KYAUTAR BIKIN KIRSIMETI:
HALAL KO HARAM?
Da yawa Musulmi suna tambayar shin ko ya halatta su karbi kyautar kiristoci a ranar kirsimeti,musamman wandan da suke zaune lafiya tare da su,ko suke aiki a guri daya.
Ga bayanin da Malamai suka yi dangane da haka:
1- Baya halatta ga Musulmi ya nuna farincikin sa da wannan ranar,ta hanyar aikawa da gaisuwa ko kyauta ko furanni, ko makamantan su.
2- Ba ya halatta gare shi ya ci abin da aka yanka da sunan wannan rana.
3- Ya halatta ya karbi kautar da za su bashi a wannan ranar, Kamar yadda ya halatta gare shi ya ci abin da za su ba shi wadanda ba yankawa ake yi ba.
Kamar kayan marmari.
4- Dalili kuwa shi ne:
A) Baihaqi ya ruwaito a cikin littafinsa As-
Sunanul Kubra 9/234 cewa, Muhammad Bn Sirin ya ce: an kawo wa Ali, Allah ya kara yarda a gare shi, kautar idin majusawa Nairuz.
Sai ya ce: menene wannan kuma?
Sai suka ce masa, ya Sarkin
Muminai yau ranar idin Nairuz ce.
Sai ya ce, to kullum ma su yi 'Nairuz'.
Wato ya karba, tare da nuna ya ji dadin kyautar.
B) Ibn Abi Shaibah a cikin littafinsa Al-Musannaf 5/126 daga Sahabin nan Abu Barzata Al-Aslamy cewa: yana da makwabta majusawa, kuma a duk
ranar bukukuwansu suna aiko masa da
kyaututtuka a gidansa, sai yakan cewa iyalinsa, yaya abin yake?; idan kayan marmari ne to ku ci,wanda kuma ba kayan maramari bane, to ku mayar musu kayansu.
C) Haka kuma ya ruwaito 5/126 cewa: wata mata ta tambayi Nana A'isha ta ce, muna tare da mata majusawa masu sana'ar shayar da jarirai,to duk ranar idin su suna aiko mana da kyauta.
Sai A'isha, Allah ya kara yarda a gare ta, ta ce mata,abin da aka yanka domin wannan ranar kada kuci.
Ku ci kayan marmari na itatuwa.
Ibn Taimiyya ya ce, wannan ya nuna idinsu ba shi da wani tasiri wajen ya hana a karbi kyautarsu.
Karbar kyautar su a ranar idin su da ranar da ba idin ba duk hukunci daya ne, domin
wannan ba shi ne taimaka musu ba akan aikinsu na kafirci.
Duba Littafinsa Iqtidha' Siratil Mustaqim 2/52.
Sannan a karshe yana da kyau mu fahimci cewa,Ba ya halatta musulmi ya taimaka da yi musu yanka a wannan ranar.
Kuma koda musulmi ne ya yanka musu ba za a ci ba.
Allah ka shiryar da mu tafarkinka madaidaici.
Dr. Sani Umar R/lemo.
Albany Dabai,
08069123479.
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve