Thursday, 21 September 2017

*FITOWA TA 10
*Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com

HASASHE NA UKU
hasashe na uku yana mayar da Sufanci ya zuwa ga tushen
Musulunci tsintsa,watau zuwa ga Alkur'ani da Sunnar Annabi(S.A.W).Ga
masu wannan ra'ayi,ayoyin Alkur'ani da hadisan Annabi(S.A.W) da suke
umarni da tsoron Allah, tuba,ikhlasi ga Allah da nasiha ga
bayinsa;tsai da sallah da yawan nafilfilu;dimantar zikiri da tilawar
Alkur'ani; tausayawa marayu da tallafawa gajiyayyu;tunanin lahira da
gudun duniya;da sauransu,wadannan su ne ainihin tushen Sufanci. Kuma
wannan shi ne ra'ayin Sufaye, wadanda a koda yaushe suke da'awar cewa
iliminsu da tafarkinsu ba su da tushe sai jigon Musulunci.
Amma idan muka dubi abinda ke kunshe a cikin Sufanci da
abubuwan dake tattare da Sufaye, sai mu ga cewa Musulunci shi kadai
bai zama tushen Sufanci. Dalili kuwa shi ne,akwai abubuwa da dama
wadanda kusan dukkanin Sufaye sun yarda da su a matsayin wani bangare
na tafarkinsu,amma wadannan abubuwa ba su da tushe a cikin addinin
Musulunci. Ga misali,kusan dukkanin Sufaye sun yarda da batun ya ye
hijabi da dayantakar samuwa da wani abu da suke kira fana'i ko
wusuli,amma wadannan lamurra duka Musulunci bai san da su ba.
Hakanan,akwai wasu bangarori na rayuwar addini inda Sufaye suka
wuce makidi da rawa,su ka kai ga matsayin da akalla za'a iya kiran su
da masu bidi'a.Wadannan sun hada da wuce gaya wajen lamurran ibada da
tsananta abubuwa da Allah (S.W.A)ya saukaka na rayuwa. Akwai,ga
misali,Sufayen da suka haramta WA kansu aure tare da cewa aure Sunna
ce ta Annabi (S.A.W),wasu kuma suka haramta wa kansu cin nama tare da
cewa nama halal ne kuma yana daga mafi soyuwar abinci wurin
Annabi(S.A.W).
To idan haka halin Sufaye yake,ya za'a ce Sufanci ya samo asali
daga Musulunci tsintsa?(sai dai anan ma dole mu lura da bambanci
tsakanin Sufayen jiya da na yau.Sufayen yau,wasu bayan mata hudu ma
har sa-daka da kuyangi gare su.)

Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 11 Insha Allah.

Abu Aisha Journalist
Jibwis Social Media Katsina

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve