummah.
  • Sensitizing and orienting Muslim Ummah on Islamic religion in relation to their developmental activities in their lives here and hereafter.
  • Discarding, rejecting and throwing away of various unislamic beliefs in publications and in whatever form.
  • Assuring, and affirming to the Muslim Ummah, that the holy prophet has accomplished and completed his mission fully, judiciously and diligently without leaving any matter unattended.
  • Anybody claiming to be a prophet, or claiming that the prophet visits him, should be considered as a great original liar.
  • Propagating Islam in Katsina State, right from the grass root (villages) level to the international level.
  • Acting vigorously and actively towards acknowledging the saying of the holy prophet (PBUH), specifically where he says: “whoever sees a negative thing, he has to change it with his hand, if he can't do that, then with his tongue, and if he can't do that, by his heart, and that is the weakest form of faith.”
  • Maintaining that a proof must be from the book of Allah and Hadith of the Holy prophet, and that proof should not be concealed under any circumstance.
The Organization, as an international Organization per se, has a lot of active organs that make the execution and running of its activities to go smoothly. Many sub committees are found in the Organization, and some of these committees include:
  • First Aid Committee
  • Da’awah Committee
  • Seminar Committee
  • Trustee committee
  • Education committee
  • Executive committee
  • Social Media committee
  • Orphanage and less privileged committee e.t.c

NATIONAL EXECUTIVES OF JIBWIS SOCIAL MEDIA COMMITTEE    

1.  DIRECTOR            IBRAHIM BABA SULAIMAN GOMBE   
2.  ASST. DIRECTOR 1       AMINU IMAM IKARA KADUNA   
3.  ASST DIRECTOR 2        ANAS ASSALAFY FAGGE KANO   
4.  SECRETARY            ADAMU ATTAHIRU KEBBI   
5.  ASST. SECRETARY 1      MUHAMMAD AHMAD BINDAWA GOMBE   
6.  ASST. SECRETARY 2      NAZEER MUKHTAR  DANJAGALE KATSINA   
7.  ORG. SECRETARY         MUSA H. MUSA GOMBE
8.  ASST. ORG. SECRETARY 1 ENGR. IBRAHIM ISMA’IL BORNO   
9.  ASST. ORG. SECRETARY 2 SHU’AIBU AMINU DALHATU SOKOTO   
10. FIN. SECRETARY    S/GAMARYA RABI'U ISA LAGOS   
11. ASST. FIN. SECT.    UMAR ABDURRA'UF NASARAWA   
12  TREASURER            IDRIS ATTAH BAUCHI   
13. AUDITOR            ALIYU KWARA KWARA   
14. ASST. AUDITOR 1    LAWWALI IBRAHIM KURYA ZAMFARA   
15. ASST. AUDITOR 2    USMAN MUHAMMAD HADEJIA JIGAWA   
16. PUBLICITY SECT.    MAHMUD ISA ASSALAFY ADAMAWA   
17. ASST. PUBLICITY SECT. 1 SHEHU YA'U USAIZA NIGER   
18. ASST. PUBLICITY SECT. 2 JABIR ZUBAIR AL-JASAWI JOS   
19. EDITOR             UMAR MOHAMMED ABUJA   
20. ASST. EDITOR     UMAR ALIYU MISAU BAUCHI   
21. LEGAL ADVISER     BRR. BILYAMINU LUKMAN TARABA   
22. ASST. LEGAL ADVISER     ADAMU ASSUNNAH BAUCHI  

PATRONS:
SHEIKH  DR  IBRAHIM  JALO  JALINGO.
SHEIKH  ABUBAKAR  ABDUSSALAM  BABANGWALE
SHEIKH  DR  RABI’U  UMAR  R/LEMU
SHEIKH  ALIYU  SA’ID  GAMAWA

Kungiyar kawar da Bidi’ah da tsayar da sunnah.

Wannan qungiya ta al’ummar musulmi an kafa ta ne tun a shekarar 1978 a Najeriya, kuma shugabanta na farko shi ne Alhai Musa Gandu Muhammad, a qarqashin kulawar Malam Abubakar Mahmud Gumi, tare da Sheikh Isma’il Idris bn Zakariyya, a matsayin shugaban majalisar malamai na farko na kungiyar.

Qungiyar ita ce irinta ta farko a tarihin yada addinin musulunci a Najeriya, hadi da harkar ilmantarwa, tare da daukaka darajar harkokin addinin Musulunci ba tare da wani tsoro ba. Don haka ne sai kungiyar ta sanya wasu ginshiqan manufofi da take so ta cimma domin kai wa ga gaci.

Daga cikin muhimman manufofin wannan kungiya sun hada da:
  • Kawar da duhun jahilci daga cikin al’umma, wanda ya yi wa al’umma katutu.
  • Hada kan al’ummar musulmi a bisa koyarwar Alqur’ani da Sunnar Manzon Allah (SAW),
  • Wayar da kan al’ummar musulmi game da al’amuran addini, domin a gudu tare a tsira tare.
  • Fadakar da al’ummar musulmi domin a yi watsi da wasu miyagun littattafai da suke tura mutane cikin halaka.
  • Tabbatarwa da cewa Annabi (SAW) ya kammala isar da sakon Allah (SWT).
  • Duk wanda ya yi da’awar annabta, ko kuma yake riya cewa Annabi (SAW) yana ziyartarsa da wani sako, to wannan zunzurutun makaryaci ne.
  • Yada Musulunci a Najeriya da wajen Najeriya.
  • Yin da’awa a kan fadin Manzon Allah (SAW) cewa: “duk wanda ya ga abin qi, to ya sauya shi da hannunsa, idan ba zai iya ba, to da harshensa, in ba zai iya ba, to da zuciyarsa, amma wannan shi ne mafi raunin imani.”
  • Kar a boye hujja in dai har ta tabbata daga littafin Allah Madaukakin Sarki, ko sunnar Manzon Allah (SAW).

Wasu daga cikin ayyukan kungiyar sun hada da:
Kasancewar wannan kungiya ta shahara sosai a kasashe daban-daban na duniya, wannan ya sa aka samar da kwamitoci daban-daban domin gabatar da ayyuka da yawa. Wasu daga cikin kwamitocin kungiyar sun hada da:

  • Kwamitin Da’awah.
  • Kwamitin Tarurrukan Wa’azi.
  • Kwamitin Kula da Marayu
  • Kwamitin Ilimi.
  • Kwamitin Mutane Goma.
  • Kwamitin Yanar gizo
  • Kwamitin Taimakon Gaggawa.

KWAMITIN ZARTASWA:

Shugabanta na kasa a wannan lokaci shi ne Sheikh Abdullahi Bala Lau, khalifa na farko a sashin shugabancin wannan kungiya tun bayan kafa kungiyar, wanda tsohon mataimakin shugaban kungiyar ne a zamanin shugabancin marigayi Alh. Musa maigandu Muhammad, kuma ya gaje shugabancin kungiyar ne bayan rasuwarsa.

Sheikh Usman Isah Taliyawa:: Mataimakin Shugaban Kungiya Na Kasa.
Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe: Babban Magatakardan kungiya
Sheikh Dr Ibrahim Jalo Jalingo: Shugaban Majalisar Malamai na kasa
Engr. Mustapha Imam Sitti: Shugaban Rundunar Yan Agaji na Kasa
Sheikh Yakubu Musa Hassan: Shugaban Kungiya na jihar Katsina


kungiyar ta samu karbuwa a sassa daban-daban na duniya. A Najeriya tana da rassa a dukkanin jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya. Haka kuma saboda irin yadda kungiyar take kokarin ilmantar da al’umma, wannan ya sa har ta sami kutsawa zuwa ga wasu kasashe, kamar su; Nijar da Mali da Sinigal da Togo da Kamaru da Cadi da Burkina da Gini, Saudi Arabia da sauransu.

Wasu daga cikin abubuwan da kungiyar ta mayar da hankali wajen yin su, sun hada da:

- Koyarwa a bisa tafarkin Manzon Allah (SAW) ba tare da bin son zuciya ko kuma yin makauniyar biyayya ga wani ba.

- Tsantsar karantar da hakikanin ilimin addinin Musulunci.

- Gabatar da wa’azin kasa a duk makwanni biyu ko uku ko hudu don tunatar da mutane abin da suka manta ko kuma lokutan da suka dace.

- Kafa makarantu domin koyar da ilimin addini da na boko, da sauran fannonin ilimi.

- Kai ziyarori gidajen marayu da gidajen yari da asibitoci, domin tallafar musulmai marasa galihu.

- Samar da taimakon gaggawa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

kungiyar ta samar da hamshaqan malamai a sassa wadanda suka sami daukaka ta ilimi a fadin duniya baki daya, saboda jajircewa da kokarin bin tafarkin Manzon tsira, Annabi Muhammad (SAW), sau da kafa.

Haka kuma ta ko wacce fuska tarihin izala zaizo , dogo ko gajere, ba za a taba mantawa da irin gudummar da marigayi Sheikh Isma'ila Idris Bin Zakariyya ya bada ba, da irinsu Marigayi Ibrahim Bawa Maishinkafa da Mal. Hudu Chikaji. Koda ba manufarmu zayyana sunan kowa ba, amma muna addu'a ga dukkan wadanda suka sadaukar da dukiyoyin su da kuma rayukansu akan wannan harka taci gaban addini, Allah ya saka musu da gidan Aljanna ya hada mu dasu a babban matsayi a lahira.

Wannan kadan ne daga cikin irin manufofin da kungiyar Izala ta kafu a kayi, kuma a haka za'a tafi da ikon Allah.

Daga Karshe Muna Addu'an Allah ya nuna mana gaskiya gaskiya ce ya bamu ikon binta, ya nuna mana karya karya ce ya bamu ikon guje mata.