*FITOWA TA 12
*Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
YADUWAR SUFANCI
Sufanci ya yadu yaduwa mai yawa a lokaci kankane.Har ya
zuwa karshen karni na biyu,Sufanci bai wuce garuruwan kufa da Basra
ba.Amma kafin karni na uku ya shude,sai da ya game manyan kasashen
Musulunci kamar Misira,Naisabur,Balah,Sham,Bagdada da sauransu.
Daga nan kuma sai Sufanci ya fara yaduwa.Jama'a sun yi
ta shigar sa kuma nashadin Sufaye ya yi ta karuwa.Suka tashi tsaye
wajen yada shi da karfafa tushensa.Suka WALLAFAR littafai masu yawa
don cimma wannan manufa.Daga nan ne Sufanci ya kama hanya zuwa
matsayinsa kamar yadda muka san shi a yau.A kan wannan hanya tasa ya
taka matakai guda uku.
Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 13 Insha Allah.
Abu Aisha Journalist.
Jibwis Social Media Katsina.
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve