*'Yan ta'adda sun kai wani sabon hari a jihar Zamfara inda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 9.
Biyu daga cikin wadanda su ka rasa ran su 'yan sanda ne.
*Kakakin rundunar 'yan sanda ta Najeriya Don Awunah ya ce an tura jami'an 'yan sanda na kwantar da tarzoma yankin.
*Ta'addancin dai daga 'yan fashi da makami da barayin shanu ya fi muni gabanin tura sojoji yankin don murkushe 'yan ta'addan.
*Masu satar mutane sun sace tsohon ministan harkokin wajen Najeriya Ambasada Bagudu Hirse.
Hirse dai ya shiga Kaduna don ta'aziyyar rasuwar tsohon sarkin musulmin Najeriya Sultan Ibrahim Dasuki inda ya gamu da akasin.
*'Yan bindiga matasa uku da fuska rufe sun tilasta Hirse ya shiga motar su daidai gidan dan uwan shugaba Buhari, Mamman Daura.
*Rahotanni sun nuna Hirse ya so ya ratse don ya gaisa da Mamman Daura inda wannan akasin ya auku.
*Sace mutane ya ta'azzara a yankin Kaduna da kewaye inda miyagun ke neman kudin fansa.
*Gwamna Kashim Shettima ya ba wa matar marigayi hazikin sojan Najeriya Laftanar Kanar Abu Ali tallafin Naira miliyan 10.
*Muhammad Abu Ali wanda dan tsohon gwamnan soja na jihar Bauchi ne Laftanar Janar Abu Ali ya rasu a kwantan bauna da 'yan Boko Haram su ka yi wa sojojin da ya ke yi wa jagoranci a Mallam Fatori da ke jihar Borno.
*Wani jirgin kasa ya subuce daga kan layin dogo a arewacin Indiya inda hakan ya haddasa asarar rayuka da samun raunuka.
Zuwa rubuta wannan labari fiye da mutum 116 su ka rasa ran su inda jami'ai ke ta kokarin ceto rayuka.
Fiye da mutum 150 su ka samu raunuka.
*Tsohon dan takarar shugabancin Amurka Mit Romney da sauran manyan 'yan jam'iyyar Republican sun gana da shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump don tattaunawa kan shirya sabuwar gwamnati.
*A na rade-radin nada Romney a matsayin sakataren wajen Amurka .
Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
21/Safar/1438
21/November/2016
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve