Wednesday, 20 September 2017

*FITOWA TA 9
*Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com

HASASHE NA BIYU
Wannan yana mayar da tushen Sufanci ga addinin
Nasara.Dalilin da masu wannan hasashe suka bayar a kan ra'ayinsu shi
ne kamanni masu yawa da ake samu tsakanin Sufaye da fada-fada na
Kirista.Ana samun kamannin ta bangaren dabi'un mabiya tafarkan biyu
kamar gudun duniya,hakuri da rayuwar talauci,haramtawa kai dadadan
abubuwan rayuwa,kauracewa aure,lazimtar tufafi iri daya maras
daraja,da sauransu.sai dai ya kamata a lura cewa wadannan sifofi na
Sufaye da fada-fadan jiya ne,ba Sufaye da fada-fada na yau ba yan
duniya wadanda suke yin addini don tara abin duniya ko cimma buri na
siyasa.
Yawancin masu wannan hasashe irin masu binciken nan ne da ake
kira da gabasawan-giri da almajiransu.Su gabasawan-giri,ko
Orientalists,Turawa ne da suke tafiya Gabas(kasashen Larabawa)su koyo
ilimin addinin Musulunci domin kawai su yi was Musulunci din zagon
kasa da kafar ungulu.Saboda ra'ayinsu na cewa an kwaikwayo Musulunci
daga Kiristanci,don haka kome aka ce ya danganci Musulunci sai su ce
daga addininsu ya samo asali.

Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 10 Insha Allah.

Abu Aisha Journalist
Jibwis Social Media Katsina

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve