*FITOWA TA 13
*Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
MATAKIN IBADA DA GUDUN DUNIYA
Matakin Ibada shi ne mataki na farko da Sufanci ya
taka,kuma wasu daga cikin sifofin da Sufanci yake da su a wannan
mataki sun lizimce shi a sauran dukkan matakan.Mafi bayyanar wadannan
sifofi su ne:lazimtar ibada,gudun duniya,tsantseni,ikhlasi,gwagwarmaya
da yakin zuciya da kuma riko da hukunce-hukuncen shari'a.
A wannan mataki,Sufaye sun siffantu da sifofin komawa ga Allah
dungurum cikin dukkan lamurra,juya baya ga duniya da
kyale-kyalenta,kauracewa mutane da barin cudanya da su,da shiga halwa
domin ibada.
Yawancin ra'ayoyin Sufaye da sifofin Sufanci a wannan mataki
sun samo tushe daga Musulunci, kuma sun dogara a kan bin shari'a da
koyi da magabata,watau Sahabban Annabi(S.A.W) da Tabi'ansu.Babu wata
falsafa,bakon tunani ko gyauron wani addini da ya shiga Sufanci a
wannan mataki,sai fa abinda ba'a rasa ba.
Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 14 Insha Allah.
Abu Aisha Journalist.
Jibwis Social Media Katsina.
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve