*FITOWA TA 10
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA KUR'ANI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
Dangane da kalmomi da lafuzza da ma'anoni,babu wata sura a
cikin Alkur'ani kamar yadda muka san shi face yan Shi'a sun zo da
sabanin kalmomi ko ayoyi a cikinta.Za mu ba da yan misalai kadan.A
karshen SURATUL FATIHA suna karanta:IHDINAS SIRADAL MUSTAKIM.SIRADA
MAN AN'AMTA ALAIHIM,GAIRIL MAGDUBI ALAIHIM WA GAIRID DALIN.A farkon
SURATUL ASRI,suna karanta:WAL ASR INNAL INSANA LA FI KHUSR.WA INNAHU
FIHI ILA AKHIRID DAHR.ILLAL LAZINA AMANU WA AMILUS SALIHATI,WA'ATAMARU
BIT TAKWA,WA'ATAMARU BIS SABR.
SURATUL FILI kuma,watau ALAM TARA KAIFA,suna fara ta kamar haka:ALAM
YA'TIKA KAIFA FA'ALA RABBUKA BI ASHABIL FILI.
Wadannan yan misalai ne kawai muka kawo domin mai karatu ya
ganewa idanunsa.Wanda yake son ya ga wadannan sauye-sauye
filla-filla,to sai ya koma ga Littafin ALSHI'ATU WAL KUR'AN na Ihsan
Ilahi Zahir,Allah ya yi masa rahama,domin shi ya tsamo wadannan
canje-canje wadanda suka shafi surorin Alkur'ani guda 114 baki daya
daga littafan yan Shi'a kuma ya jera su,ya rattaba su,tare da
ruwayoyinsu.
Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 11 Insha Allah.
Abu Aisha Journalist
Jibwis Social Media Katsina
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve