*FITOWA TA 13
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA KUR'ANI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
Yan Shi'a suna kudure cewa Imaminsu na 12,wanda suke kira
Mahadi ya faku fakuwa biyu,babba da karama.A lokacin karamar
fakuwa,wacce ta yi tsawon shekara 65,ya rika saduwa da manyan
almajiransa wadanda ya rika aiko su da sakwanni zuwa ga mabiyansa.Kuma
a shekara ta 259 bayan Hijira, ya shiga fakuwa babba,wacce ya kai har
zuwa yau,kuma wacce a cikinta ba ya saduwa da kowa.Wannan babbar
fakuwa za ta kare a karshen duniya, sa'ad da Mahadin zai bayyana don
ya kaddamar da wasu ayyuka masu ban tsoro da ban mamaki.[Domin bayanin
wannan tatsuniya,duba A CRITICAL REVISION OF SHI'A na Imam Musa
Musawi,bugun the supreme Islamic Council,
Columbia-Amurka,1412/1992,shafi na 77-78.]
Mai son ganin wadannan ayyuka,sai ya duba littafinmu mai taken MUGUN
NUFIN YAN SHI'A GA AL'UMMA.
Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 14 Insha Allah.
Abu Aisha Journalist.
Jibwis Social Media Katsina.
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve