Wednesday, 14 December 2016

LABARAI A TAKAICE


LABARAI A TAKAICE

*Tsohon gwamnan jihar sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya karbi ziyyarar jaddada goyon bayan kungiyoyin kabilar Yarbawa da Igbo a gidansa na Sokoto dake Shinkafi Road. Kungiyoyin dai sunczo bada gaisuwar girma ne tare da nuna goyon bayansu ga jagoransu Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa.

*A nasu jawabin shugabannin sun nuna jaddada goyon bayansu ga jam'iyyar PDP akoda yaushe har zuwa 2019, tare da biyayya ga shugaban jam'iyyar PDP Alhaji Ibrahim Milgoma da sauran shugabanni jam'iyya.

*Daga karshe Garkuwan Sakkwato ya yi bayanin godiya da wannan ziyara da wadannan manyan kungiyoyin suka yi masa inda ya maida jawabi ga kungiyoyin da sucigaba da hakuri da adawa da suke yi da kuma biyayya ga jam'iyyar PDP.

*Sojojin Nijeriya sun samu nasarar ceto kimanin Shanu 300 daga barayin shanu a jihar Zamfara inda aka mika su ga jami'an gwamnatin jihar don mika su ga wadanda suka mallake su.

*Kwamandan Birget ta Daya da ke Sokoto, Birgediya Janar Ginikanwa Nwosu ne ya bayyana haka inda ya nuna cewa a kowane mako suna ceto akalla shanu 500 daga barayin Shanun. Ya kara cewa an kara yawan sojoji a jihar don murkushe ayyukan satar mutane da shanu.

*Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya tabbatar da cewa jam'iyyar APC ta tafka manyan Kurakurai wanda dole sai ta zauna don duba yadda za ta shawo kansu.

Dogara ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da ya kai ziyara ga Shugaban APC na Kasa, Cif John Odigie Oyegun a hedkwatar jam'iyyar da ke Abuja inda ya nuna cewa akwai bukatar samun kyakkyawar alaka tsakanin majalisa da bangaren gwamnati.

*Kotun tarayyar Najeriya  da ke garin Ado Ekiti da ke jihar Ekiti ta umarci hukumar EFCC da ta gaggauta bude asusun ajiyar Bankin Gwamnan Ekiti, Ayo Fayose wanda ta rufe kwanaki bisa Izinin wata kotun tarayya da ke Lagas.

*A hukuncin da Alkalin kotun, Mai Shari'a Taiwo Taiwo ta yanke, ya nuna cewa hukumar EFCC ba ta bi tsarin doka wajen rufe asusun guda biyu da ke Bankin Zenith. Alkalin ya kuma nuna cewa EFCC ta shiga hakkin Fayose a matsayinsa na Gwamnan wanda kuma dokar kasa ta bashi kariya daga fuskantar tuhuma.

*Shugabar kasar Liberian Ellen Johnson Sirleaf, wacce ta jagoranci wata tawagar shugabannin kasashen yammacin Afrika don sasanta rikicin siyasar kasar Gambia ta ce babu wata yarjejejeniya da suka cimma don kawo karshen dambarwar.

*Tun da farko dai Sojoji a Gambia sun mamaye hedikwatar hukumar zabe yayin da Jam'iyyar Mr Jammeh ta shigar da kara a kotun kolin kasar inda ta bukaci a soke zaben.

*Sai dai a halin yanzu kotun bata da isassun Alkalai, saboda haka ba a san takamammen lokacin da za a saurari karar ba. Abaya dai Shugaban kungiyar ta ECOWAS, Marcel de Souza, ya yi barazanar cewa za su yi amfani da karfi idan Mista Jammeh ya ki mutunta kundin tsarin mulkin kasar.

*Zababben shugaban kasar Adama Barrow, wanda ya lashe zaben na 1 ga watan Disamba, ya nemi taimakon kasashen duniya. A watan gobe ne ya kamata a rantsar da shi a kan karagar mulki.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
14/Rabi-Al'Awwal/1438
14/December/2016
Albany Dabai,
08069123479.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve