*FITOWA TA 9
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA KUR'ANI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
Ta fuskar adadin surori ma,akwai dan bambanci saboda akwai
wasu surori wadanda yan Shi'a suke kudure cewa an debe su daga cikin
Alkur'ani. Misali shi ne wata sura da suke kira SURATUL WILAYA wacce
suka ce wai a cikinta Allah ya yi umarni da nada Ali binu Abi Dalib a
matsayin Khalifa bayan rasuwar Annabi(S.A.W).Wannan sura ba mu san ta
ba,babu ita a cikin Alkur'aninmu,amma su yan Shi'a suna kudure cewa
wai Sahabbai ne suka debe ta don cin amana.a fadinsu,domin su hana Ali
binu Abi Dalib(r.a)hakkinsa na gadar Annabi,suka nada Abubakar a
makwafinsa.Wannan ita ce akidarsu.Wal iyazu billah!!
Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 10 Insha Allah.
Abu Aisha Journalist.
Jibwis Social Media Katsina.
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve