*FITOWA TA 12
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA KUR'ANI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
Wannan ya sa yan Shi'a suke kalubalantar mutane da
cewa,idan gaskiya ne suna da nasu Kur'ani dabam,kamar yadda ake
dangana musu(ko da yake mai karatu yana iya ganin cewa ruwayoyinsu ne
suka tabbatar da samuwarsa)to don me ba'a fito musu da shi su gan
shi?Su kanyi tambaya:Ina Kur'anin nasu yake?
To wannan tambaya tasu malamansu sun amsa ta da
kansu.Shaihinsu,Hussain Alkhurasani yana cewa "Mu yan Shi'a muna
kudure cewa akwai wani Alkur'ani da Imam Ali ya rubuta da hannunsa mai
albarka, bayan da ya kare yi wa Annabi sutura kuma ya zartar da
wasiyyarsa.Littafin ya ci gaba da zama a hannun Imamai a matsayin
amana daga Allah har ya iso ga Imam Mahadi wanda ya adana shi kuma zai
fito da shi a yayin da zai bayyana." [Duba Al'islam ala Dau'it
Tashayyu'i na Hussain Alkhurasani,ba tarihi,shafi na 204.]
Wannan ruwaya yana tabbatar da cewa kur'anin yan Shi'a ya
kasance akwai shi,kuma ya ci gaba da zama a hannun Imamai har na
tsawon kimanin shekaru 250 daga zamanin Sayyidina Ali(R.A) zuwa
zamanin mahadinsu(watau Imaminsu na 12)wanda aka haife shi a shekara
ta 225 bayan Hijira.Wannan Imamin nasu shi ne ya tafi da littafin a
lokacin babbar fakuwarsa,kuma zai komo da shi a lokacin da zai bayyana
a karshen duniya.
Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 13 Insha Allah.
Abu Aisha Journalist.
Jibwis Social Media Katsina.
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve