Thursday, 28 September 2017

*FITOWA TA 15.
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA KUR'ANI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com

Bayan mun gabatar da bayani a kan wannan akida kamar yadda
take a cikin littafan yan Shi'a masu inganci a wajensu,muna ganin babu
karin bayani dangane da abinda akidar ta tattare na kafirci da jahilci
da bata.Amma saboda yankan hanzari ga masu kiran kansu yan Shi'a, bari
muyi bayanin kafircin wannan akida a takaice.
Da farko dai akidar ta karyata Alkur'ani mai girma saboda a
cikinsa Allah mai girma da daukaka ya tabbatar da cewa ya tsare
Littafinsa ta yadda kari ko ragi ba za su shige shi ba.Ubangiji
Madaukaki ya ce,"Lalle,mu ne muka saukar da Ambato (Alkur'ani), kuma
lalle mu,masu kiyayewa ne gare shi."(Suratul Hijr:9). A wata ayar
kuma,ya tabbatar da cewa barna ba ta shiga wannan littafi ko ta halin
kaka: "Wadannan da suka kafirta game da Alkur'ani a lokacin da ya je
musu,kuma lalle ne,hakika,littafi ne mabuwayi.Barna ba za ta zo ba
daga baya gare shi .Saukarwa ce daga Mai Hikima,Godadde." Suratu
Fussilat:41-42).

Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 16 Insha Allah.

Abu Aisha Journalist.
Jibwis Social Media Katsina.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve