Tuesday, 29 November 2016

MAULIDI A MAHANGAR MUSULUNCI [1]

Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

Yau Talata 29/2/1438 H wanda ya dace da 29/11/2016 M
muna dab da kaiwa goma sha biyu ga watan Rabii'ul
Awwal, kuma kamar yadda aka sani ne cewa wannan rana
ta sha biyu ga Watan Shawwal ita ce ranar da wasu ke
bukin ranar haifuwar Annabi Muhammad mai tsira da
amincin Allah, saboda neman lada da falala a wurin Allah,
duk kuwa da cewa rikon wannan rana a matsayin Idi bidi'a
ce wurin dukkan Maluman Musulunci! Haka dai Shaidan
yake batar da mutane ta hanyar kawata musu wani abin da
ba Shari'ah ba ne har su rika ganin shi tamkar abin da yake
Shari'ah ne! Allah yana cewa cikin Suratu Faatir aya ta 8:-
(( ﺃﻓﻤﻦ ﺯﻳﻦ ﻟﻪ ﺳﻮﺀ ﻋﻤﻠﻪ ﻓﺮﺍﻩ ﺣﺴﻨﺎ ﻓﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻀﻞ ﻣﻦ ﻳﺸﺎﺀ ﻭﻳﻬﺪﻱ
ﻣﻦ ﻳﺸﺎﺀ ﻓﻼ ﺗﺬﻫﺐ ﻧﻔﺴﻚ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺣﺴﺮﺍﺕ ﺍﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻢ ﺑﻤﺎ
ﻳﺼﻨﻌﻮﻥ)).
Ma'ana: ((yanzu wanda aka kawata masa mummunan
aikinsa har ya gan shi wani abu Mai kyau "yana daidai da
waninsa?" saboda haka lalle Allah yana batar da wanda
yake so, kuma ya shiryar da wanda yake so, kada ranka ya
halaka a kansu saboda bakin ciki. Lalle Allah Masani ne ga
abin da suke sana'antawa)).
Mu a nan, a bisa dogara da ayah ta 104 a cikin Suratu Aali
inda Allah Ya ce:-
(( ﻭﻟﺘﻜﻦ ﻣﻨﻜﻢ ﺃﻣﺔ ﻳﺪﻋﻮﻥ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﻭﻳﺄﻣﺮﻭﻥ ﺑﺎﻟﻤﻌﺮﻭﻑ ﻭﻳﻨﻬﻮﻥ ﻋﻦ
ﺍﻟﻤﻨﻜﺮ ﻭﺃﻭﻟﺌﻚ ﻫﻢ ﺍﻟﻤﻔﻠﺤﻮﻥ )).
Ma'ana: ((A samu wata al'umma daga cikinku da za ta yi
kira zuwa ga alheri, sannan ta umurni da abin da Shari'ah ta
sani, kuma ta yi hani ga abin da Shari'ah bata sani ba. To
su wadannan Al'umma sune masu rabauta)). Da kuma
dogara kan aya ta 78, da 79 cikin Suratul Maa'idah inda
Allah Madaukaki ya yi maga a kan Banuu Isaraa'iil ya ce:-
(( ﻟﻌﻦ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻛﻔﺮﻭﺍ ﻣﻦ ﺑﻨﻲ ﺍﺳﺮﺍﺋﻴﻞ ﻋﻠﻰ ﻟﺴﺎﻥ ﺩﺍﻭﺩ ﻭﻋﻴﺴﻰ ﺍﺑﻦ
ﻣﺮﻳﻢ ﺫﻟﻚ ﺑﻤﺎ ﻋﺼﻮﺍ ﻭﻛﺎﻧﻮﺍ ﻳﻌﺘﺪﻭﻥ . ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻻ ﻳﺘﻨﺎﻫﻮﻥ ﻋﻦ ﻣﻨﻜﺮ
ﻓﻌﻠﻮﻩ ﻟﺒﺌﺲ ﻣﺎ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻳﻔﻌﻠﻮﻥ )).
Ma'ana: ((An la'anci wadanda suka kafirta daga Banu
Isaa'iil a bisa harshen Daawuuda da Isa Dan Maryam,
saboda irin yadda suka yi sabo, suka kasance suna ketare
iyaka. Suka kasance ba sa hana juna yin mummunan aikin
da suke aikatawa. Wallahi abin da suka kasance suna
aikatawa ya yi muni)). Da kuma dogara kan hadithin da
Imam Muslim ya ruwaito hadithi na 49 inda Annabi mai tsira
da amincin Allah yake cewa:-
(( ﻣﻦ ﺭﺃﻯ ﻣﻨﻜﻢ ﻣﻨﻜﺮﺍ ﻓﻠﻴﻐﻴﺮﻩ ﺑﻴﺪﻩ ﻓﺎﻥ ﻟﻢ ﻳﺴﺘﻄﻊ ﻓﺒﻠﺴﺎﻧﻪ ﻓﺎﻥ ﻟﻢ
ﻳﺴﺘﻄﻊ ﻓﺒﻘﻠﺒﻪ ﻭﺫﻟﻚ ﺍﺿﻌﻒ ﺍﻻﻳﻤﺎﻥ )).
Ma'ana: ((Wanda duk ya ga munkari daga cikinku sai ya
jirkita shi da hannunsa, in kuma ba zai iya ba, sai ya jirkita
shi da harshensa, in kuma ba zai iya ba sai ya jirkita shi da
zuciyarsa, wannan shi ne mafi raunin Imani)). Da kuma
dogara kan maganar Sahabin Annabi Abdullahi Dan Mas'ud
Allah ya kara masa yarda, wacce ta zo cikin littafin Ibnu
Wadh,dhah shafi na 11 da littafin Ali'itisaam na Imamush
Shaatibii 1/107 inda ya ce:-
(( ﺍﺗﺒﻌﻮﺍ ﻭﻻ ﺗﺒﺘﺪﻋﻮﺍ ﻓﻘﺪ ﻛﻔﻴﺘﻢ )).
Ma'ana: ((Ku bi -abin da Annabi ya zo da shi- kada ku kirkiri
bidi'ah, domin an gama muku kome -na addini-)). Dankuma
dogara har yanzu a kan maganar shi Sahabi Abdullahi Dan
Mas'uud wacce ta zo cikin littafin Ibnu Wadh'dhah shafi na
11 da kuma Sunanud Daarami 1/68-69 a inda ya ce lokacin
da ya wuce wani mai wa'azi a cikin masallaci yana ce wa
mutane: ku yi Subhanallah kafa goma, ku yi la'laha illalah
kafa goma, sai ya ce da su:-
(( ﻭﻳﺤﻜﻢ ﻳﺎ ﺃﻣﺔ ﻣﺤﻤﺪ ﻣﺎ ﺍﺳﺮﻉ ﻫﻠﻜﺘﻜﻢ ! ﻫﺆﻻﺀ ﺻﺤﺎﺑﺔ ﻧﺒﻴﻜﻢ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻣﺘﻮﺍﻓﺮﻭﻥ ﻭﻫﺬﻩ ﺛﻴﺎﺑﻪ ﻟﻢ ﺗﺒﻞ ﻭﺃﺗﻴﺘﻪ ﻟﻢ ﺗﻜﺴﺮ ﻭﺍﻟﺬﻱ
ﻧﻔﺴﻲ ﺑﻴﺪﻩ ﺍﻧﻜﻢ ﻟﻌﻠﻰ ﻣﻠﺔ ﻫﻲ ﺃﻫﺪﻯ ﻣﻦ ﻣﻠﺔ ﻣﺤﻤﺪ ﺍﻭ ﻣﻔﺘﺘﺤﻮﺍ ﺑﺎﺏ
ﺿﻼﻟﺔ . ﻗﺎﻟﻮﺍ ﻳﺎ ﺃﺑﺎ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﻣﺎ ﺍﺭﺩﻧﺎ ﺍﻻ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﻗﺎﻝ ﻭﻛﻢ ﻣﺮﻳﺪ
ﻟﻠﺨﻴﺮ ﻟﻦ ﻳﺼﻴﺒﻪ ﺍﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺍﻥ ﻗﻮﻣﺎ
ﻳﻘﺮﺀﻭﻥ ﺍﻟﻘﺮﺍﻥ ﻻ ﻳﺠﺎﻭﺯ ﺗﺮﺍﻗﻴﻬﻢ ﻭﺍﻳﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﺎ ﺍﺩﺭﻱ ﻟﻌﻞ ﺍﻛﺜﺮﻫﻢ ﻣﻨﻜﻢ
ﺛﻢ ﻭﻟﻰ ﻋﻨﻬﻢ )).
Ma'ana: ((kaitonku ya ku al'ummar Muhammad mamakin
saurin halakarku! Wadannan Sahabban annabinku ne mai
tsira da amincin Allah ga su nan da yawa, wadannan
tufafinsa ne ba su gama yagewa ba, wadannan butocinsa
ne ba su gama fashewa ba. Ina rantsuwa da Wanda raina
yake hannunsa lalle ne ku ko dai kuna kan wani addini ne
da ya fi addinin Muhammad shiriya ko kuwa ku masu bude
kofar bata ne. Sai suka ce wallahi baban Abdurrahman
babu abin da muke nufi sai alheri. Sai ya ce ai da yawa mai
son alheri ba zai taba samun sa ba. Lalle Manzon Allah mai
tsira da amincin Allah ya gaya mana cewa akwai wasu
mutane da za su rika karanta Alkur'ani amma kuma ba zai
wuce makogoronsu ba, Ina rantsuwa da Allah watakila mafi
yawansu daga cikinku suke. Daga nan sai ya juya ya bar
su)). Intaha. Da kuma dogara kan maganar babban Taabi'ii
Hasanul Basarii wacce ta zo cikin littafin Ibnu Wadh'dhah,
da littafin Alitisam na Shaatibii 1/111 inda ya ce: ((Mai yin
bidi'ah ba zai Kara kokari cikin azuminsa na bidi'ah ba, ko
sallarsa ta bidi'ah ba, face hakan ya nisantar da shi daga
Allah)).
Dogara kan wadannan ayoyi da hadithai da maganganun
Sahabbai da Taabi'ai da kuka ji su yanzu ne ya sa muke
gargadin Al'ummar Musulmi, muke hana su rikon ranar
haihuwar Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah a
matsayin ranar Idi, muke musu gargadin rikon bukin maulidi
a matsayin wani abu na addini da ake neman lada da shi a
wurin Allah Madaukakin Sarki!
Saboda abu ne tabbatacce wurin Maluman Musulunci cewa
Annabi Mai tsira da amincin Allah bai yi bukin maulidi ba,
Sahabbai ba su yi bukin maulidi ba, Taabi'ai ba su yi bukin
maulidi ba, Taabi'ut Taabi'in ba su yi bukin maulidi ba. Duk
kuwa abin da ba zama addini ba a zamanin Sahabbai, da
Taabi'ai, da Taabi'ut Taabi'in tare da kasancewar sababin
yin sa a lokacin nasu' da kuma ikon yin sa daga gare su
yana nan' amma kuma babu Wanda ya yi shi daga cikinsu,
to lalle wannan abin babu ta yadda za a yi ya zamanto
addini karbabbe a wurin na bayansu har zuwa tashin
Kiyama.
Yan'uwa Musulmi! Lalle shi rikon ranar maulidi a matsayin
Idi, da maida shi ranar buki, ba a fara yin shi ba cikin
wannan Al'umma sai cikin karni na hudu na hijirar Annabi
Mai tsira da amincin Allah' watau sai a cikin shekara ta dari
uku da settin da biyu (362). Sannan mutumin da ya fara yin
wannan buki na maulidi shi ne wani sarki dan Shi'ah
Fadimiyyah Mai suna Almu'izzu li Dininl Lah a garin
Alkahira' kamar yadda yake rubuce cikin littattafan
Musulunci da tarihi, da wasunsu, kuna iya duba wadannan
littattafan:-
ﺍﻟﻤﻮﺍﻋﻆ ﻭﺍﻻﻋﺘﺒﺎﺭ ﺑﺬﻛﺮ ﺍﻟﺨﻄﻂ ﻭﺍﻻﺛﺎﺭ ﻟﻠﻤﻘﺮﻳﺰﻱ ١/ ٤٩٠، ﻭﺻﺒﺢ
ﺍﻷﻋﺸﻰ ﻓﻲ ﺻﻨﺎﻋﺔ ﺍﻹﻧﺸﺎﺀ ﻟﻠﻘﻠﻘﺸﻨﺪﻱ ٣/ ٤٩٨، ﻭﺗﺎﺭﻳﺦ ﺍﻻﺣﺘﻔﺎﻝ
ﺑﺎﻟﻤﻮﻟﺪ ﺍﻟﻨﺒﻮﻱ ﻟﻠﺴﻨﺪﻭﺑﻲ ﺹ٦٩، ﻭﺃﺣﺴﻦ ﺍﻟﻜﻼﻡ ﻓﻴﻤﺎ ﻳﺘﻌﻠﻖ ﺑﺎﻟﺴﻨﺔ
ﻭﺍﻟﺒﺪﻋﺔ ﻣﻦ ﺍﻷﺣﻜﺎﻡ ﻟﻤﺤﻤﺪ ﺑﺨﻴﺖ ﺹ٤٤، ٤٥، ﻭﺍﻟﻤﺤﺎﺿﺮﺍﺕ ﺍﻟﻔﻜﺮﻳﺔ
ﻟﻠﺸﻴﺦ ﻋﻠﻲ ﻓﻜﺮﻱ ﺹ٨٤، ﻭﺍﻹﺑﺪﺍﻉ ﻓﻲ ﻣﻀﺎﺭ ﺍﻻﺑﺘﺪﺍﻉ ﻟﻠﺸﻴﺦ ﻋﻠﻲ
ﻣﺤﻔﻮﻅ ﺹ١٢٦، ﻭﺍﻟﺘﺎﺭﻳﺦ ﺍﻟﻌﺒﺎﺳﻲ ﻭﺍﻟﻔﺎﻃﻤﻲ ﻟﻠﺸﻴﺦ ﺍﺣﻤﺪ ﻣﺨﺘﺎﺭ
ﺍﻟﻌﺒﺎﺩﻱ ﺹ٢٦١، ٢٦٢ .
Almawaa'izu wa Litibaar na Maqriizii 1/490, da Subhul
A'ashaa na Qalqashandii 3/498, da Taariikhu Lihtifaali Bil
Maulidin Nabawii na Sanduubii shafi na 69, da Ahsanul
Kalam fi ma yataallaqu bis Sunnati wal Bidi'ati minal Ahkam
na Muhammad Bakhiit shafi na 44,45, da Almuhadharaatul
Fikriyyah na Ali Fikrii shafi na 84, da Al'ibdaa fi Madharri
Libtidaa na Ali Mahfuuz shafi na 126, da Taarikhul Abbaasii
wal Faatimii na Ahmad Mukhtaar Al'abbadii shafi na
261,262.
MALUMAN MUSULUNCI DABAN DABAN SUN HANA YIN
BUKIN MAULIDI:
Yan'uwa Musulmi! Lalle da yawa daga cikin maluman
Musulunci sun gargadi Al'umma sun hana su yin bukin
maulidi da rikon shi a matsayin wata ibadah da za a nemi
lada wurin Allah da ita, kuma sun bayyanar da cewa yin
bukin maulidi bidi'a ce kuma bata.
Daga cikin wadannan malamai akwai manya manyan
malumanmu na mazhabar Malikiyyah, kamar Ibnul Hajj
wanda ya rasu a shekarar hijira ta 732 watau yau da
rasuwarsa shekaru 702 ke nan da suka wuce, da kuma
Umarul Faakihaanii wanda ya rasu a shekarar hijira ta 734
watau yau da mutuwarsa shekara 700 ke nan da suka
wuce, da kuma Ibraahimush Shaatibii wanda ya rasu a
shekarar hijira ta 690 watau yau da rasuwarsa shekara 744
ke nan da suka wuce, da kuma uwa-uba Sheik Uthmanu
Dan Fodiyo wanda ya rasu a shekarar hijira ta 1234 watau
yau shekara 201 ke nan da rasuwarsa.
Amma Sheik Ibnul Hajj ga abin da yake cewa cikin littafin
Almudkhal 2/2, da 2/10-11 :-
(( ﻭﻣﻦ ﺟﻤﻠﺔ ﻣﺎ ﺍﺣﺪﺛﻮﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﻣﻊ ﺍﻋﺘﻘﺎﺩﻫﻢ ﺍﻥ ﺫﻟﻚ ﻣﻦ ﺍﻛﺒﺮ
ﺍﻟﻌﺒﺎﺩﺍﺕ ﻭﺍﻇﻬﺮ ﺍﻟﺸﻌﺎﺋﺮ ﻣﺎ ﻳﻔﻌﻠﻮﻧﻪ ﻓﻲ ﺷﻬﺮ ﺭﺑﻴﻊ ﺍﻻﻭﻝ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ
ﻭﻗﺪ ﺍﺣﺘﻮﻯ ﻋﻠﻰ ﺑﺪﻉ ﻭﻣﺤﺮﻣﺎﺕ ﺟﻤﻠﺔ ﻓﻤﻦ ﺫﻟﻚ ﺍﺳﺘﻌﻤﺎﻟﻬﻢ ﺍﻟﻤﻐﺎﻧﻲ
ﻭﻣﻌﻬﻢ ﺁﻻﺕ ﺍﻟﻄﺮﺏ(( ﺍﻟﻰ ﺍﻥ ﻗﺎﻝ: )) ﻭﺍﻥ ﺧﻼ ﻣﻨﻪ ﻭﻋﻤﻞ ﻃﻌﺎﻣﺎ ﻓﻘﻂ
ﻭﻧﻮﻯ ﺑﻪ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﻭﺩﻋﺎ ﺍﻟﻴﻪ ﺍﻻﺧﻮﺍﻥ ﻭﺳﻠﻢ ﻣﻦ ﻛﻞ ﻣﺎ ﺗﻘﺪﻡ ﺫﻛﺮﻩ ﻓﻬﻮ
ﺑﺪﻋﺔ ﺑﻨﻔﺲ ﻧﻴﺘﻪ ﻓﻘﻂ ﺇﺫ ﺍﻥ ﺫﻟﻚ ﺯﻳﺎﺩﺓ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻭﻟﻴﺲ ﻣﻦ ﻋﻤﻞ
ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺍﻟﻤﺎﺿﻴﻦ ﻭﺍﺗﺒﺎﻉ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺍﻭﻟﻰ ﺑﻞ ﺃﻭﺟﺐ ﻣﻦ ﺍﻥ ﻳﺰﻳﺪ ﻧﻴﺔ
ﻣﺨﺎﻟﻔﺔ ﻟﻤﺎ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻋﻠﻴﻪ ﻷﻧﻬﻢ ﺍﺷﺪ ﺍﺗﺒﺎﻋﺎ ﻟﺴﻨﺔ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺗﻌﻈﻴﻤﺎ ﻟﻪ ﻭﺳﻨﺘﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﻟﻬﻢ ﻗﺪﻡ ﺍﻟﺴﺒﻖ
ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺒﺎﺩﺭﺓ ﺍﻟﻰ ﺫﻟﻚ ﻭﻟﻢ ﻳﻨﻘﻞ ﻋﻦ ﺍﺣﺪ ﻣﻨﻬﻢ ﺍﻧﻪ ﻧﻮﻯ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﻭﻧﺤﻦ
ﻟﻬﻢ ﺗﺒﻊ ﻓﻴﺴﻌﻨﺎ ﻣﺎ ﻭﺳﻌﻬﻢ )).
Ma'ana: ((Yana daga cikin jumlar abin da suka kirkira na
bidi'o'i tare da akidar cewa hakan yana daga cikin manyan
ibadodi, kuma yana daga cikin alamomin Musulunci mafi
fita fili: abin nan da suke aikatawa cikin watan Rabii'ul
Awwal na bukin maulidi. Shi dai maulidi ya tattari
abubuwan haramun da yawa a dunkule, daga cikinsu akwai
wake-wake da suke yi tare da Kayan kade-kade .... To
amma idan yin maulidi ya wifinta daga yin wake-wake tare
da kayan kade-kade mai yin maulidin ya yi abinci kawai ya
yi nufin maulidi da shi ya kira yan'uwa zuwa cin abincin, to,
yin hakan ya zama bidi'ah saboda niyyar maulidin da ya yi,
domin niyyar maulidin kari ne a cikin Addini ba ya kuma
daga cikin ayyukan Salaf Magabata ba, bin Magabata kuwa
shi ne ya fi dacewa, kai shi ne ma wajibi da a ce mutum zai
kara wani abu sabanin abin da suka kasance a kansa,
domin su Magabata su ne suka fi kowa yin koyi da Manzon
Allah, kuma su ne suka fi kowa girmama shi da girmama
sunnarsa, kuma su suke da kafar rigaya wajen takawa
zuwa ga abin da yake alheri ne, babu kuma mutum daya da
ya ciro yin niyyar maulidi daga dayansu, mu kuwa sauran
Musulmi mabiya ne gare su, dukkan abin da ya wadatar da
su na addini shi ne zai wadatar da mu)).
Sannan Imamul Faakihaanii ya ce cikin Risalarsa ta maulidi
mai suna Almurid fil Kalaami alaa Hukmil Maulid :-
(( ﻻ ﺍﻋﻠﻢ ﻟﻬﺬﺍ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﺍﺻﻼ ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺏ ﻭﻻ ﺳﻨﺔ ﻭﻻ ﻳﻨﻘﻞ ﻋﻤﻠﻪ ﻋﻦ ﺍﺣﺪ
ﻣﻦ ﻋﻠﻤﺎﺀ ﺍﻻﻣﺔ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻫﻢ ﺍﻟﻘﺪﻭﺓ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﺍﻟﻤﺘﻤﺴﻜﻮﻥ ﺑﺂﺛﺎﺭ
ﺍﻟﻤﺘﻘﺪﻣﻴﻦ ﺑﻞ ﻫﻮ ﺑﺪﻋﺔ ﺍﺣﺪﺛﻬﺎ ﺍﻟﺒﻄﺎﻟﻮﻥ ﻭﺷﻬﻮﺓ ﻧﻔﺲ ﺍﻋﺘﻨﻰ ﺑﻬﺎ
ﺍﻻﻛﺎﻟﻮﻥ ﺑﺪﻟﻴﻞ ﺍﻧﺎ ﺍﺫﺍ ﺃﺩﺭﻧﺎ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻷﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﺨﻤﺴﺔ ﻗﻠﻨﺎ ﺍﻣﺎ ﺍﻥ ﻳﻜﻮﻥ
ﻭﺍﺟﺒﺎ ﺍﻭ ﻣﻨﺪﻭﺑﺎ ﺍﻭ ﻣﺒﺎﺣﺎ ﺍﻭ ﻣﻜﺮﻭﻫﺎ ﺍﻭ ﻣﺤﺮﻣﺎ ﻭﻫﻮ ﻟﻴﺲ ﺑﻮﺍﺟﺐ
ﺇﺟﻤﺎﻋﺎ ﻭﻻ ﺑﻤﻨﺪﻭﺏ ﻻﻥ ﺣﻘﻴﻘﺔ ﺍﻟﻤﻨﺪﻭﺏ ﻣﺎ ﻃﻠﺒﻪ ﺍﻟﺸﺮﻉ ﻣﻦ ﻏﻴﺮ ﺫﻡ
ﻋﻠﻰ ﺗﺮﻛﻪ ﻭﻫﺬﺍ ﻟﻢ ﻳﺄﺫﻥ ﻓﻴﻪ ﺍﻟﺸﺮﻉ ﻭﻻ ﻓﻌﻠﻪ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﻭﻻ ﺍﻟﺘﺎﺑﻌﻮﻥ ﻭﻻ
ﺍﻟﻌﻠﻤﺎﺀ ﺍﻟﻤﺘﺪﻳﻨﻮﻥ ﻓﻴﻤﺎ ﻋﻠﻤﺖ ﻭﻫﺬﺍ ﺟﻮﺍﺑﻲ ﻋﻨﻪ ﺑﻴﻦ ﻳﺪﻱ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻥ ﻋﻨﻪ
ﺳﺌﻠﺖ ﻭﻻ ﺟﺎﺋﺰ ﺍﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﻣﺒﺎﺣﺎ ﻻﻥ ﺍﻻﺑﺘﺪﺍﻉ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻟﻴﺲ ﻣﺒﺎﺣﺎ
ﺑﺈﺟﻤﺎﻉ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﻓﻠﻢ ﻳﺒﻖ ﺍﻻ ﺍﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﻣﻜﺮﻭﻫﺎ ﺍﻭ ﺣﺮﺍﻣﺎ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma'ana: ((Ban san wata hujja da za ta halatta yin maulidi
ba a cikin Alkur'ani da Sunnah, kuma ba a nakalto yin bukin
maulidi koda daga mutum daya ba cikin maluman Al'umma
wadanda su ne abin koyi a cikin Addini , kuma su ne ke riko
da maganganun magabata, kai, abin da dai yake ciki shi ne:
shi dai maulidi wata biri'ah ce da marasa aikin yi suka
kirkira kuma sha'awar son rai ce da masu cin dukiyar
mutane cikin karya suka runguma, saboda shi dai bukin
maulidi idan muka shimfida shi a kan hukunce-hukuncin
nan guda biyar sai mu ce: ko dai ya zama wajibi, ko kuwa
ya zama mustahabbi, ko kuwa ya zama mubaahi, ko kuwa
ya zama makruuhi, ko kuwa ya zama haraamun, to in mun
yi hakan za mu ga cewa shi dai ba wajibi ba ne bisa
Ijmaa'in Malamai, shi kuwa ba mustahabbi ba ne domin
abin da ake nufi da mustahabbi shi ne abin da Shari'ah ta
ce a yi ba tare da an zargi Wanda ya ki yi ba, shi kuwa
maulidi Shari'ah ba ta ce a yi shi ba, kuma ni a sanina
Sahabbai, da Taabi'ai, da malamai masu riko da Addini ba
su yi shi ba, wannan shi ne jawabina a gaban Allah a kan
bukin maulidi in har aka tambaye ni. Kuma ba zai halatta
ba a ce Maulidi ya zama mubaahi saboda kirkiran wani abu
cikin addini ba zai zama mubaahi ba a bisa Ijmaa'in
Musulmi, saboda haka babu abin da ya rage face maulidi ya
zama makruuhi ko kuwa haramun)). Intaha.
Sannan Imamush Shaatibii ya ce -a lokacin da yake yin
bayanin ma'anar bidi'ah- cikin littafinsa mai suna Alitisam
1/50,53 :-
(( ﻋﺒﺎﺭﺓ ﻋﻦ ﻃﺮﻳﻘﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻣﺨﺘﺮﻋﺔ ﺗﻀﺎﻫﻲ ﺍﻟﺸﺮﻋﻴﺔ ﻳﻘﺼﺪ
ﺑﺎﻟﺴﻠﻮﻙ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﺍﻟﻤﺒﺎﻟﻐﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﺘﻌﺒﺪ ﻟﻠﻪ ﺳﺒﺤﺎﻧﻪ .... ﻳﻌﻨﻲ ﺍﻧﻬﺎ ﺗﺸﺎﺑﻪ
ﺍﻟﻄﺮﻳﻘﺔ ﺍﻟﺸﺮﻋﻴﺔ ﻣﻦ ﻏﻴﺮ ﺍﻥ ﺗﻜﻮﻥ ﻓﻲ ﺍﻟﺤﻘﻴﻘﺔ ﻛﺬﻟﻚ ﺑﻞ ﻫﻲ ﻣﻀﺎﺩﺓ
ﻟﻬﺎ ﻣﻦ ﺃﻭﺟﻪ ﻣﺘﻌﺪﺩﺓ .... ﻣﻨﻬﺎ ﺍﻟﺘﺰﺍﻡ ﺍﻟﻜﻴﻔﻴﺎﺕ ﻭﺍﻟﻬﻴﺌﺎﺕ ﺍﻟﻤﻌﻴﻨﺔ
ﻛﺎﻟﺬﻛﺮ ﺑﻬﻴﺌﺔ ﺍﻻﺟﺘﻤﺎﻉ ﻋﻠﻰ ﺻﻮﺕ ﻭﺍﺣﺪ ﻭﺍﺗﺨﺎﺫ ﻳﻮﻡ ﻭﻻﺩﺓ ﺍﻟﻨﺒﻲ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻋﻴﺪﺍ ﻭﻣﺎ ﺃﺷﺒﻪ ﺫﻟﻚ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma'ana: ((Bidi'ah wata kirkirarriyar hanya ce cikin addini
mai kama da addinin gaskiya ana nufin kaiwa matuka
matuka cikin bautar Allah da yin ta .., ina nufin ita bidi'ah
tana kama da hanyar Shari'ah ba tare da ta kasance hanyar
Shari'ah ta hakika ba, kai a gaskiya ma tana karo ne da
hanyar Shari'ah ta fiskoki da yawa ... Daga cikinsu akwai
lazimtar wasu irin siffofi ayyanannu, kamar zikirin da ake yi
a bisa tsarin haduwa a kan sauti daya' da kuma rikon ranar
haihuwar Manzon Allah mai tsira da amincin Allah a
matsayin idi, da abin da yake Kama da haka)).
Sannan Shehu Uthmanu Dan Fodiyo ya ce cikin littafinsa
mai suna Ihyaaus Sunnah wa Iqmaadul Bid'ah shafi na
104 :-
(( ﻓﺎﻥ ﻗﻠﺖ ﻣﺎ ﺣﻜﻢ ﻣﺎ ﻳﻔﻌﻞ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻲ ﺷﻬﺮ ﺭﺑﻴﻊ ﺍﻻﻭﻝ ﻓﻲ ﻳﻮﻡ
ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﺍﻭ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺍﻟﺴﺎﺑﻊ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﻣﻦ ﺍﺟﺘﻤﺎﻉ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻟﻠﺬﻛﺮ ﻭﺍﻟﻄﻌﺎﻡ
ﺍﻟﺬﻱ ﻳﻌﻤﻠﻮﻧﻪ ﻟﺬﻟﻚ؟ ﻗﻠﺖ: ﺍﻧﻪ ﺑﺪﻋﺔ ﻣﻜﺮﻭﻫﺔ ﺍﻥ ﺧﻼ ﻋﻦ ﻛﻞ ﻣﻌﺼﻴﺔ .
ﻭﻗﻴﻞ: ﺍﻥ ﺍﻟﺼﻮﺍﺏ ﺍﻥ ﻋﻤﻞ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﺍﻟﺸﺮﻳﻒ ﺍﻟﻨﺒﻮﻱ ﻣﻦ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﺍﻟﺤﺴﻨﺔ
ﺍﻟﻤﻨﺪﻭﺑﺔ ﺍﺫﺍ ﺧﻼ ﻋﻦ ﻣﻌﺼﻴﺔ . ﻭﺃﻣﺎ ﻣﺎ ﻳﻌﺘﺎﺩﻩ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻲ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﺰﻣﺎﻥ
ﻓﻲ ﺫﻟﻚ ﻣﻦ ﺍﺧﺘﻼﻁ ﺍﻟﺮﺟﺎﻝ ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﻓﻤﻌﺎﺫ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻥ ﻳﻘﻮﻝ ﺍﺣﺪ
ﺑﺠﻮﺍﺯﻩ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma'ana: ((Idan ka ce: Mene ne hukuncin abin da mutane
suke yi a cikin watan Rabii'ul Awwal a ranar maulidi ko
kuwa a ranar bakwai ga maulidi na taruwar jama'a saboda
yin zikiri da cin abincin da aka yi tanadinsa saboda hakan?
Sai in ce: Wannan bidi'ah ce makruuhiyah in yin maulidin ya
wofinta daga dukkan sabon Allah. Amma kuma wasu sun
ce: Abin da yake daidai shi ne shi bukin maulidin Annabi
yana daga cikin bidi'o'i masu kyau matukar dai ya wofinta
daga ko wane sabon Allah. To amma abin da mutane suka
Saba yin shi a maulidi a wannan zamani na cakuda
tsakanin maza da mata a'uuzu billahi da wani mutum zai ce
halal ne)).
Wannan shi ne abin da malumanmu na mazhabar
Malikiyyah suka fada game da bukin maulidi.
Sannan Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah wanda ya rasu a
shekarar hijira ta 728 watau shekaru 706 ke nan da suka
wuce shi ya yi maganar maulidi ya kuma tabbatar da cewa
maulidi bidi'ah ce, ya rubuta cikin littafinsa mai suna
Iqtidhaa'us Siraa'til Mustaqiim 2/123-124 :-
(( ﻭﻛﺬﻟﻚ ﻣﺎ ﻳﺤﺪﺛﻪ ﺑﻌﺾ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺍﻣﺎ ﻣﻀﺎﻫﺎﺓ ﻟﻠﻨﺼﺎﺭﻯ ﻓﻲ ﻣﻴﻼﺩ
ﻋﻴﺴﻰ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻭﺍﻣﺎ ﻣﺤﺒﺔ ﻟﻠﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺗﻌﻈﻴﻤﺎ
ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻗﺪ ﻳﺜﻴﺒﻬﻢ ﻋﻠﻰ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﻤﺤﺒﺔ ﻭﺍﻻﺟﺘﻬﺎﺩ ﻻ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﻣﻦ ﺍﺗﺨﺎﺫ
ﻣﻮﻟﺪ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻋﻴﺪﺍ ﻣﻊ ﺍﺧﺘﻼﻑ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻲ ﻣﻮﻟﺪﻩ
ﻓﺎﻥ ﻫﺬﺍ ﻟﻢ ﻳﻔﻌﻠﻪ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﻣﻊ ﻗﻴﺎﻡ ﺍﻟﻤﻘﺘﻀﻲ ﻟﻪ ﻭﻋﺪﻡ ﺍﻟﻤﺎﻧﻊ ﻣﻨﻪ ﻟﻮ
ﻛﺎﻥ ﺧﻴﺮﺍ ﻭﻟﻮ ﻛﺎﻥ ﻫﺬﺍ ﺧﻴﺮﺍ ﻣﺤﻀﺎ ﺍﻭ ﺭﺍﺟﺤﺎ ﻟﻜﺎﻥ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻨﻬﻢ ﺍﺣﻖ ﺑﻪ ﻣﻨﺎ ﻓﺎﻧﻬﻢ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﺍﺷﺪ ﻣﺤﺒﺔ ﻟﺮﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺗﻌﻈﻴﻤﺎ ﻟﻪ ﻣﻨﺎ ﻭﻫﻢ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﺍﺣﺮﺹ ﻭﺍﻧﻤﺎ ﻛﻤﺎﻝ ﻣﺤﺒﺘﻪ
ﻭﺗﻌﻈﻴﻤﻪ ﻓﻲ ﻣﺘﺎﺑﻌﺘﻪ ﻭﻃﺎﻋﺘﻪ ﻭﺍﺗﺒﺎﻉ ﺃﻣﺮﻩ ﻭﺇﺣﻴﺎﺀ ﺳﻨﺘﻪ ﺑﺎﻃﻨﺎ
ﻭﻇﺎﻫﺮﺍ ﻭﻧﺸﺮ ﻣﺎ ﺑﻌﺚ . ﺑﻪ ﻭﺍﻟﺠﻬﺎﺩ ﻋﻠﻰ ﺫﻟﻚ ﺑﺎﻟﻘﻠﺐ ﻭﺍﻟﻴﺪ ﻭﺍﻟﻠﺴﺎﻥ
ﻓﺎﻥ ﻫﺬﻩ ﻃﺮﻳﻘﺔ ﺍﻟﺴﺎﺑﻘﻴﻦ ﺍﻷﻭﻟﻴﻦ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻬﺎﺟﺮﻳﻦ ﻭﺍﻷﻧﺼﺎﺭ ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ
ﺍﺗﺒﻌﻮﻫﻢ ﺑﺈﺣﺴﺎﻥ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma'ana: ((Haka nan abin da sashin mutane ke kirkira ko dai
saboda koyi da Kiristoci cikin bukin Kirsimeti' ko kuwa
saboda son Annabi mai tsira da amincin Allah da girmama
shi, zai yiwu Allah ya ba su lada a kan nuna kokari da
soyayya' amma ba zai ba su lada a kan bidi'o'in rikon
maulidin Annabi mai tsira da amincin Allah a matsayin idi
ba duk da yake ma masu tarihi sun yi sabani a kan wace
rana ce da wani wata ne aka haife shi! Shi dai bukin maulidi
babu wani daga cikin magabata da ya yi shi duk kuwa da
cewa dukkan dalilan da ake bayarwa na yin bukin a yanzu
akwai su a wancan lokacin ma, kuma babu wani abu da zai
hana su yin bukin inda yin shi alheri ne. Lalle ne da yin
bukin maulidi tsantsar alheri ne to da Salaf Magabata su
suka fi cancantar yin sa a kanmu, saboda sun fi mu son
Manzon Allah mai tsira da amincin Allah da girmama shi,
kuma sun fi kowa son aikata alheri. Lalle cikar soyayya da
girmamawa ga Annabi tana cikin bin shi ne da yi masa
da'ah da bin umurnin shi, da raya sunnar shi ciki da waje,
da yada abin da aka aiko da shi, da yin jihadi da zuciya, da
hannu, da harshe a kan hakan wannan ita ce hanyar
Magabata na farko daga cikin Muhajirai da Ansarawa da
wadanda suka bi su da kyautayi)).
Yan'uwa Musulmi! Wannan shi ne matsayin bukin maulidi
daga bakunan wadannan gagga-gaggan maluman
Musulunci, tare ma kuma da cewa Maluman tarihi da siiirah
sun yi sabani game da ranar haihuwar shi Annabi mai tsira
da amincin Allah, a inda wasu suka ce:
1- An haife shi ne a ran biyu ga watan Rabii'ul Awwal.
2- Wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran takwas ga
watan Rabii'ul Awwal.
3- Wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran goma ga watan
Rabii'ul Awwal.
4- Wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran goma sha
biyumga watan Rabii'ul Awwal.
5- wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran goma sha
bakwai ga watan Rabii'ul Awwal.
6- Wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran ashrin ga watan
Rabii'ul Awwal.
7- Wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran goma sha biyu
ga watan Ramadhan.
Domin ganin wannan sabanin sai ku dubi littafin Taariikhul
Islam na Imamuz Zahbii a Juz'in Siirah shafi na 25-27, da
kuma littafin Albidaayatu wan Nihaayatu na Alhaafiz Ibnu
Katheer 2/662.
Yan'uwa Musulmi! Kauli daidai har bakwai a kan ranar
haihuwar Annabi mai tsira da amincin Allah babu kuma
wani wanda ya isa ya ce: wannan kauli shi ne hakikanin
gaskiya wancan kaulin kuma ba gaskiy ba ne, saboda abu
ne da ya faru kafin zuwan Musulunci kuma bayan shi
Musulunci ya zo bai tabbatar da ranar haihuwar ba ta
hanyar wahayi saboda rashin muhimmancin yin hakan a
cikin Addini.
Ke nan ware wata rana daga cikin ranakun nan da aka
ambata da riyawar cewa ita ce ranar da aka haifi Manzon
Allah mai tsira da amincin Allah akwai nau'i na karya da
shedan zur a cikin yin hakan. Allah ya tsare mu da son
zuciya.
Wannan shi ne kashi na farko game da bayananmu a kan
bukin maulidi, kashi biyu na tafe in sha Allahu Ta'ala, kuma
zai yi bayani ne game da shubuhohin da yan bidi'ah ke
ambatawa domin tabbatar da bidi'ar maulidi.
Allah Madaukakin Sarki muke roko da Ya nuna mana
gaskiya gaskiya ce ya ba mu ikon bin ta Ya nuna mana
karya karya ce Ya ba mu ikon kin ta. Ameen.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve