Tuesday, 19 September 2017

*FITOWA TA 8
*Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com

HASASHE NA DAYA
Za mu fara da hasashen Falsafar Girkawa.Afladuniya Sabuwa
ita ce mazhabar falsafa wacce dadadden failasufin nan Bagirke mai suna
Sakkas ya kago ta.Shi Sakkas ya fara rayuwarsa a matsayin dan dako
kuma daga baya ya nemi ilimin falsafa har ya zama babban failasufi.Har
ya zuwa rasuwarsa,Sakkas bai bar wasu littafai ko rubuce rubuce ba a
kan bayanin mazhabarsa ta falsafa.sai bayan mutuwarsa ne,almajirinsa
Afladin,ya tattara maganganunsa da koyarwarsa da tunane-tunanensa ya
rubuce su,wanda wannan aiki shi ya tabbatar da wanzuwar mazhabar
tasa.Don haka ne kuma ake kiran mazhabar da sunan almajirin,watau
Afladuniya.
Babu shakka Musulmi sun fassara littafan Girkawa zuwa harshen
Larabci,haka nan kuma sunyi darasun falsafofinsu da
tunane-tunanensu,kuma hakan ya yi tasiri ga rayuwar Musulmi da
tunaninsu.Har wa yau kuma,babu shakka cewa mazhabar Afladuniya Sabuwa
ta yi tasiri ga ayyukan Musulmi na fagen tunani,musamman Sufaye,kamar
yadda za'a iya gani a rubuce rubucen yan Ikhwanus Safa,wata kungiyar
asiri ta Sufaye.To amma duk da haka masu bincike na ganin cewa rashin
adalci ne a dangana Sufanci ga wannan mazhaba ita kadai,ko kuma ace
Afladuniya Sabuwa ita ce tushen Sufanci. Dalili kuwa shi ne,Sufanci ya
dade da yaduwa a tsakanin Musulmi kafin su fassaro littafan Girkawa ko
su tasirantu da falsafarsu.
Sai dai babu mai musun cewa akwai falsafar Girkawa da
ra'ayoyinsu a cikin Sufanci, kamar yadda zamu gani a nan gaba yayin da
muka zo magana a kan matakan Sufanci.Ra'ayoyin Sufaye dangane da
sani(ilimi),fana'i,yaye hijabi,da sauransu,duka sun samo tushensu ne
daga falsafar Girkawa da sauran falsafofin wasu al'ummai,kamar mutanen
Sin,Indiya,Masar ta dori,da sauransu.
Saboda haka,ba mu iya cewa Afladuniya Sabuwa ita kadai ita ce
tushen Sufanci kamar yadda ba mu iya musun tasirinta a
cikinsa.Afladuniya na daga cikin shika-shikan Sufanci wadanda aka dora
ganinsu a kansu.

Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 9 Insha Allah.

Abu Aisha Journalist
Jibwis Social Media Katsina

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve