Sunday, 1 October 2017

TUNATARWA: KOMAWA KARATUN Imam Nasir Abdurrahman A GARIN FUNTUA.

Sakamakon Hutu da akaje na karatukan da Malam yake gabatarwa a wurare daban-daban a garin Funtua, Tun daga wanda akeyi a Masjidus Sunnah Kwanar Kwadai, da Wanda akeyi a Masjidu Jami'u Hajarat Plaza duk bayan Magrib zuwa Isha'i, da kuma wanda akeyi a Masallacin gidan Malam da Asuba.
Insha Allah za'a komo dukkan karatukan daga yau dinnan Juma'a 08/01/1440  (29/09/2017).

Hoto:
*Littafin da za'ayi kenan Yau dinnan (In Allah Yaso) SUWARUN MIN HAYATIT TABI'IN (Tarihin Tabi'ai).*

Da fatan za a isar da wannan saqo.

Sanarwa daga:
Jibwis Social Media Katsina State.
JibwisKatsina.blogspot.com

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve