Tuesday, 26 September 2017

*FITOWA TA 14.
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA KUR'ANI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com

Har yau,wani malamin nasu ya ba da bayani mai kama da
wannan.Ya ce,"Bayan rasuwar Annabi,Sarkin Musulmi (yana nufin Ali) ya
dauko Alkur'ani a cikin mayafinsa,ya kawo wa Abubakar da Umar suna
zaune a Masallaci su da wasu mutane. Ya ba su shi,amma sai suka ce:Ba
mu bukatar Kur'aninka;muna da namu Kur'anin,ya ishe mu! Sai ya ce:Shi
ke nan,ba za ku kara ganin sa ba daga yau,sai Mahadi ya bayyana!"[Duba
NUR AL'ANWAR FI SHARHIS SAHIFATIS SAJADIYYA na Ni'imatullahi
Aljaza'iri,bugun Darul Mahajjatil Baida,Bairut 1420,shafi na 175.]
Wadannan bayanai daga malaman Shi'a,idan sun gasgata,suna
tabbatar da cewa Kur'anin yan Shi'a ya kasance akwai shi a hannun
Imamansu,kuma almajiran Imamai sun karanta shi har lokacin da imami na
12 ya shiga dashi kogo inda ya faku fakuwarsa ta karshe.Saboda haka
sai su jira shi daga nan har sanda jaki ya tsiri kaho!
Akwai wani dan Shi'a wanda ya taba yin wata burga.Ya dauko
Kur'ani cikakke na Musulmi, wanda aka buga a kasar Iran,ga tambarin
Jumhuriyyar Islama rangadau a bangin littafin.Sa'annan ya ce,"kun ce
yan Shi'a ba su yarda da Kur'ani ba,ya akayi suka buga wannan? " Sai
aka ce masa,ai buga Kur'ani ba shi ne yarda da shi ba.Idan yan Shi'a
sun yarda da Alkur'ani don me suke kafirta wadanda Alkur'ani ya yi wa
shaida da imani,watau Sahabban Annabi(S.A.W)? Sai gogan na ka ya yi
turus! Allah ya tsarshe mu bata.

Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 15 Insha Allah.

Abu Aisha Journalist.
Jibwis Social Media Katsina.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve