*FITOWA TA 15.
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA KUR'ANI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
Bayan mun gabatar da bayani a kan wannan akida kamar yadda
take a cikin littafan yan Shi'a masu inganci a wajensu,muna ganin babu
karin bayani dangane da abinda akidar ta tattare na kafirci da jahilci
da bata.Amma saboda yankan hanzari ga masu kiran kansu yan Shi'a, bari
muyi bayanin kafircin wannan akida a takaice.
Da farko dai akidar ta karyata Alkur'ani mai girma saboda a
cikinsa Allah mai girma da daukaka ya tabbatar da cewa ya tsare
Littafinsa ta yadda kari ko ragi ba za su shige shi ba.Ubangiji
Madaukaki ya ce,"Lalle,mu ne muka saukar da Ambato (Alkur'ani), kuma
lalle mu,masu kiyayewa ne gare shi."(Suratul Hijr:9). A wata ayar
kuma,ya tabbatar da cewa barna ba ta shiga wannan littafi ko ta halin
kaka: "Wadannan da suka kafirta game da Alkur'ani a lokacin da ya je
musu,kuma lalle ne,hakika,littafi ne mabuwayi.Barna ba za ta zo ba
daga baya gare shi .Saukarwa ce daga Mai Hikima,Godadde." Suratu
Fussilat:41-42).
Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 16 Insha Allah.
Abu Aisha Journalist.
Jibwis Social Media Katsina.
Thursday, 28 September 2017
*FITOWA TA 14.
*Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
Daga cikin manyan Sufaye na wannan mataki akwai Ibrahim binu
Adham.Shi binu Adham dan sarki ne Wanda ya taso cikin rayuwa ta jin
dadi irin rayuwar ya'yan fada,amma daga baya sai ya karkata zuwa
Sufanci, ya shagala da ibada da gudun duniya. Ya rabu da dukkan wani
jin dadi irin na yan sarki,kuma ya rika cin abinci da gumin
goshinsa.Daga bisani ya yi kaura daga garinsu,Kauratu Balakh,ya tafi
da niyyar aikin Hajji.Ya rasu a kasar sham,a kan hanyarsa ta zuwa
Makka.
Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 15 Insha Allah.

Tuesday, 26 September 2017
*FITOWA TA 14.
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA KUR'ANI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
Har yau,wani malamin nasu ya ba da bayani mai kama da
wannan.Ya ce,"Bayan rasuwar Annabi,Sarkin Musulmi (yana nufin Ali) ya
dauko Alkur'ani a cikin mayafinsa,ya kawo wa Abubakar da Umar suna
zaune a Masallaci su da wasu mutane. Ya ba su shi,amma sai suka ce:Ba
mu bukatar Kur'aninka;muna da namu Kur'anin,ya ishe mu! Sai ya ce:Shi
ke nan,ba za ku kara ganin sa ba daga yau,sai Mahadi ya bayyana!"[Duba
NUR AL'ANWAR FI SHARHIS SAHIFATIS SAJADIYYA na Ni'imatullahi
Aljaza'iri,bugun Darul Mahajjatil Baida,Bairut 1420,shafi na 175.]
Wadannan bayanai daga malaman Shi'a,idan sun gasgata,suna
tabbatar da cewa Kur'anin yan Shi'a ya kasance akwai shi a hannun
Imamansu,kuma almajiran Imamai sun karanta shi har lokacin da imami na
12 ya shiga dashi kogo inda ya faku fakuwarsa ta karshe.Saboda haka
sai su jira shi daga nan har sanda jaki ya tsiri kaho!
Akwai wani dan Shi'a wanda ya taba yin wata burga.Ya dauko
Kur'ani cikakke na Musulmi, wanda aka buga a kasar Iran,ga tambarin
Jumhuriyyar Islama rangadau a bangin littafin.Sa'annan ya ce,"kun ce
yan Shi'a ba su yarda da Kur'ani ba,ya akayi suka buga wannan? " Sai
aka ce masa,ai buga Kur'ani ba shi ne yarda da shi ba.Idan yan Shi'a
sun yarda da Alkur'ani don me suke kafirta wadanda Alkur'ani ya yi wa
shaida da imani,watau Sahabban Annabi(S.A.W)? Sai gogan na ka ya yi
turus! Allah ya tsarshe mu bata.

*FITOWA TA 13
*Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
MATAKIN IBADA DA GUDUN DUNIYA
Matakin Ibada shi ne mataki na farko da Sufanci ya
taka,kuma wasu daga cikin sifofin da Sufanci yake da su a wannan
mataki sun lizimce shi a sauran dukkan matakan.Mafi bayyanar wadannan
sifofi su ne:lazimtar ibada,gudun duniya,tsantseni,ikhlasi,gwagwarmaya
da yakin zuciya da kuma riko da hukunce-hukuncen shari'a.
A wannan mataki,Sufaye sun siffantu da sifofin komawa ga Allah
dungurum cikin dukkan lamurra,juya baya ga duniya da
kyale-kyalenta,kauracewa mutane da barin cudanya da su,da shiga halwa
domin ibada.
Yawancin ra'ayoyin Sufaye da sifofin Sufanci a wannan mataki
sun samo tushe daga Musulunci, kuma sun dogara a kan bin shari'a da
koyi da magabata,watau Sahabban Annabi(S.A.W) da Tabi'ansu.Babu wata
falsafa,bakon tunani ko gyauron wani addini da ya shiga Sufanci a
wannan mataki,sai fa abinda ba'a rasa ba.
Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 14 Insha Allah.

Monday, 25 September 2017
*FITOWA TA 13
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA KUR'ANI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
Yan Shi'a suna kudure cewa Imaminsu na 12,wanda suke kira
Mahadi ya faku fakuwa biyu,babba da karama.A lokacin karamar
fakuwa,wacce ta yi tsawon shekara 65,ya rika saduwa da manyan
almajiransa wadanda ya rika aiko su da sakwanni zuwa ga mabiyansa.Kuma
a shekara ta 259 bayan Hijira, ya shiga fakuwa babba,wacce ya kai har
zuwa yau,kuma wacce a cikinta ba ya saduwa da kowa.Wannan babbar
fakuwa za ta kare a karshen duniya, sa'ad da Mahadin zai bayyana don
ya kaddamar da wasu ayyuka masu ban tsoro da ban mamaki.[Domin bayanin
wannan tatsuniya,duba A CRITICAL REVISION OF SHI'A na Imam Musa
Musawi,bugun the supreme Islamic Council,
Columbia-Amurka,1412/1992,shafi na 77-78.]
Mai son ganin wadannan ayyuka,sai ya duba littafinmu mai taken MUGUN
NUFIN YAN SHI'A GA AL'UMMA.

*FITOWA TA 12
*Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
YADUWAR SUFANCI
Sufanci ya yadu yaduwa mai yawa a lokaci kankane.Har ya
zuwa karshen karni na biyu,Sufanci bai wuce garuruwan kufa da Basra
ba.Amma kafin karni na uku ya shude,sai da ya game manyan kasashen
Musulunci kamar Misira,Naisabur,Balah,Sham,Bagdada da sauransu.
Daga nan kuma sai Sufanci ya fara yaduwa.Jama'a sun yi
ta shigar sa kuma nashadin Sufaye ya yi ta karuwa.Suka tashi tsaye
wajen yada shi da karfafa tushensa.Suka WALLAFAR littafai masu yawa
don cimma wannan manufa.Daga nan ne Sufanci ya kama hanya zuwa
matsayinsa kamar yadda muka san shi a yau.A kan wannan hanya tasa ya
taka matakai guda uku.
Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 13 Insha Allah.

Friday, 22 September 2017
*FITOWA TA 11
*Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
Idan muka lura da kyau daga abinda ya gabata na hasashe
uku da muka ambata a sama,za mu gane cewa duka masu wadannan hasashe
sun yi kusuri wajen fahimtar Sufanci, domin sun dube shi ta bangare
guda kawai a yayin da suka kawar da kai ga barin wasu bangarorin.Masu
hasashe na daya,wadanda suke su raba Sufanci cancakar da Musulunci,
sun mayar da shi ga falsafar Girkawa. Wadannan mutane sun kau da kai
ga barin wasu bangarori na Sufanci wadanda babu mai musun cewa daga
Musulunci suke.Masu hasashe na biyu,wadanda dama yawancinsu
gabasawan-giri ne kamar yadda muka gabatar,sun ce Kiristanci shi ne
tushen Sufanci. Su kuwa masu hasashe na uku,wadanda yawancinsu Sufaye
ne su da kansu,sun nace akan cewa tafarkinsu ya samo tushe daga
addinin Musulunci tsintsarsa.
Amma gaskiyar lamarin ita ce,Sufanci bai da tushe guda,domin
kuwa ya samo asali daga wurare dabam-daban.Wannan ya sa ya kunshi
abubuwa mabambanta wadanda kuma suka yi nesa da juna.A cikin Sufanci
akwai Musulunci da falsafar Girkawa, da addinin Yahudu da Nasara,da
kuma gyauron tsoffin addinai na Gabas mai Nisa kamar Budanci na kasar
Sin da Indiya.Wannan ita ce hakikanin magana dangane da tushen
Sufanci, kuma a fili take ga duk mutumin da ya san Sufanci sani na
hakika.
Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 12 Insha Allah.

Wannan ya sa yan Shi'a suke kalubalantar mutane da
cewa,idan gaskiya ne suna da nasu Kur'ani dabam,kamar yadda ake
dangana musu(ko da yake mai karatu yana iya ganin cewa ruwayoyinsu ne
suka tabbatar da samuwarsa)to don me ba'a fito musu da shi su gan
shi?Su kanyi tambaya:Ina Kur'anin nasu yake?
To wannan tambaya tasu malamansu sun amsa ta da
kansu.Shaihinsu,Hussain Alkhurasani yana cewa "Mu yan Shi'a muna
kudure cewa akwai wani Alkur'ani da Imam Ali ya rubuta da hannunsa mai
albarka, bayan da ya kare yi wa Annabi sutura kuma ya zartar da
wasiyyarsa.Littafin ya ci gaba da zama a hannun Imamai a matsayin
amana daga Allah har ya iso ga Imam Mahadi wanda ya adana shi kuma zai
fito da shi a yayin da zai bayyana." [Duba Al'islam ala Dau'it
Tashayyu'i na Hussain Alkhurasani,ba tarihi,shafi na 204.]
Wannan ruwaya yana tabbatar da cewa kur'anin yan Shi'a ya
kasance akwai shi,kuma ya ci gaba da zama a hannun Imamai har na
tsawon kimanin shekaru 250 daga zamanin Sayyidina Ali(R.A) zuwa
zamanin mahadinsu(watau Imaminsu na 12)wanda aka haife shi a shekara
ta 225 bayan Hijira.Wannan Imamin nasu shi ne ya tafi da littafin a
lokacin babbar fakuwarsa,kuma zai komo da shi a lokacin da zai bayyana
a karshen duniya.

Thursday, 21 September 2017
*FITOWA TA 11
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA KUR'ANI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
Watakila mai karatu ya yi tambaya:Don me yan Shi'a ba su buga
wannan tafkeken "kur'ani" nasu,wanda ya ninka na Musulmi har sau uku,
su sayar a kasuwa? Amsa ita ce,abinda yake hana su bayyana Wannan
littafi nasu shi ne takiyya,watau munafunci da yaudara!! A hakika yan
Shi'a ba Kur'aninsu kadai suke boyewa ba;akidarsu ta takiyya tana
umarnin su da boye manyan littafan malamansu,wadanda suka kunshi
akidojinsu da manufofinsu,sai ga manyan mabiyansu wadanda suka riga
suka yi zurfi a cikin tafarkinsu.Kadan daga cikin littafansu suke
sayarwa a kasuwa,sauran sai dai a same su a manyan cibiyoyinsu da
makarantunsu.Kur'aninsu kuwa,idan akwai shi cikakke,to babu shakka ba
mai ganin sa sai manyan shaihinnansu da,sai kuma almajirai amintattu.
Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 12 Insha Allah.
Abu Aisha Journalist
Jibwis Social Media Katsina

*FITOWA TA 10
*Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
HASASHE NA UKU
hasashe na uku yana mayar da Sufanci ya zuwa ga tushen
Musulunci tsintsa,watau zuwa ga Alkur'ani da Sunnar Annabi(S.A.W).Ga
masu wannan ra'ayi,ayoyin Alkur'ani da hadisan Annabi(S.A.W) da suke
umarni da tsoron Allah, tuba,ikhlasi ga Allah da nasiha ga
bayinsa;tsai da sallah da yawan nafilfilu;dimantar zikiri da tilawar
Alkur'ani; tausayawa marayu da tallafawa gajiyayyu;tunanin lahira da
gudun duniya;da sauransu,wadannan su ne ainihin tushen Sufanci. Kuma
wannan shi ne ra'ayin Sufaye, wadanda a koda yaushe suke da'awar cewa
iliminsu da tafarkinsu ba su da tushe sai jigon Musulunci.
Amma idan muka dubi abinda ke kunshe a cikin Sufanci da
abubuwan dake tattare da Sufaye, sai mu ga cewa Musulunci shi kadai
bai zama tushen Sufanci. Dalili kuwa shi ne,akwai abubuwa da dama
wadanda kusan dukkanin Sufaye sun yarda da su a matsayin wani bangare
na tafarkinsu,amma wadannan abubuwa ba su da tushe a cikin addinin
Musulunci. Ga misali,kusan dukkanin Sufaye sun yarda da batun ya ye
hijabi da dayantakar samuwa da wani abu da suke kira fana'i ko
wusuli,amma wadannan lamurra duka Musulunci bai san da su ba.
Hakanan,akwai wasu bangarori na rayuwar addini inda Sufaye suka
wuce makidi da rawa,su ka kai ga matsayin da akalla za'a iya kiran su
da masu bidi'a.Wadannan sun hada da wuce gaya wajen lamurran ibada da
tsananta abubuwa da Allah (S.W.A)ya saukaka na rayuwa. Akwai,ga
misali,Sufayen da suka haramta WA kansu aure tare da cewa aure Sunna
ce ta Annabi (S.A.W),wasu kuma suka haramta wa kansu cin nama tare da
cewa nama halal ne kuma yana daga mafi soyuwar abinci wurin
Annabi(S.A.W).
To idan haka halin Sufaye yake,ya za'a ce Sufanci ya samo asali
daga Musulunci tsintsa?(sai dai anan ma dole mu lura da bambanci
tsakanin Sufayen jiya da na yau.Sufayen yau,wasu bayan mata hudu ma
har sa-daka da kuyangi gare su.)
Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 11 Insha Allah.

Wednesday, 20 September 2017
*FITOWA TA 10
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA KUR'ANI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
Dangane da kalmomi da lafuzza da ma'anoni,babu wata sura a
cikin Alkur'ani kamar yadda muka san shi face yan Shi'a sun zo da
sabanin kalmomi ko ayoyi a cikinta.Za mu ba da yan misalai kadan.A
karshen SURATUL FATIHA suna karanta:IHDINAS SIRADAL MUSTAKIM.SIRADA
MAN AN'AMTA ALAIHIM,GAIRIL MAGDUBI ALAIHIM WA GAIRID DALIN.A farkon
SURATUL ASRI,suna karanta:WAL ASR INNAL INSANA LA FI KHUSR.WA INNAHU
FIHI ILA AKHIRID DAHR.ILLAL LAZINA AMANU WA AMILUS SALIHATI,WA'ATAMARU
BIT TAKWA,WA'ATAMARU BIS SABR.
SURATUL FILI kuma,watau ALAM TARA KAIFA,suna fara ta kamar haka:ALAM
YA'TIKA KAIFA FA'ALA RABBUKA BI ASHABIL FILI.
Wadannan yan misalai ne kawai muka kawo domin mai karatu ya
ganewa idanunsa.Wanda yake son ya ga wadannan sauye-sauye
filla-filla,to sai ya koma ga Littafin ALSHI'ATU WAL KUR'AN na Ihsan
Ilahi Zahir,Allah ya yi masa rahama,domin shi ya tsamo wadannan
canje-canje wadanda suka shafi surorin Alkur'ani guda 114 baki daya
daga littafan yan Shi'a kuma ya jera su,ya rattaba su,tare da
ruwayoyinsu.

*FITOWA TA 9
*Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
HASASHE NA BIYU
Wannan yana mayar da tushen Sufanci ga addinin
Nasara.Dalilin da masu wannan hasashe suka bayar a kan ra'ayinsu shi
ne kamanni masu yawa da ake samu tsakanin Sufaye da fada-fada na
Kirista.Ana samun kamannin ta bangaren dabi'un mabiya tafarkan biyu
kamar gudun duniya,hakuri da rayuwar talauci,haramtawa kai dadadan
abubuwan rayuwa,kauracewa aure,lazimtar tufafi iri daya maras
daraja,da sauransu.sai dai ya kamata a lura cewa wadannan sifofi na
Sufaye da fada-fadan jiya ne,ba Sufaye da fada-fada na yau ba yan
duniya wadanda suke yin addini don tara abin duniya ko cimma buri na
siyasa.
Yawancin masu wannan hasashe irin masu binciken nan ne da ake
kira da gabasawan-giri da almajiransu.Su gabasawan-giri,ko
Orientalists,Turawa ne da suke tafiya Gabas(kasashen Larabawa)su koyo
ilimin addinin Musulunci domin kawai su yi was Musulunci din zagon
kasa da kafar ungulu.Saboda ra'ayinsu na cewa an kwaikwayo Musulunci
daga Kiristanci,don haka kome aka ce ya danganci Musulunci sai su ce
daga addininsu ya samo asali.
Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 10 Insha Allah.

Tuesday, 19 September 2017
*FITOWA TA 9
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA KUR'ANI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
Ta fuskar adadin surori ma,akwai dan bambanci saboda akwai
wasu surori wadanda yan Shi'a suke kudure cewa an debe su daga cikin
Alkur'ani. Misali shi ne wata sura da suke kira SURATUL WILAYA wacce
suka ce wai a cikinta Allah ya yi umarni da nada Ali binu Abi Dalib a
matsayin Khalifa bayan rasuwar Annabi(S.A.W).Wannan sura ba mu san ta
ba,babu ita a cikin Alkur'aninmu,amma su yan Shi'a suna kudure cewa
wai Sahabbai ne suka debe ta don cin amana.a fadinsu,domin su hana Ali
binu Abi Dalib(r.a)hakkinsa na gadar Annabi,suka nada Abubakar a
makwafinsa.Wannan ita ce akidarsu.Wal iyazu billah!!

*FITOWA TA 8
*Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
HASASHE NA DAYA
Za mu fara da hasashen Falsafar Girkawa.Afladuniya Sabuwa
ita ce mazhabar falsafa wacce dadadden failasufin nan Bagirke mai suna
Sakkas ya kago ta.Shi Sakkas ya fara rayuwarsa a matsayin dan dako
kuma daga baya ya nemi ilimin falsafa har ya zama babban failasufi.Har
ya zuwa rasuwarsa,Sakkas bai bar wasu littafai ko rubuce rubuce ba a
kan bayanin mazhabarsa ta falsafa.sai bayan mutuwarsa ne,almajirinsa
Afladin,ya tattara maganganunsa da koyarwarsa da tunane-tunanensa ya
rubuce su,wanda wannan aiki shi ya tabbatar da wanzuwar mazhabar
tasa.Don haka ne kuma ake kiran mazhabar da sunan almajirin,watau
Afladuniya.
Babu shakka Musulmi sun fassara littafan Girkawa zuwa harshen
Larabci,haka nan kuma sunyi darasun falsafofinsu da
tunane-tunanensu,kuma hakan ya yi tasiri ga rayuwar Musulmi da
tunaninsu.Har wa yau kuma,babu shakka cewa mazhabar Afladuniya Sabuwa
ta yi tasiri ga ayyukan Musulmi na fagen tunani,musamman Sufaye,kamar
yadda za'a iya gani a rubuce rubucen yan Ikhwanus Safa,wata kungiyar
asiri ta Sufaye.To amma duk da haka masu bincike na ganin cewa rashin
adalci ne a dangana Sufanci ga wannan mazhaba ita kadai,ko kuma ace
Afladuniya Sabuwa ita ce tushen Sufanci. Dalili kuwa shi ne,Sufanci ya
dade da yaduwa a tsakanin Musulmi kafin su fassaro littafan Girkawa ko
su tasirantu da falsafarsu.
Sai dai babu mai musun cewa akwai falsafar Girkawa da
ra'ayoyinsu a cikin Sufanci, kamar yadda zamu gani a nan gaba yayin da
muka zo magana a kan matakan Sufanci.Ra'ayoyin Sufaye dangane da
sani(ilimi),fana'i,yaye hijabi,da sauransu,duka sun samo tushensu ne
daga falsafar Girkawa da sauran falsafofin wasu al'ummai,kamar mutanen
Sin,Indiya,Masar ta dori,da sauransu.
Saboda haka,ba mu iya cewa Afladuniya Sabuwa ita kadai ita ce
tushen Sufanci kamar yadda ba mu iya musun tasirinta a
cikinsa.Afladuniya na daga cikin shika-shikan Sufanci wadanda aka dora
ganinsu a kansu.
Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 9 Insha Allah.

Monday, 18 September 2017
*FITOWA TA 8
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA KUR'ANI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
Kur'anin yan Shi'a ya sha bamban da Alkur'anin Musulmi ta
fuskoki masu yawa.Mun riga mun gabatar da bayanin bambancinsu ta wajen
jimillar ayoyinsu,inda Kur'anin yan Shi'a yake da adadin ayoyi dubu
sha bakwai(17,000)dai-dai wa daida,a yayinda namu yake da ayoyi dubu
shida da dari biyu da talatin da shida(6,236)kacal.Ta fuskar tsawon
surori ma,littafan guda biyu sun sha bamban.Ga misali,ya zo a cikin
KITAB SULAIM BINU KAIS,mashahurin littafin nan na Shi'a wanda saboda
ingancinsaa wajensu suke masa lakabi da A.B.C. Din Shi'a, cewa wai
SURATUL AHAZAB wacce take da ayoyi 73 a kur'aninmu,su a nasu Kur'anin
adadin ayoyin BAKARA ne da ita,watau 286.SURATUN NUR kuwa,wacce take
da ayoyi 64,su a wajensu ayoyi 160 ke gareta.SURATUL HUJURATI
kuma,wacce a cikin Kur'anin da muka sani ayoyinta 18 ne kacal,su a
nasu Kur'anin ayoyinta 90 ne dai-dai was daida.[Duba KITAB SULAIM BINU
QAIS na Sulaim binu Qais Alhilali Alkufi,bugun Mu'assasatul
A'alami,Bairut,ba tarihi ,shafi na 122.]
Anan zamu dakata sai kuma fitowa ta 9 Insha Allah.

*FITOWA TA 7
*Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
BULLAR SUFANCI DA YADUWARSA
Malamai da masana tarihi sun hadu a kan cewa Sufanci ya bulla
duniyar Musulmi a cikin karni na biyu bayan Hijira,watau a cikin
shekara dari ta biyu bayan kaurar Manzon Allah (S.A.W).Hasali ma,masu
bincike sun kai ga samo asalin mutum na farko wanda aka fara kira da
lakabin Sufi a duniya.Wannan mutum shi ne Abu Hashim Alkufi
Assufi,wanda ya rasu a shekara ta 150 bayan Hijira. Wani abu da yake
karfafa wannan ra'ayi shi ne,duk manyan litattafan da aka rubuta a kan
Sufanci, ba wanda ya yi magana a kan abinda ya wuce wannan
tarihin,watau karni na biyu bayan Hijira.
Da yake mun ga zamanin da Sufanci ya bulla,to bari mu duba mu ga
shin wadanne abubuwa ne suka kawo bullar tasa,ko kuma a takaice,ina
Sufanci ya samo tushensa?Malamai sun yi hasashe da dama a kan asalin
Sufanci da tushensa.Akwai masu ganin cewa,Sufanci ya samo asali ne
daga addinin Musulunci tsintsa,watau daga Alkur'ani da sunnar
Annabi(S.A.W).Akwai kuma masu hasashen cewa Sufanci ya samo asalinsa
ne daga addinin Kirista ta hanyar cudanyar Musulmi da Kiristoci,bayan
Musulunci ya ci kasashensu da yaki.Masu hasashe na uku kuwa suna ganin
cewa Sufanci ya samo tushe ne daga wata falsafa ta Girkawa da ake kira
Afladuniya Sabuwa.
Yanzu bari mu duba wadannan ra'ayoyi guda uku tare da bayanin
malamai a kansu.
Anan zamu dakata sai kuma a fitowa ta 8 Insha Allah.

Saturday, 16 September 2017
LALLE ABUBAKAR MAI YAWAN DARAJOJI NE A GURIN ALLAH DA MANZONSA:
✍ Rubutawa: *Sheik Dr Ibrahim Jalo Jalingo (Hafizahullah)*
Sayyidina Abubakar Bin Abi Quhaafah Allah Ya kara masa yarda Mutum ne mai yawan darajoji a gurin Allah da manzonSa; ga ma wasu siffofi da darajoji har guda biyar da manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya siffanta shi da su:-
1. Shi Abubakar Siddiqi ne; watau mai martabar waliyyan Allah ta biyu ne bayan martabar farko ta Annabci; kamar yadda Allah Ya jeranta wadannan martabobi hudu na waliyyanSa a cikin Suratun Nisaa'i aya ta 69 inda ya ce:-
((ومن يطع الله والرسول فأولئك مع الذين انعم الله عليهم من النبيين والصديقين والشهداء والصالحين وحسن أولئك رفيقا)).
Ma'ana: ((Kuma wadannan da suka yi da'a ga Allah da ManzonSa, to, wadannan suna tare da wadanda Allah Ya yi ni'ima a kansu, daga Annabawa, da Siddiqai, da Shahidai, da Salihai. Kuma wadannan sun kyautatu ga zama abokan tafiya)).2. Shi Abubakar shi ne mutumin da Annabi ya fi son shi a cikin dukkan Mazaje.
3. Shi Abubakar mutum ne da Annabi ya ba da umurnin a yi koyi da shi.
4. Shi Abubakar mutum ne da Allah Ya 'yanta shi daga Wuta.
5. Shi Abubakar shi ne mutumin da yake shugabantar dukkan manya majiya karfi in banda Annabawa da Manzanni a cikin Aljannah.
Lalle banda wadannan darajoji biyar da muka ambata yanzu, akwai wasu darajojin daban.
Ga hujjar wadannan darajoji biyar na Babban Sahabi Abubakar da muka ambata daga ingantattun hadithan manzon Allah mai tsira da amincin Allah:-
(1). Bukhariy ya ruwaito Hadithi na 3675, da Abu Dawud Hadithi na 4653, da Tirmiziy Hadithi na 3697, da Nasaa'iy Hadithi na 8079, da Ahmad Hadithi na 12127, da Ibnu Hibban Hadithi na 6865, da Bazzar Hadithi na 7094, da Dabaraaniy Hadithi na 144, da Abu Ya'alaa Hadithi na 2910, da Abdur Razzaq Hadithi na 20401 daga Sahabi Uthman Bin Affan, da Sahabi Anas Bin Malik Allah Ya kara musu yarda sun ce:-
((ان النبي صلى الله عليه وسلم صعد احدا وأبو بكر وعمر وعثمان فرجف بهم، فقال: اثبت احد فانما عليك نبي وصديق وشهيدان)).
Ma'ana: ((Lalle Annabi mai tsira da amincin Allah ya hau (dutsen) Uhudu tare da Abubakar da Umar da Uthman, sai ya (dutsen) ya girgiza, sai ya ce: Uhudu ka nitsu ba wasu ba ne a kanka in banda wani Annabi, da wani Siddiqi, da wasu Shahidai biyu)).(2). Bukhariy ya ruwaito Hadithi na 4379, ma Muslim Hadithi na 2384, da Tirmiziy Hadithi na 3885, da Nasaa'iy Hadithi na 8052, da Ibnu Majah Hadithi ne 101, da Ahmad Hadithi na 17844, da Hakim Hadithi na 6740, da Ibnu Hibban Hadithi na 6885, da Dabaraaniy Hadithi na 18644, da Baihaqiy Hadithi na 12879 daga Sahabi Anas Bin Malik, da Sahabi Amr Bin A'as Allah Ya kara musu yarda suka ce:-
((ان النبي صلى الله عليه وسلم سيل اَي الناس أحب إليك؟ قال: عايشة. فقيل له: من الرجال؟ قال: ابوها)).
Ma'ana: ((Lalle an tambayi Annabi mai tsira da amincin Allah: wanene ne daga cikin mutane ya fi soyuwa a gare ka? Sai ya ce: A'isha. Sai aka ce da shi: daga cikin Maza fa? Sai ya ce: Mahaifinta)).(3). Tirmiziy ya ruwaito Hadithi na 3662, da Ahmad Hadithi na 23293, da Hakim Hadithi na 4451, da Dabaraaniy Hadithi na 8344, da Bazzar Hadithi na 2827, da Baihaqiy Hadithi na 10348 daga Sahabi Abdullahi Bin Mas'ud, da Sahabi Huzaifah Allah Ya kara musu yarda sun ce:-
((قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: اقتدوا باللذين من بعدي ابي بكر وعمر)).
Ma'ana: ((Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: Ku yi koyi da Wadannan biyun a bayana: Abubakar da Umar)).(4). Tirmiziy ya ruwaito Hadithi na 3679, da Hakim Hadithi na 3557, da Ibnu Hibban Hadithi na 6864 daga Sahabiya uwar Muminai A'isha, da Sahabi Az-Zubair Bin Awwam Allah Ya kara musu yarda suka ce:-
((ان رسول الله صلى الله عليه وسلم قال لابي بكر: انت عتيق الله من النار)).
Ma'ana: ((Lalle manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce wa Abubakar: Kai ne 'yantaccen Allah daga Wuta)).(5). Tirmiziy ya ruwaito Hadithi na 3665, da Ibnu Majah Hadithi na 95, da Ahmad Hadithi na 603, da Ibnu Hibban Hadithi na 6904, da Bazzar Hadithi na 490, da Dabaraaniy Hadithi na 17717, da Abu Ya'alaa Hadithi na 624 daga Sahabi Aliyyu Bin Dalib, da Sahabi Anas Bin Malik, da Sahabi Abdullahi Bin Abbas Allah Ya kara musu yarda sun ce:-
((ان النبي صلى الله عليه وسلم قال: ابو بكر وعمر سيدا كهول اهل الجنة من الاولين والاخرين الا النبيين والمرسلين)).
Ma'ana: ((Lalle Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: Abubakar da Umar shugabanni ne na manya majiya karfi na Aljannah tun na farkonsu har na karshensu amma banda Annabawa da Manzanni)).Lalle wannan shi ne matsayin Sahabi Abubakar a idanun Shari'ar Musulunci. Kuma lalle 'yan bidi'ar da suka maida ginshikin addininsu shi ne zagin shi da la'antar shi sun tabe. Allah Ya taimake mu Ya raba mu da sharrin bidi'ah. Ameen.
MUHADARORI/WA'AZI DARI (100) NA SHEIKH KABIR GOMBE

Wadannan Kadan Ne Daga Cikin Wa'azuzzuka Da Babban Sakataren 'Kungiyar Jama'atu-Izalatil-Bid'ah- Wa-Ikamatis-Sunnah Na Kasa Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe Hafizahullah Ya Gabatar, Wadanda Cibiyar Yada Sunnah Ta DARULFIKR Ta Dora, Kuma Admins Na Dandalin Masoya Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe Hafizahullah #ISupportSheikKabirGombe Suka Tattara Domin Ku Sami Saukin Saukewa.
000 Yi Like Din Shafin Mu A Facebook
http://facebook.com/ISupportSheikKabirGombe
001 Kula Da Sallah
http://darulfikr.com/s/21704
002 Kyautatawa a Musulunci
http://darulfikr.com/s/22411
003 Matasa Mu Tashi Mu Nema Ilimi
http://darulfikr.com/s/22414
004 Matan Aljannah A Duniya
http://darulfikr.com/s/22415
005 Tausayin Yara Mata akan Iyayensu
http://darulfikr.com/s/22523
006 Ta'aziyan Alhaji Ahmadu Chanchangi
http://darulfikr.com/s/22522
007 Kabari Aya ne A Garemu
http://darulfikr.com/s/22520
008 BANBAMCI TSAKANIN GWAURO DA MAI AURE
http://darulfikr.com/s/7431
009 Duniya Budurwar Wawa
http://darulfikr.com/s/10159
010 MATASA KASHIN BAYAN RAYA SUNNAH
http://darulfikr.com/s/21151
011 Muhimmancin Gudunmawa a Musulunci
http://darulfikr.com/s/10285
012 Rashin godiyar Allan mu game da BUHARIYYAH
http://darulfikr.com/s/8869
013 Saki kowa ka kama Allah
http://darulfikr.com/s/20022
014 Son Zuciya ubangiji ne da wasu ke bautawa
http://darulfikr.com/s/10113
015 Sunnah in Bakayi Bani Guri
http://darulfikr.com/s/9209
016 Waye Masoyin Annabi
http://darulfikr.com/s/10392
017 Ayatullahi Buratai
http://darulfikr.com/s/4106
018 Garin Neman Gira An Rasa Ido
http://darulfikr.com/s/2912
018 Rayuwa Adam Acikin Duniya
http://darulfikr.com/s/5093
019 Wasika Zuwaga Mawadata
http://darulfikr.com/s/3027
020 Ladubban Tarewa A Sabon Gida
http://darulfikr.com/s/3016
021 Tonon Silili Da Tufin Allah Tsine
http://darulfikr.com/s/4144
022 Anyi walkiya mun gansu
http://darulfikr.com/s/1309
023 DAN KASA NAGARI
http://darulfikr.com/s/18314
024 IKLar Shaye-Shaye
http://darulfikr.com/s/927
025 Riba da illolinta
http://darulfikr.com/s/929
026 Gyara kayan ba zai zamo sauke mu raba ba
027 http://darulfikr.com/s/3586
028 Ihidinas Siradal Musataeem
http://darulfikr.com/s/5413
029 BIDI'AR MAULIDI
030 http://darulfikr.com/s/935
031 Kowanne tsintsu kukan gidan su yake
http://darulfikr.com/s/5252
032 Majlisin Malamai
http://darulfikr.com/s/4401
033 Makircin Shi'a
http://darulfikr.com/s/2432
034 Nigeria ta fara hayaki
http://darulfikr.com/s/942
035
Ribar kafa
http://darulfikr.com/s/9092
036 ILLAR ZINA
http://darulfikr.com/s/939
037 Shirin Fatawa na Kada Fm
http://darulfikr.com/s/6854
038 ILLOLIN JAHILCI
http://darulfikr.com/s/944
039 SADA ZUMINCI
http://darulfikr.com/s/946
040 MADINAR GAUSI
http://darulfikr.com/s/949
041 MALAMN BIDIA DILALA SHARI
http://darulfikr.com/s/945
042 MATAN ANNABI SAW
http://darulfikr.com/s/947
043 MATAN ANNABI SAW 2
044 http://darulfikr.com/s/948
045 MUMMUNAR CIKAWA
http://darulfikr.com/s/950
046 SUNNA SAK BIDI'A SAM
http://darulfikr.com/s/952
047
HUKUNCHIN KALLO
http://darulfikr.com/s/951
048 KO KINKI KO KINSO
http://darulfikr.com/s/953
049 WEYE MAI SALLAH
http://darulfikr.com/s/955
050 YAN SHI'A
http://darulfikr.com/s/956
051 WA'AZIN KANGIWA
http://darulfikr.com/s/18197
052 WA'AZIN GARIN LARABAR ABASAWA
http://darulfikr.com/s/17975
053 WA'AZIN MATA NA DORAYI
http://darulfikr.com/s/17976
054 Wa'azin Mata Sumaila
http://darulfikr.com/s/17972
055 Wa'azin Lagos 01
http://darulfikr.com/s/9112
056 Wa'azin Lagos
http://darulfikr.com/s/7434
Waazin zamfarah
ttp://darulfikr.com/s/8764
057 Wa'azin Miya
http://darulfikr.com/s/5519
058 Wa'azin Owode Ogun
http://darulfikr.com/s/19055
059 Wa'azin sokoto 1
http://darulfikr.com/s/930
060 Wa'zin Sokoto 2
http://darulfikr.com/s/931
061 Wa'zin Sokoto 3
http://darulfikr.com/s/933
062 Wa'azin Mata Zamfarah
ttp://darulfikr.com/s/932
063 Wa'azin Suleja
http://darulfikr.com/s/934
064 Wa'azin Kankiya
http://darulfikr.com/s/3393
065 Wa'azin Yantumaki
http://darulfikr.com/s/937
066 Wa'azin Billiri
http://darulfikr.com/s/5258
067 Wa'azin Bolari
http://darulfikr.com/s/5252
068 Wa'azin Yola
http://darulfikr.com/s/957
069 Wa'azin Jalingo
http://darulfikr.com/s/20862
070 Wa'azin,Accra Ghana
http://darulfikr.com/s/9092
071 Wa'azin Niger
http://darulfikr.com/s/940
072 Wa'azin Illela
http://darulfikr.com/s/943
073 Wa'azin Pandogari 1
http://darulfikr.com/s/954
074 Wa'azin Pandogari 2
http://darulfikr.com/s/936
075 Wa'azin Sumaila Kano
http://darulfikr.com/s/17973
076 Wa'azin Agege Lagos
http://darulfikr.com/s/18503
077 Wa'azin Jahar Kano
http://darulfikr.com/s/13102
078 Wa'azin Bauchi
http://darulfikr.com/s/4203
079 Wa'azin Jihar Kano 5
http://darulfikr.com/s/1369
080 Wa'azin Liman Katagun Bauchi
http://darulfikr.com/s/4204
081 Waazin Mata Taraba
http://darulfikr.com/s/19931
082 Wa'azin Maza Ogere
http://darulfikr.com/s/19059
083 Wa'azin Mata Owode Ogun
http://darulfikr.com/s/19058
084 Wa'azin Maza Owode Ogun
http://darulfikr.com/s/19057
085 Wa'azin Mata Ogere
http://darulfikr.com/s/19074
086 Wa'azin Shagamu Ogun
http://darulfikr.com/s/19060
087 Alaba Rago Lagos
http://darulfikr.com/s/19075
088 Wa'azin Zaria
https://kiwi6.com/file/494p6nu72v
089 Wa'azin Yola 2
https://kiwi6.com/file/mritel0tu0
090 Wa'azin Kumo
https://kiwi6.com/file/xwu3stijrf
091 Wa'azin Lagos 2014
https://kiwi6.com/file/zo52lzbay2
092 Wa'azi Funtua
https://kiwi6.com/file/fh6j8e6e0v
092 Wa'azin Gamahttps://kiwi6.com/file/0ptyt0vi2m
093 Wa'azin Suleja 2
https://kiwi6.com/file/st2bmi55wv
094 Wa'azin Tsafe
https://kiwi6.com/file/1ygupz01fh
095 Wa'azin Dan Sadau
https://kiwi6.com/file/kfnr1bkenv
096 Wa'azin Ikara
https://kiwi6.com/file/71ngomy2zu
097 Wa'azin Madobi
https://kiwi6.com/file/56555ivywk
098 Wa'azin Rano
https://kiwi6.com/file/kmyjhjzx15
099 Wa'azin Jos
https://kiwi6.com/file/r8ghnl8jvu
100 Wa'azin Kaduna City
https://kiwi6.com/file/lhejc4i4nq
Kuci Gaba Da Kasancewa Damu Domin Samun Links Da Zaku Sauke Karatukan Malam Da Sauran Malaman Sunnah.
dannan Link Din Dake Kasa Kayi Like Na Shafin Mu.
www.facebook.com/ISupportSheikKabirGombe

ZAGIN SAHABBAI HARAMUN NE:
ZAGIN SAHABBAI HARAMUN NE:
1. Yana daga cikin manyan alamu na bacewar manyan kungiyoyin 'Yan bidi'ah; Khawaarijawansu, da Shi'awansu, da Naasibawansu: zagin sahabban Manzon Allah mai tsira da amincin Allah.
2. Lalle zagin babban Sahabi Aliyyu Bin Abi Dalib Allah Ya kara masa yarda, da zagin sauran sahabban Annabi mai tsira da aminci Allah manyansu da kananansu laifi ne babba, a gaskiya ma ba ma wai zagin Sahabbai ba Aliyyu, ko Abubakar, ko Umar, ko Uthman ko wasunsu ba ne laifi kawai, a'a zagin ko wane Musulmi ma laifi ne babba a bisa nassin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah; Imamul Bukhariy ya ruwaito Hadithi na 48, da Muslim Hadithi na 64, da Tirmiziy Hadithi na 1983, da Nasaa'iy Hadithi na 4108, da Ibnu Majah Hadithi na 69, da Ahmad Hadithi na 3647, da Ibnu Hibban Hadithi na 5939, da Bazzar Hadithi na 1172, da Dabaraaniy Hadithi na 9958 daga Sahabi Abdullahi Bin Mas'ud Allah Ya kara masa yarda cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce:-
Ku 'yan bidi'ah Shi'awanku, da Khawarijawanku, da Nasibawanku ku ne kuke zagin Sahabbai har yau har gobe, ku ne kuma a cikin aqidarku da za ce: Sahabban nan za su dawo duniya a yanzu to kuwa da za ku yake su saboda wannan shi ne ginshikin addininku.
3. Amma su Ahlus Sunnah babu Sahabin da suke zagi ballantana ma su yake shi da za a kaddara cewa zai sake dawowa duniya a yanzu. Sannan su Ahlus Sunnah dukkan abin da ya faru da su Sahabban a zaminsu na zage-zagen juna, ko na yake yaken juna, suna bin abin da Allah Madaukakin Sarki Ya hukunta ne game da yin ta'amuli da hakan; watau na cewa wannan abin da ya faru a tsakaninsu bai fidda su daga Musulunci ba bai kuma fidda su daga Imani ba, a'a suna nan Musulmi Muminai; kamar dai yadda Shi Allah Madaukakin Sarki Ya ce ne cikin Suratul Hujurat aya ta 9-10:-
Ga shi dai a nan kuna gani karara cikin wadannan ayoyi biyun inda Allah Madaukakin Sarki Ya kira bangarori biyun da cewa su 'yan'uwan juna ne, Ya kuma siffanta su da cewa su Muminai ne; duk kuwa da cewa suna yakar junansu, suna kashe junansu suna ta zagin junansu. Haka Allah Ya ga dama Ya tabbatar da wannan hukuncin game da Sahabban Annabi mai tsira da amincin Allah; su kuma Ahlus Sunnah sun yarda da dukkan abin da Allah Madaukakin Sarki Ya ce a cikin Alkur'ani mai girma; saboda haka ba sa kore wa Sahabban Musulunci da Imani.
4. Haka nan su Ahlus Sunnah ba sa zagin kowa daga cikin wadannan Sahabban saboda Annabi mai tsira da amincin Allah ya haramta zagin su; Bukhariy ya ruwaito Hadithi na 3673, da Muslim Hadithi na 2540, da Abu Dawud Hadithi na 4660, da Tirmiziy Hadithi na 3861, da Nasaa'iy Hadithi na 8250, da Ibnu Majah Hadithi na 161, da Ahmad Hadithi na 11094, da Ibnu Hibban Hadithi na 7353, da Dabraaniy cikin Kabeer Hadithi na 303 daga Sahabi Abu Sa'id Al-Khudriy, da Sahabi Abu Hurairah Allah Ya Kara musu yarda cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce:-
5. Tabbas Ahlus Sunnah suna gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya hore musu mika wuya ga dukkan abin da Allah da MsnzonSa suka ce musu, ko suka umurce su da yi ko da bi. Allah Ya taimake mu. Ameen.
1. Yana daga cikin manyan alamu na bacewar manyan kungiyoyin 'Yan bidi'ah; Khawaarijawansu, da Shi'awansu, da Naasibawansu: zagin sahabban Manzon Allah mai tsira da amincin Allah.
2. Lalle zagin babban Sahabi Aliyyu Bin Abi Dalib Allah Ya kara masa yarda, da zagin sauran sahabban Annabi mai tsira da aminci Allah manyansu da kananansu laifi ne babba, a gaskiya ma ba ma wai zagin Sahabbai ba Aliyyu, ko Abubakar, ko Umar, ko Uthman ko wasunsu ba ne laifi kawai, a'a zagin ko wane Musulmi ma laifi ne babba a bisa nassin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah; Imamul Bukhariy ya ruwaito Hadithi na 48, da Muslim Hadithi na 64, da Tirmiziy Hadithi na 1983, da Nasaa'iy Hadithi na 4108, da Ibnu Majah Hadithi na 69, da Ahmad Hadithi na 3647, da Ibnu Hibban Hadithi na 5939, da Bazzar Hadithi na 1172, da Dabaraaniy Hadithi na 9958 daga Sahabi Abdullahi Bin Mas'ud Allah Ya kara masa yarda cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce:-
(( ﺳﺒﺎﺏ ﺍﻟﻤﺴﻠﻢ ﻓﺴﻮﻕ ﻭﻗﺘﺎﻟﻪ ﻛﻔﺮ )).
Ma'ana: ((Zagin Musulmi fasikanci ne yakar shi kuma kafirci ne)).Ku 'yan bidi'ah Shi'awanku, da Khawarijawanku, da Nasibawanku ku ne kuke zagin Sahabbai har yau har gobe, ku ne kuma a cikin aqidarku da za ce: Sahabban nan za su dawo duniya a yanzu to kuwa da za ku yake su saboda wannan shi ne ginshikin addininku.
3. Amma su Ahlus Sunnah babu Sahabin da suke zagi ballantana ma su yake shi da za a kaddara cewa zai sake dawowa duniya a yanzu. Sannan su Ahlus Sunnah dukkan abin da ya faru da su Sahabban a zaminsu na zage-zagen juna, ko na yake yaken juna, suna bin abin da Allah Madaukakin Sarki Ya hukunta ne game da yin ta'amuli da hakan; watau na cewa wannan abin da ya faru a tsakaninsu bai fidda su daga Musulunci ba bai kuma fidda su daga Imani ba, a'a suna nan Musulmi Muminai; kamar dai yadda Shi Allah Madaukakin Sarki Ya ce ne cikin Suratul Hujurat aya ta 9-10:-
(( ﻭﺍﻥ ﻃﺎﺋﻔﺘﺎﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﺍﻗﺘﺘﻠﻮﺍ ﻓﺄﺻﻠﺤﻮﺍ ﺑﻴﻨﻬﻤﺎ ﻓﺎﻥ ﺑﻐﺖ ﺍﺣﺪﺍﻫﻤﺎ ﻋﻠﻰ ﺍﻻﺧﺮﻯ ﻓﻘﺎﺗﻠﻮﺍ ﺍﻟﺘﻲ ﺗﺒﻐﻲ ﺣﺘﻰ ﺗﻔﻲﺀ ﺍﻟﻰ ﺍﻣﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﺎﻥ ﻓﺎﺀﺕ ﻓﺄﺻﻠﺤﻮﺍ ﺑﻴﻨﻬﻤﺎ ﺑﺎﻟﻌﺪﻝ ﻭﺃﻗﺴﻄﻮﺍ ﺍﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﺤﺐ ﺍﻟﻤﻘﺴﻄﻴﻦ . ﺇﻧﻤﺎ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻮﻥ ﺍﺧﻮﺓ ﻓﺄﺻﻠﺤﻮﺍ ﺑﻴﻦ ﺃﺧﻮﻳﻜﻢ ﻭﺍﺗﻘﻮﺍ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻌﻠﻜﻢ ﺗﺮﺣﻤﻮﻥ )).
Ma'ana: ((Idan aka samu wasu kungiyoyi biyu daga Muminai suka yaki juna to ku yi sulhu a tsakaninsu idan dayar ta yi zalunci a kan dayar to ku yaki wacce take zaluncin har sai ta dawo zuwa ga umurnin Allah, idan ta dawo sai ku yi sulhu a tsakaninsu cikin adalci, ku yi adalci lalle Allah Yana son masu adalci. Abin sani shi ne Muminai 'yan'uwan juna ne, saboda haka ku yi sulhu a tsakanin 'yan'uwanku, ku ji tsoron Allah kila a muku rahama)).Ga shi dai a nan kuna gani karara cikin wadannan ayoyi biyun inda Allah Madaukakin Sarki Ya kira bangarori biyun da cewa su 'yan'uwan juna ne, Ya kuma siffanta su da cewa su Muminai ne; duk kuwa da cewa suna yakar junansu, suna kashe junansu suna ta zagin junansu. Haka Allah Ya ga dama Ya tabbatar da wannan hukuncin game da Sahabban Annabi mai tsira da amincin Allah; su kuma Ahlus Sunnah sun yarda da dukkan abin da Allah Madaukakin Sarki Ya ce a cikin Alkur'ani mai girma; saboda haka ba sa kore wa Sahabban Musulunci da Imani.
4. Haka nan su Ahlus Sunnah ba sa zagin kowa daga cikin wadannan Sahabban saboda Annabi mai tsira da amincin Allah ya haramta zagin su; Bukhariy ya ruwaito Hadithi na 3673, da Muslim Hadithi na 2540, da Abu Dawud Hadithi na 4660, da Tirmiziy Hadithi na 3861, da Nasaa'iy Hadithi na 8250, da Ibnu Majah Hadithi na 161, da Ahmad Hadithi na 11094, da Ibnu Hibban Hadithi na 7353, da Dabraaniy cikin Kabeer Hadithi na 303 daga Sahabi Abu Sa'id Al-Khudriy, da Sahabi Abu Hurairah Allah Ya Kara musu yarda cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce:-
(( ﻻ ﺗﺴﺒﻮﺍ ﺃﺻﺤﺎﺑﻲ ﻓَﻠَﻮ ﺍﻥ ﺍﺣﺪﻛﻢ ﺃﻧﻔﻖ ﻣﺜﻞ ﺍﺣﺪ ﺫﻫﺒﺎ ﻣﺎ ﺑﻠﻎ ﻣﺪ ﺍﺣﺪﻫﻢ ﻭﻻ ﻧﺼﻴﻔﻪ )).
Ma'ana: ((Kada ku zagi sahabbaina lalle da dayanku zai ba da sadakar zinarin da ya kai dutsen Uhudu nauyi to da ladan da zai samu ba zai kai ladan da dayansu zai samu ba idan ya yi sadakar mudu guda ko ma rabin mudun da zai ciyar)). Haka nan Dabraaniy ya ruwaito cikin Kabeer Hadithi na 12,541, da Bazzar cikin Musnad Hadithi na 5753 daga Sahabi Ibnu Abbas da Sahabi Ibnu Umar Allah Ya kara musu yarda cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce:-(( ﻣﻦ ﺳﺐ ﺃﺻﺤﺎﺑﻲ ﻓﻌﻠﻴﻪ ﻟﻌﻨﺔ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺍﻟﻤﻼﺋﻜﺔ ﻭﺍﻟﻨَّﺎﺱ ﺍﺟﻤﻌﻴﻦ )).
Ma'ana: ((Duk wanda ya zagi Sahabbaina tsinuwar Allah da Mala'iku da Mutane gaba daya ta tabbata a kan shi)).5. Tabbas Ahlus Sunnah suna gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya hore musu mika wuya ga dukkan abin da Allah da MsnzonSa suka ce musu, ko suka umurce su da yi ko da bi. Allah Ya taimake mu. Ameen.
Friday, 15 September 2017
Ƙungiyar Izala tayi ƙira ga gwamnatin tarayya, da ta gaggauta ɗaukan mataki akan ƴan ta'addan Ƙabilar Igbo (IPOB)

......Kazalika Shugaban Izalar yayi ƙira ga Al'ummar musulmi su saka Ƴan yankin Rohingya dake kasar Myanmar cikin muhimman addu'oin kariyar Allah a duk inda suke.
Daga: Ibrahim Baba Suleiman
Shugaban Ƙungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'ah wa iƙamatis-Sunnah ta tarayyar Naijeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau, yayi ƙira da babbar murya akan gwamnatin tarayya ta ɗauki mataki na daƙile ƙisan gilla da Inyamurai ƴan a waren Ƙasar Biyafara suke yiwa Hausawa a garin Aba da wasu garuruwan inyamurai a kudu maso yammacin Naijeriya.
Shugaban yace zura ido ƴan ta'addan suna ɗauƙar doka a hannunsu bazai haifar da ɗa mai ido ba, lura da yadda Ƴan Ƙabilar Hausawa a jos suka fara ɗaukan doka akan wasu inyamurai waɗanda basuji ba basu gani ba a garin jos.
Sheikh Lau yayi ƙira da a tura jami'an tsaro su daƙile wannan ta'addancin da ƴan awaren suke yiwa Hausawa, kuma su zaƙulo waɗanda suka kitsa wannan rikici domin a hukunta su kamar yadda dokar ƙasa ta tanada, domin babu wanda yafi ƙarfin gwamnati" Inji Sheikh Bala Lau".
Shehin Malamin yayi ƙira ga matasan Arewa da suyi haƙuri kada su ɗauki doka a hannun su, saboda tabbacin cewa wannan gwamnati mai adalci bara ta zurawa ƴan ta'adda ido suna abun da suka ga dama a ƙasa ba.
A Ƙarshe Sheikh Bala Lau ƴa ƙira ga Limaman juma'a da Malamai masu karantarwa a masallatai da sauran Ɗaiɗaikun Jama'a da su sanya ƴan uwa Musulman yankin Rohingya na kasar Myanmar Cikin addu'oi na musamman, Kan kisan ƙare dangi daga maguzawa masu bin addinin Buddha suke musu.
A yanzu haka dai akwai 'yan gudun hijira kimanin 400,000 da ke rakube a Bangladesh.
Sheik Lau yayi addu'ar Allah ya zaunar da Al'ummar musulmi lafiya a duk inda suke a faɗin Duniya, ya zaunar ƙasar mu lafiya, ya mana maganin waɗanda suke neman wargajewar ƙasar Amin.

Thursday, 14 September 2017
SHEKARU 25 DA RASUWAR SHEIK ABUBAKAR GUMI

TAKAITACCEN TARIHINSA
An haifi Shaikh Abubakar Mahmud Gumi ne a cikin garin Gumi dake jihar Sokoto, a shekara ta 1340 bayan Hijira dai dai da shekarar Miladiyya 1922.
Malam ya tashi ne cikin kyakkyawar tarbiyya da natsuwa da tsafta da neman Ilimi karkashin kulawar mahaifin sa (Alkalin Gumi a wancan zamanin).
Haka kuma marigayi Sheik Gumi ya yi karance-karance na zaure a majalisi daban daban na Malaman da suka shahara a kasar Hausa a wancan lokaci, tare da karatu na nizamiyya daga nan kasar har kasar Sudan da kasar Saudi Arabiya.
Shaikh Abubakar Gumi mutum ne mai kokarin binciken Al-kur'ani da Sunna kan hukunce hukuncen Shari'a, tun daga abin da ya shafi Tauhidi, Hadisi, Fikhu da luggar Larabci, wanda karantarwar da ya yi ta tabbatar da haka.
Malam ya yi rubuce-rubuce masu yawa, kadan daga cikin su akwai:- *Al Akeedatus Saheehah bi Muwaafakatish Shari'ah
*Tarjamar Ma'a'nonin Al-ƙur'ani Mai Girma.
Tafsirin Al-kur'ani:
*Raddul Azhaan ilaa Ma'aanil Kur'an.
*Tarjamar littafin Hadisin "Arba'uunan Nawawiy"
Littafi mai suna *Manufata" ko (Where I Stand).
Wannan littafi ya na da matukar amfani ga sanin tarin siyasar kasar nan da ta shafi Addini da Mulki da sauransu.
Sheik Gumi ya rasu ne a ranar 11 ga watan Satumba, 1992.
Marigayi Sheikh Gumi baya zagi ko habaici ga wani, hasalima in ka jefi shi da baƙar magana, shi sai ya jefo maka fara tas.
Allah ya jikan Malam, ya gafarta masa da sauran Musulmai muminai Amin.

Sunday, 10 September 2017
Hudubar Jum'ah daga Haramin Makka mai Albarka 17/12/1438H
Hudubar jum'ah daga Haramin Makka mai Albarka
Liman: Sheikh Khalid Al-Ghamidi
Mai Fassara: Dr. Mansur Sokoto
Rana: 17/12/1438H
Maudhu'i: Mika Wuya ga Allah
Liman ya yi doguwar gabatarwa mai cike da hikima dauke da godiyar Allah a kan shar'anta aikin Hajji da ya yi don amfani iri iri da musulmi suke samu a ciki.
Limamin ya kira Alhazai su gode ma da ya zabo su daga cikin al'ummar musulmin duniya don su yi wannan ibada mai girma
Ya zayyano darussa muhimmai da ya kamata Alhaji ya tafi da su gida bayan kammala wannan aiki.
Daga cikin wadannan darussa liman ya yi dogon sharhi a kan maganar Tauhidi da mika wuya ga Allah da Manzonsa. Ya ce duk ayyukan Hajji da'a ne da biyayya ga umurnin Allah da aikin Manzonsa.
Limamin ya bayyana darajojin Annabi Ibrahim (AS) wanda duk sawunsa ne ake bi ga aikin Hajji. Ya ce Annabi Ibrahim shi ne wanda ya kai matuka wajen bin umurnin Allah shi da iyalansa; matarsa Hajar da dansa Ibrahim. Yau ga shi duk ayyukansu ne muke kwaikwaya a cikin aikin Hajji shekara bayan shekara.
Wajibi ne mu koma ga Allah muna masu amfani da wadannan darussa da muka koya a cikin wannan ibada mai girma.
A cikin huduba ta biyu ma limamin kara fadada magana ya yi game da zancen mika wuya ga Allah da kakkabe aikin shaidan da shubuha da son zuciya. Idan kana mumini ba ya dacewa ka gitta ma lamarin Allah da son zuciya ko ka yi kari cikin addinin Allah da bidi'a ko ka yi shakka a cikin nassoshin addini wanda zai kai ga ture su ko kuma yi tawilin su.
Daga karshe liman ya yi maganar matattun zukata masu kin maganar Allah da zukata masu rashin lafiya wadanda suke guje ma karantarwar gaskiya da kin aikata ta.
Sannan ya rufe da Hadisin Huzaifa wanda ya yi maganar fitinu kuma ya ba da mafita.
Liman ya yi addu'oi masu yawa masu albarka musamman ga Alhazai da wadanda suka yi masu hidima da musulmin da ke cikin tashin hankula a Arakan da sauran wurare.
Allah ya amsa.

Subscribe to:
Comments (Atom)