Monday, 18 September 2017

*FITOWA TA 7
*Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com

BULLAR SUFANCI DA YADUWARSA

Malamai da masana tarihi sun hadu a kan cewa Sufanci ya bulla
duniyar Musulmi a cikin karni na biyu bayan Hijira,watau a cikin
shekara dari ta biyu bayan kaurar Manzon Allah (S.A.W).Hasali ma,masu
bincike sun kai ga samo asalin mutum na farko wanda aka fara kira da
lakabin Sufi a duniya.Wannan mutum shi ne Abu Hashim Alkufi
Assufi,wanda ya rasu a shekara ta 150 bayan Hijira. Wani abu da yake
karfafa wannan ra'ayi shi ne,duk manyan litattafan da aka rubuta a kan
Sufanci, ba wanda ya yi magana a kan abinda ya wuce wannan
tarihin,watau karni na biyu bayan Hijira.
Da yake mun ga zamanin da Sufanci ya bulla,to bari mu duba mu ga
shin wadanne abubuwa ne suka kawo bullar tasa,ko kuma a takaice,ina
Sufanci ya samo tushensa?Malamai sun yi hasashe da dama a kan asalin
Sufanci da tushensa.Akwai masu ganin cewa,Sufanci ya samo asali ne
daga addinin Musulunci tsintsa,watau daga Alkur'ani da sunnar
Annabi(S.A.W).Akwai kuma masu hasashen cewa Sufanci ya samo asalinsa
ne daga addinin Kirista ta hanyar cudanyar Musulmi da Kiristoci,bayan
Musulunci ya ci kasashensu da yaki.Masu hasashe na uku kuwa suna ganin
cewa Sufanci ya samo tushe ne daga wata falsafa ta Girkawa da ake kira
Afladuniya Sabuwa.
Yanzu bari mu duba wadannan ra'ayoyi guda uku tare da bayanin
malamai a kansu.

Anan zamu dakata sai kuma a fitowa ta 8 Insha Allah.

Abu Aisha Journalist
Jibwis Social Media Katsina

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve