Wednesday, 30 November 2016

MAULIDI A MAHANGAR MUSULUNCI (II)


Ibrahim Jalo Jalingo

Akwai shubuhohin da masu shar'anta Idin maulidi ke
ambatawa a matsayin hujjojin da ke wajabta Idin maulidi ko
halatta shi, saboda haka In sha Allahu Ta'ala za mu ambaci
uku daga cikinsu a wannan rubutu namu (kashi na 2)
sannan mu ba da amsarsu, saboda burin da muke da shi
na tsarkake addinin Musulunci daga wannan bidi'ah mai
kama da bidi'ar Kirsimeti wacce Kiristoci ke yi cikin ko wace
shekara, haka nan saboda burinmu na cewa: dukkanmu mu
al'ummar Musulmi mu hadu a kan daidai, mu gudu tare mu
tsira tare. Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce cikin
ingantaccen hadithinsa:
(( ﻻ ﻳﺆﻣﻦ ﺍﺣﺪﻛﻢ ﺣﺘﻰ ﻳﺤﺐ ﻻﺧﻴﻪ ﻣﺎ ﻳﺤﺐ ﻟﻨﻔﺴﻪ )).
Ma'ana: ((Dayanku ba zai yi imani ba har sai ya so wa
dan'uwansa abin da yake so wa kansa)).
****************************
SHUBUHA TA FARKO:
Shubuha ta farko: Suka ce: Allah ne da kansa Ya yi umurni
da yin bukin Idin maulidi cikin Suratu Yunus aya ta 58 a
inda ya ce:-
{ ﻗﻞ ﺑﻔﻀﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺑﺮﺣﻤﺘﻪ ﻓﺒﺬﻟﻚ ﻓﻠﻴﻔﺮﺣﻮﺍ ﻫﻮ ﺧﻴﺮ ﻣﻤﺎ ﻳﺠﻤﻌﻮﻥ }.
Ma'ana: {Ka ce: Ku yi farin ciki da falalar Allah da
rahamarSa shi ne mafi alheri daga abin da suke tarawa}.
Suka ce: Annabi shi ne falalar Allah da rahamarSa, Allah
kuwa Ya ce a yi farin ciki da falalarSa da kuma rahamarSa,
farin cikin kuwa yana nufin shirya bukin maulidinsa ne ahi
Annabi mai tsira da amincin Allah, ke nan shirya bukin
maulidi ko wace shekara bin wani umurni ne na musamman
Wanda ya fito daga Allah madaukakin Sarki, rashin bin
wannan umurni kuwa lalle saba wa Shi Allah Madaukakin
Sarki ne!!!
Amsa a kan wannan shubuha tana da rassa da yawa:-
Na farko: sai a ce da su: Fassara wannan ayar da cewa
tana umurni ne da yin bukin maulidi fassara ce da take
Kama da fassarar Baatiniyyah da gulaatus suufiyyah da
suke yi wa wasu nassoshin Alkur'ani mai girma, kamar
yadda suka fassara ayah ta 25 cikin Suratu Nuuhin inda
Allah Yake magana game da mutanen Annabi Nuhu Ya ce:-
{ ﻣﻤﺎ ﺧﻄﻴﺌﺎﺗﻬﻢ ﺃﻏﺮﻗﻮﺍ ﻓﺄﺩﺧﻠﻮﺍ ﻧﺎﺭﺍ ﻓﻠﻢ ﻳﺠﺪﻭﺍ ﻟﻬﻢ ﻣﻦ ﺩﻭﻥ ﺍﻟﻠﻪ
ﺃﻧﺼﺎﺭﺍ}.
Ma'ana: {Saboda laifukansu na ganganci aka nitsar da su
(cikin ruwa) sannan aka sanya su a Wuta. Saboda haka ba
su sama wa kansu wanin Allah a matsayin Mai taimako ba}.
Sai suka ce: ma'anar ayar ita ce: Allah Yana nufin cewa
abin nan da suka yi wa Annabi Nuhu na saba wa umurnin
da Allah ya aiko shi da shi shi ne ya Kai su ga yin nitso cikin
tekunan sanin Allah! Watau dai abin nan da suka yi na saba
wa Annabi Nuhu babu wani zunubi a cikinsa kamar yadda
wasu ke tsammani!!
Suka kuma fassara inda Allah Ya ce cikin Suratul Israa'i aya
ta 23:-
{ ﻭﻗﻀﻰ ﺭﺑﻚ ﺍﻻ ﺗﻌﺒﺪﻭﺍ ﺍﻻ ﺇﻳﺎﻩ }.
Ma'ana: {UbangijinKa Ya hukunta cewa kada ku bauta wa
kowa sai Shi}.
Sai suka ce: Ma'anar ayar ita ce: "Ubangijinka Ya riga ya
kaddara muku cewa ba za ku yi wata bauta ba face Allahn
ne dai kuka bautawa! saboda haka babu wani abu a
duniyan da za ku bautawa face a hakikanin lamari Allah ne
Shi kadanSa kuka bautawa!!
Suka kuma fassara inda Allah ya ce cikin Suratul Hijri aya ta
99 :-
{ ﻭﺍﻋﺒﺪ ﺭﺑﻚ ﺣﺘﻰ ﻳﺄﺗﻴﻚ ﺍﻟﻴﻘﻴﻦ }.
Ma'ana: {Kuma ka bauta wa Ubangijinka har mutuwa ta zo
maka}. Sai suka ce: ma'anarsa shi ne: shi Dan Adam ana
umurtansa da yin ibada ne har zuwa lokacin da ya kai
matsayin Yakini da sanin Allah, da zarar ya kai wannan
matsayi ayyukan ibada sun fadi ke nan a Kansa!!
Reshe na biyu: Sai a ce da su: Wani malami ne cikin
maluman tafsiiri daga magabata Salafus Salih ya fassara
wannan ayar da irin wannan fassara taku ta cewa: Ana
nufin yin bukin maulidi ne da wannan ayah? Lalle muna
tabbatar wa masu karatun wannan rubutu namu cewa: har
abada yan bidi'ar maulidi ba za su iya kawo koda malamin
tafsiiri daya ba daga cikin Salafus Salih da ya fassara
wannan ayar da cewa tana nufin umurni ne da yin bukin
maulidi.
Rashe na uku: Sai a ce da su: In dai har wannan ayar tana
nufin yin bukin maulidi ne to kuwa lazimin hakan shi ne:
Sahabbai da sauran shugabannin Al'ummah kamar su Abu
Hanifah, da Mali, da Shafi'ii da Ahmad, da sauransu
dukkansu ke nan sun nuna kiyayya da rashin kauna ga
Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah, sannan dukkansu
ke nan sun saba wa umurnin Allah da ya zo cikin wannan
aya ta 58 da ta zo cikin Suratu Yunus, domin har suka
gama rayuwarsu babu wani daga cikinsu da ya taba yin
bukin maulidi! Duk kuwa wanda ya ce: Sahabbai, da
Taabi'ai da sauran shugabannin Al'ummah ba sa kaunar
Manzon Allah ko ba sa girmama shi, ba sa bin umurnin
Allah da ya zo cikin Alkur'ani na girmama shi to lalle
wannan ya bace bata bayyananniya! Lazimin wannan kuwa
shi ne: Yan bukin maulidi su ne batattu saboda lazimin
maganarsu ta tabbatar da cewa Sahabban Manzon Allah da
Taabi'ai, da Taabi'utttaabi'ina da sauran Sugabannin
Al'ummah batattu ne, saboda ba su yi aiki da wannan aya
ba:-
{ ﻗﻞ ﺑﻔﻀﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺑﺮﺣﻤﺘﻪ ﻓﺒﺬﻟﻚ ﻓﻠﻴﻔﺮﺣﻮﺍ ﻫﻮ ﺧﻴﺮ ﻣﻤﺎ ﻳﺠﻤﻌﻮﻥ }.
Reshe na hudu: Sai a ce da su: Dukkan abin da bai zama
nuna soyayya ba ne ga Manzon Allah a zamanin Shabbai
da Taabi'ai da sauran Shugabanni kamar Imam Malik, da
Abu Hanifah, da Shaa'i'ii, da Ahmad, to ba zai zama nuna
soyayya ga Manzon Allah ba a wannan zamani namu.
Idan kuma wani daga cikin yan bukin maulidi ya fidda
jahilcinsa a fili ya ce: Ai Suyuutii ya halatta yin bukin
maulidi ! Sai a ce da shi: Ai shi Suyuutii ba ya daga cikin
wadanda ake kira Magabata cikin Musulunci, a'a yana cikin
jerin yan baya ne, domin ya mutu ne a shekara ta 911 na
hijira watau yau shekara 523 ke nan da suka wuce. Kuma
shi Suyuutii a wurin Malamai mutum ne da yake kama da
mai tara kirare cikin dare, ya kan dauki kirare sannan ya kan
dauki macizai da kunamu, saboda wannan idan har ya
halatta bidi'ar bukin maulidi ba wani abin mamaki ba ne a
gurin Malamai, domin ya yi ma abin da ya fi hakan muni da
ban mamaki, saboda Mai littafin Rimaahu Hizbir Rahiim ya
ce a cikin wannan littafi nasa wanda aka buga tare da
littafin Jawaahirul Ma'aa'nii 1/199 ya ce shi Suyuutii ya ce
cikin littafinsa mai suna :-
ﺗﻨﻮﻳﺮ ﺍﻟﺤﻠﻚ ﻓﻲ ﺇﻣﻜﺎﻥ ﺭﺅﻳﺔ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﻭﺍﻟﻤﻠﻚ
"Ya ga Annabi kuma ya yi taro da shi a farke har sau
saba'in da wani abu"! Mai irin wannan magana mara tushe
don ya ce bukin maulidi halal ne mene abin mamaki a cikin
maganarsa? Allah Ya tsare daga fadawa cikin ko wace irin
halaka. Ameen.
SHUBUHA TA BIYU:
Shubuha ta biyu suka ce: Duk wata ni'ima da Allah Ya yi wa
mutum, to dole ne ya gode aw Allah a kanta, saboda lokacin
da Annabi ya dawo Madinah ya ga Yahudawa suna azumi a
ranar goma ga watan Muharram sai shi Annabi mai tsira da
amincin Allah ya tambaye su ya ce: Me ya sa kuke azumin
wannan rana? Sai suka ce masa: Wannan rana ce da Allah
Ya tsirar da Annabi Musa tare da jama'arsa, kuma Ya
halakar da Fir'auna tare da mutanensa cikin teku, shi ya sa
Annabi Musa yake azumin wannan rana saboda gode wa
Allah mu ma shi ya sa muke yin azuminsa, sai Annabi mai
tsira da amincin Allah Ya ce: Mun fi ku cancantar yin abin
da Annabi Musa ya yi, saboda haka ya yi azumin wannan
ranar kuma ya umurci Musulmi da su yi azuminsa. A nan
muna ganin babu wata ni'ima da ta kai haihuwar Annabi
Muhammad mai tsira da amincin Allah, kuma ko shakka
babu wannan ni'ima za ta wajabta mana gode aw Allah,
wannan kuwa shi ya sa muke yin bukin maulidi saboda
nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki.
Amsa a kan wannan shubuha tasu sai a ce da su: Lalle
gaskiya ne ni'imomin Allah suna wajabta godiyar Allah a
kan bayinSa, to amma hakika ni'ima mafi girma a cikin
Musulunci ita ce:Ni'imar ba wa Annabi mai tsira da amincin
Allah Manzanci, ba. Wai ni'imar haihuwar sa ba, domin
Alkur'ani mai girma bai yi nuni da ishara zuwa haihuwarsa
koda sau daya ba, to amma ya yi nuni da ishara zuwa ga
manzancinsa ba sau daya ba ba sau biyu ba! Allahl
Madaukakin Sarki Ya ce cikin Suratu Aa'li Imraan aya ta
164:-
{ ﻟﻘﺪ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﺇﺫ ﺑﻌﺚ ﻓﻴﻬﻢ ﺭﺳﻮﻻ ﻣﻦ ﺍﻧﻔﺴﻬﻢ ﻳﺘﻠﻮ
ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺁﻳﺎﺗﻪ ﻭﻳﺰﻛﻴﻬﻢ ﻭﻳﻌﻠﻤﻬﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺤﻜﻤﺔ }.
Ma'ana: {Hakika Allah Ya yi babbar falala ga muminai
domin Ya aika da Manzo daga ainihinsu yana karanta musu
ayoyinSa Yana tsarkake su yana karantar da su Littafi da
Hikima}. A nan Allah bai ce: domin an haifi wani Manzo
daga cikinsu ba, a'a sai Ya ce: Domin an aiko wani manzo.
Wannan shi ne halin da za ku tarar game da ko wane Manzo
daga cikin manzannin Allah Madaukakin Sarki, watau abin
himmantuwa game da shi shi ne aiko shi ba wai ranar
haihuwarsa ba, kamar dai yadda Allah Madaukakin Sarki ya
ce cikin Suratul Bakara aya ta 213:-
{ ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺃﻣﺔ ﻭﺍﺣﺪﺓ ﻓﺒﻌﺚ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻨﺒﻴﻴﻦ ﻣﺒﺸﺮﻳﻦ ﻭﻣﻨﺬﺭﻳﻦ ﻭﺍﻧﺰﻝ
ﻣﻌﻬﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﺑﺎﻟﺤﻖ ﻟﻴﺤﻜﻢ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻴﻤﺎ ﺍﺧﺘﻠﻔﻮﺍ ﻓﻴﻪ }.
Ma'ana: {A da mutane sun kasance al'umm ce guda daya,
sai Allah Ya aiko Annabawa suna masu bishara suna masu
gargadi, kuma Ya saukar da Littafi da gaskiya tare da su'
domin ya yi hukunci tsakanin mutane cikin abin da suka
Saba aw juna cikinsa}. Kun gani a nan' da dai mayar da
wata rana Idi da sunan addini halal ne cikin addinin
Musulunci, to da kuwa marar da aka aiko Manzon Allah mai
tsira da amincin Allah Idi shi ne ya fi.
Sannan kuma game da azumin da shi Annabi mai tsira da
amincin Allah ya yi na ranar Aashuuraaa to fa dole ne mu
sani cewa: Shi fa Annabi mai tsira da amincin Allah shi ne
mai shar'antawa kuma mai isar da sako daga Ubangijinsa
zuwa ga sauran mutane, saboda haka ba ya halatta a gare
mu mu yi kiyasin wani mutum a kan shi, har na mu fada
cikin wata bidi'a, domin abin da ake bukata ga dukkan
al'ummar Musulmi shi ne: Su zama masu bi a koda yaushe
ba wai masu kirkiro bidi'o'i ba. Sannan kuma shi azumi ai
kishiyar bukin Idi ne saboda azumi yana nufin hana sa kai
cin abinci shi kuwa bukin Idi yana nufin ciyar da kai abinci
ne, saboda haka ta kaka za a kira yin azumi bukin Idi?
SHUBUHA TA UKU:
Shubuha ta uku: suka ce: Annabi mai tsira da amincin Allah
ya kasance yana azumi a ko wane ran litinin, a lokacin da
Sahabbai suka tambaye shi: Don me yake azumi a wannan
rana? Sai ya ce: yana azumtar ko wace litinin ne saboda a
ran litinin ne aka haife shi.
Yan maulidi suka ce wannan yana nufin ke nan Annabi mai
tsira da amincin Allah shi ma yana bukin maulidi watau
yana bukin ranar haihuwarsa.
Amsa a kan wannan shubuha ta yan maulidi sai a ce da su:-
Na daya: Musulmi ba sa musun halaccin azumin ranar
litinin da kuma falalarsa, haka ma azumin ranar alhamis da
falalarsa, to amma shi wannan azumin aka yi shi ne cikin
dukkan kwanakin litinin da alhamis na shekara, ba wai sau
daya ne ba kawai ake yin shi cikin shekara, kamar yadda
masu yin bidi'ar maulidi suke yin shi sau daya cikin
shekara.
Na biyu: lalle kiyasta bukin maulidi a kan azumin ranar
litinin da ake yi cikin ko wane mako, kiyasin abin da yake
bidi'ah ne a kan bin da yake Sunnah, wannan kuwa Kiyasi
ne batacce.
Na uku: lalle inda su masu bukin maulidi suna son koyi ne
da Annabi mai tsira da amincin Allah cikin abin da shi
Annabin ya yi a ranar haihuwarsa, to da sai su wadatu da
abin da shi Annabi mai tsira da amincin Allah ya wadatu da
shi, watau sai su rika yin azumi cikin ko wace ranar litinin,
ba wai su rika bukin maulidi cikin ko wace ranar gama sha
biyu ga watan Rabi'ul Awwal ba, saboda shi Manzon Allah
mai tsira da amincin Allah bai yi maulidi a ranar goma sha
biyu ga watan Rabi'ul Awwal ba duk kuwa da cewa yana
damar yin hakan in da yin hakan ya dace da Shari'ar
Musulunci, to amma da yake hakan bai dace da Shari'ar
Musulunci sam bai yi hakan ba, abin kawai aka sani ya yi
shi ne: Azumin ranar litinin cikin ko wane mako. Ke nan
wannan zai wajabta wa yan bukin maulidi in har dai suna
son Annabi suna kuma girmama shi suna kaunar bin
hanyar da ya bi, su bar yin bukin maulidi a ranar goma sha
biyu ga watan Rabi'ul Awwal su koma yin azumin ranar
litinin ko wane mako, da kuma ranar alhamis ko wane
mako.
Allah Madaukakin Sarki muke roko da Ya tausaya wa
al'ummarmu Ya cusa musu son AnnabinSa mai tsira da
amincin Allah tare da son bauta maSa ta hanyar sunnar
Annabin naSa ba wai ta hanyar bidi'ar da Shaidan ya
kawata musu ba. Ameen.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve