Tuesday, 29 November 2016

LABARAI A TAKAICE


*Gwamnan Ondo mai barin gado Olusegun Mimiko ya taya gwamna mai jiran gado Rotimi Akeredolu murnar lashe zaben gwamnan jihar da ke kudu maso yammacin Najeriya.

*Wannan dai wani ci gaba ne don Mimiko na jam'iyyar PDP ya taya dan APC murna wanda ya kada dan takarar sa Eyitayo Jegde.

*A gefe guda PDP mai adawa ta ki amincewa da sakamakon zaben da bukatar a soke shi.

*Kakakin bangaren Ahmed Makarfi na jam'iyyar ta PDP Dayo Adeyeye ya ce jam'iyyar ta umurci reshen ta na Ondo ya shigar da kara a kotun sauraron karar zaben jihar.

*Hukumar zaben Najeriya INECta bakin daraktan ta na labaru Barista Osaze Uzi ta ce an gudanar da zaben gaskiya  kuma sakamakon zaben shine ainihin abun da al'ummar jihar Ondo su ka zaba.

*Ina shawartar 'yan Nijeriya da su goyi bayan kokarin da gwamnatin Buhari take yi domin shawo kan matsalolin da take fama da su a Nijeriya, Inji tsohon shugaban Naijeriya Yakubu Gowon

*A wani mataki na wanke kansa, Tsohon Shugaban Kwamitin Dattawa na jam'iyyar PDP, Cif Tony Anenih ya bayyana cewa zamanin da Shugaba Buhari ya yi Shugaban mulkin soja a shekarar 1985 ya bayar da umarnin garkame shi saboda kawai ya mallaki tarin dukiya.

*A cewar Tony Anenih a iya saninsa babu wani laifi da ya yi a wancan lokaci illa kawai wasu makiyansa ne suka kai kokensa a matsayinsa na Shugaban jam'iyyar NPN na jihar Bendel inda ya ce an kai shi gidan kurkuku na Kirikiri wanda a can ya hadu da wasu gwamnonin farar hula wadanda suka taba bayar da umarnin zartar da hukuncin kisa a kan wasu masu laifi a lokacin suna kan mulki.

*Duk Mutanen Dake Kusa Da Buhari Ba sa Iya Fada Masa Gaskiya, Cewar Buba Galadima

*Buba Galadima ya kuma kara da cewa idan har shugaba Buhari na bukatar ya fitar da kansa daga kunya a wurin 'yan Nijeriya, dole sai ya yi tankade rairaya a cikin mukarrabansa.

*Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ba gaskiya bane maganganun da ya ke ji ana ta yawo da shi cewa wai yana da matsala da Tinubu ko kuma jam'iyyar APC na da matsala da Tinubu.

*Buhari ya ce Tinubu ba mutum bane wanda jam'iyyar APC za ta tayi wasa dashi musamman ganin irin dimbin gudunmawar da ya ke ba jam'iyyar tun kafuwarta.
Buhari ya ce zantukan da ake ta yadawa na kanzon kurege ne domin basu da wata madafa.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
29/Safar/1438
29/November/2016

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve