Thursday, 21 September 2017

*FITOWA TA 11
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA KUR'ANI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com

Watakila mai karatu ya yi tambaya:Don me yan Shi'a ba su buga
wannan tafkeken "kur'ani" nasu,wanda ya ninka na Musulmi har sau uku,
su sayar a kasuwa? Amsa ita ce,abinda yake hana su bayyana Wannan
littafi nasu shi ne takiyya,watau munafunci da yaudara!! A hakika yan
Shi'a ba Kur'aninsu kadai suke boyewa ba;akidarsu ta takiyya tana
umarnin su da boye manyan littafan malamansu,wadanda suka kunshi
akidojinsu da manufofinsu,sai ga manyan mabiyansu wadanda suka riga
suka yi zurfi a cikin tafarkinsu.Kadan daga cikin littafansu suke
sayarwa a kasuwa,sauran sai dai a same su a manyan cibiyoyinsu da
makarantunsu.Kur'aninsu kuwa,idan akwai shi cikakke,to babu shakka ba
mai ganin sa sai manyan shaihinnansu da,sai kuma almajirai amintattu.

Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 12 Insha Allah.

Abu Aisha Journalist
Jibwis Social Media Katsina

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve