Monday, 18 September 2017

*FITOWA TA 8
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA KUR'ANI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com

Kur'anin yan Shi'a ya sha bamban da Alkur'anin Musulmi ta
fuskoki masu yawa.Mun riga mun gabatar da bayanin bambancinsu ta wajen
jimillar ayoyinsu,inda Kur'anin yan Shi'a yake da adadin ayoyi dubu
sha bakwai(17,000)dai-dai wa daida,a yayinda namu yake da ayoyi dubu
shida da dari biyu da talatin da shida(6,236)kacal.Ta fuskar tsawon
surori ma,littafan guda biyu sun sha bamban.Ga misali,ya zo a cikin
KITAB SULAIM BINU KAIS,mashahurin littafin nan na Shi'a wanda saboda
ingancinsaa wajensu suke masa lakabi da A.B.C. Din Shi'a, cewa wai
SURATUL AHAZAB wacce take da ayoyi 73 a kur'aninmu,su a nasu Kur'anin
adadin ayoyin BAKARA ne da ita,watau 286.SURATUN NUR kuwa,wacce take
da ayoyi 64,su a wajensu ayoyi 160 ke gareta.SURATUL HUJURATI
kuma,wacce a cikin Kur'anin da muka sani ayoyinta 18 ne kacal,su a
nasu Kur'anin ayoyinta 90 ne dai-dai was daida.[Duba KITAB SULAIM BINU
QAIS na Sulaim binu Qais Alhilali Alkufi,bugun Mu'assasatul
A'alami,Bairut,ba tarihi ,shafi na 122.]

Anan zamu dakata sai kuma fitowa ta 9 Insha Allah.

Abu Aisha Journalist
Jibwis Social Media Katsina

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve