*FITOWA TA 11
*Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
Idan muka lura da kyau daga abinda ya gabata na hasashe
uku da muka ambata a sama,za mu gane cewa duka masu wadannan hasashe
sun yi kusuri wajen fahimtar Sufanci, domin sun dube shi ta bangare
guda kawai a yayin da suka kawar da kai ga barin wasu bangarorin.Masu
hasashe na daya,wadanda suke su raba Sufanci cancakar da Musulunci,
sun mayar da shi ga falsafar Girkawa. Wadannan mutane sun kau da kai
ga barin wasu bangarori na Sufanci wadanda babu mai musun cewa daga
Musulunci suke.Masu hasashe na biyu,wadanda dama yawancinsu
gabasawan-giri ne kamar yadda muka gabatar,sun ce Kiristanci shi ne
tushen Sufanci. Su kuwa masu hasashe na uku,wadanda yawancinsu Sufaye
ne su da kansu,sun nace akan cewa tafarkinsu ya samo tushe daga
addinin Musulunci tsintsarsa.
Amma gaskiyar lamarin ita ce,Sufanci bai da tushe guda,domin
kuwa ya samo asali daga wurare dabam-daban.Wannan ya sa ya kunshi
abubuwa mabambanta wadanda kuma suka yi nesa da juna.A cikin Sufanci
akwai Musulunci da falsafar Girkawa, da addinin Yahudu da Nasara,da
kuma gyauron tsoffin addinai na Gabas mai Nisa kamar Budanci na kasar
Sin da Indiya.Wannan ita ce hakikanin magana dangane da tushen
Sufanci, kuma a fili take ga duk mutumin da ya san Sufanci sani na
hakika.
Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 12 Insha Allah.
Abu Aisha Journalist.
Jibwis Social Media Katsina.
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve