Wednesday, 14 December 2016

LABARAI A TAKAICE

LABARAI A TAKAICE

*Ayau talata ne ake saran tawagar kungiyar kasashen Afirka ta Yamma zata isa kasar Gambia dan janyo hankalin shugaba Yahya Jammeh na ganin ya sauka daga mukamin sa cikin ruwan sanyi bayan shan kashin da yayi a zaben shugaban kasar.

Shugabar kungiyar ECOWAS Ellen Johnson Sirleaf zata jagoranci tawagar wadda ta kunshi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da shugaban Saliyo Ernest Bai Karoma da shugaban Ghana mai barin gado John Dramani Mahama.

*Shugaban. Naijeriya, Muhammad Buhari ya tabbatar da cewa kafin shekarar 2019, gwamnatinsa za ta gina Madatsun ruwa 400 a duk fadin kasar nan don gudanar da noman rani.

Shugaban ya bayyana haka ne a wurin taron kungiyar yaki da yunwa ta FCPN wanda aka yi a Abuja inda ya nuna cewa yawan 'yan Nijeriya ya rubanya  a tsakanin shekaru 25 yana mai jaddada cewa a kan haka ne ya sa gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen farfado da harkar noma da ma'adinai.

*Ya ce ta hanyar gina Madatsun ruwa ne, manoma za su iya yin noma sau uku a duk shekara.

*Gwamnan Jihar Akwa Ibom da ke kudancin Nijeriya, inda rufin wata Majami'a ya fadi akan masu ibada a ranar Asabar da ta gabata, in da mutane da yawa suka mutu, ya bada umarnin kama wadanda suka yi kwangilar ginin, cewar wata kafar yada labarai ta jihar.

*Gwamna Emmanuel wanda yake a majami'ar yayin da al'amarin ya faru, kuma ya tsira ba tare da jin ko da ciwo ba, ya bada umarnin kamen.

*Maimaita zaben majalisa na jihar Rivers da ke kudu maso kudancin Najeriya bai wanye lafiya ba inda 'yan bangar siyasa su ka hallaka wani jami'in 'yan sanda DSP Alkali Muhammed kazalika su ka fille kan sa.

A wannan harin da ya faru a yankin da shugaban babbar jam'iyyar adawa na jihar ya fito, wassu abokan aikin dan sandan sun sha da kyar.

*Jihar Rivers dai ta dade da zama mai hatsarin gaske wajen gudanar da lamuran zabe inda baya ga kisan gilla da 'yan bangar ke yi su kan fille kan wanda su ka kashe don firgita jami'an tsaro da sauran 'yan siyasar da su ke hamayya da su.

*Wasu 'yan bindiga dadi da har yanzu ba a san ko su wane ne ba sun arce da wasu mata 35 a kauyen Matankari da ke karkashin masarautar Dansadau a karamar hukumar Maru da ke jihar Zamfara.

*Da yake tabbatar da aukuwar lamarin Kwamishinan 'Yan sanda jihar, Shaba Alkali ya ce rundunarsa ta samu nasarar kwato wasu daga cikin Matan kuma a halin yanzu suna ci gaba da farautar wadannan 'yan ta'addan da nufin kwato sauran Matan.

*Rahotanni dai sun nuna cewa 'yan bindiga dadin wanda yawansu ya kai kusan mutum 100 sun aukawa kauyen ne inda suka rika harbe harbe ta yadda suka tarwatsa mutanen kauyen sannan suka arce da Matan.

*Gwamnatin jihar Bauchi da ke arewa maso  gabashin Najeriya ta biya ma'aikata albashi na wasu watanni  da su ke bin bashi inda hakan ya kawo walwala a jihar.

*Gwamna Muhammad Abdullahi Abubakar na jam'iyyar APC ya sha ba wa ma'aikatan hakuri da nuna gwamnatin ta sa na bin duk hanyoyin da su ka dace don biyan albashin.

*Akwai jihohi da dama da su ka gaza biyan albashi musamman don raguwar kudaden shiga da kuma kason da jihohin ke samu daga gwamnatin taraiya.

*Hakanan jihohi da dama sun dauki matakan bincike don rage ma'aikata musamman na bogi da wadanda ke karbar albashi ba bisa ka'ida ba.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
13/Rabi-Al'Awwal/1438
13/December/2016

Albany Dabai,
08069123479.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve