Sunday, 25 June 2017

Wasu daga cikin jerin Tafsirin Al-qur'ani mai girma na garin Katsina

📀📀📀📀📀📀📀📀📀📀📀📀📀📀📀📀
✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴
*Malam Zakariya Aliyu Sandamu*
🎤1. http://k003.kiwi6.com/hotlink/5tukiwtgwf/
01_Ramadan_Tafsir_-_Malam_Zakariya.mp3

🎤2. http://k003.kiwi6.com/hotlink/ja53ql40aq/
02_Ramadan_Tafsir_-_Malam_Zakariya.mp3

🎤3. http://k003.kiwi6.com/hotlink/q99t3qydvb/
2017-05-29_16_2751_2735_27.mp3

🎤4. http://k003.kiwi6.com/hotlink/rcs3x238zi/
04_Ramadan_Tafsir_-_Malam_Zakariya.mp3

🎤5. http://k003.kiwi6.com/hotlink/8axrnki5rr/
05_Ramadan_Tafsir_-_Malam_Zakariya.mp3

🎤6. http://k003.kiwi6.com/ …/foqe4yycoa/
M._Zakariyya_Aliyu_Sanda…

🎤7. http://k003.kiwi6.com/hotlink/d1skcx04l9/
REC007.lite.mp3

🎤8. http://k003.kiwi6.com/hotlink/q5qjfeun74/
REC009.lite.mp3

🎤9. http://k003.kiwi6.com/hotlink/50616y4rsu/
REC010.lite.mp3

🎤10. http://k003.kiwi6.com/hotlink/ivkn9nzpmn/
REC012.lite.mp3

🎤11. http://k003.kiwi6.com/hotlink/83y2ky8li5/
REC014.lite.mp3

🎤12. http://k003.kiwi6.com/hotlink/mps4hkfqv0/
REC015.lite.mp3

🎤14. http://kiwi6.com/file/6a2pbub3j7

🎤15. http://kiwi6.com/file/gtv98teku4

🎤16. http://kiwi6.com/file/7johe2gk7z

🎤17. http://kiwi6.com/file/nxoftabfm0

🎤18. http://kiwi6.com/file/ad9lujhajm

🎤19. http://kiwi6.com/file/b94wwfqiza

🎤20. http://kiwi6.com/file/3ux7eiis44

🎤21. http://kiwi6.com/file/nhkralijne

🎤22. http://kiwi6.com/file/rijgxpieq8

🎤23. http://kiwi6.com/file/xmnwx79re7

🎤24. http://kiwi6.com/file/n9mu3wb57w

🎤25 http://kiwi6.com/file/ntysrfiw3r

🎤26. http://kiwi6.com/file/uevvf6z2nu

🎤27 http://kiwi6.com/file/dy1pse9dxr

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴
*Malam Abdullahi Ayuba*

🎤1. http://k003.kiwi6.com/hotlink/4rhda68o68/
AUD-20170527-WA0017.amr

🎤2a. http://k003.kiwi6.com/hotlink/46nhwzsdkg/
02a_Ramadan_Tafsir_-_Mal._Abdullahi_Ayub.amr

🎤2b. http://k003.kiwi6.com/hotlink/yglkvxjgby/
02b_Ramadan_Tafsir_-_Mal._Abdullahi_Ayub.amr

🎤3. http://k003.kiwi6.com/hotlink/n70jxd28mf/
03_Ramadan_Tafsir_-_Mal._Abdullahi_Ayub.amr

🎤4. http://k003.kiwi6.com/hotlink/u02sv4up3m/
04_Ramadan_Tafsir_-_Mal._Abdullahi_Ayub.amr

🎤5. http://k003.kiwi6.com/hotlink/5zttsddlyj/
05_Ramadan_Tafsir_-_Mal._Abdullahi_Ayub.amr

🎤6. http://k003.kiwi6.com/ho …/zsmopp2s63/
AUD-20170606-WA0002.amr

🎤7. http://k003.kiwi6.com/ho …/knv9op8vib/
AUD-20170606-WA0003.amr

🎤8. http://k003.kiwi6.com/ho …/7ynav0gehr/
AUD-20170606-WA0004.amr

🎤9. http://k003.kiwi6.com/ho …/7m2xxqq3sx/
AUD-20170606-WA0005.amr

🎤10. http://k003.kiwi6.com/ho …/s3wru7o63v/
AUD-20170606-WA0006.amr

🎤11. http://k003.kiwi6.com/ho …/w4gcl7k87g/
AUD-20170607-WA0003.amr

🎤14. http://k003.kiwi6.com/ …/14_Ramadan_Tafsir_-_Mal._Abdullahi_…

🎤15 http://k003.kiwi6.com/ …/15_Ramadan_Tafsir_-_Mal._Abdullahi_…

🎤16 http://k003.kiwi6.com/ …/16_Ramadan_Tafsir_-_Mal._Abdullahi_…

🎤17. http://k003.kiwi6.com/ …/17_Ramadan_Tafsir_-_Mal._Abdullahi_…

🎤18. http://k003.kiwi6.com/ …/18_Ramadan_Tafsir_-_Mal._Abdullahi_…

🎤19 http://k003.kiwi6.com/ho …/59gu2e3do7/
AUD-20170614-WA0022.amr

🎤20. http://k003.kiwi6.com/ …/20_Ramadan_Tafsir_-_Mal._Abdullahi_…

🎤21. http://k003.kiwi6.com/hotlink/ncc1akfuym/
21_Ramadan_Tafsir_-_Mal._Abdullahi_Ayub.mp3

🎤22. http://k003.kiwi6.com/hotlink/cknqlxcj8a/
22_Ramadan_Tafsir_-_Mal._Abdullahi_Ayub.mp3

🎤23. http://k003.kiwi6.com/hotlink/rxzp68ozgz/
23_Ramadan_Tafsir_-_Mal._Abdullahi_Ayub.mp3

🎤24. http://k003.kiwi6.com/hotlink/ldwofcqmxw/
24_Ramadan_Tafsir_-_Mal._Abdullahi_Ayub.mp3

🎤25. http://k003.kiwi6.com/hotlink/djrisvowjt/
25_Ramadan_Tafsir_-_Mal._Abdullahi_Ayub.mp3

🎤27. http://k003.kiwi6.com/hotlink/kgaqr4vccl/
AUD-20170623-WA0011.amr

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴
*Malam Aminu Usman (Abu Ammar)*


🎤1. http://darulfikr.com/s/23119

🎤2. http://darulfikr.com/s/23121

🎤3. http://darulfikr.com/s/23122

🎤4. http://darulfikr.com/s/23123

🎤5. http://darulfikr.com/s/23124

🎤6. http://darulfikr.com/s/23125

🎤7. http://darulfikr.com/s/23126

🎤8. http://darulfikr.com/s/23127

🎤9. http://darulfikr.com/s/23128

🎤10. http://darulfikr.com/s/23129

🎤11. http://darulfikr.com/s/23130

🎤12. http://darulfikr.com/s/23131

🎤13. http://darulfikr.com/s/23132

🎤14. http://darulfikr.com/s/23133

🎤 15. http://darulfikr.com/s/23345

🎤16. http://darulfikr.com/s/23134

🎤17. http://darulfikr.com/s/23270

🎤18. http://darulfikr.com/s/23272

🎤 19. http://darulfikr.com/s/23346

🎤20. http://darulfikr.com/s/23452

🎤 21. http://darulfikr.com/s/23538

🎤 22. http://darulfikr.com/s/23656

🎤 23. http://darulfikr.com/s/23785

🎤 24. http://darulfikr.com/s/23879

🎤 25. http://darulfikr.com/s/23948

🎤 26. http://darulfikr.com/s/24002

🎤 27. http://darulfikr.com/s/24082

🎤 28. http://darulfikr.com/s/24324
✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴
*Mal. Muhammad Usamatu Abbas*

🎤 01. http://darulfikr.com/s/23416

🎤 02. http://darulfikr.com/s/23417

🎤 03. http://darulfikr.com/s/23418

🎤 04. http://darulfikr.com/s/23420

🎤 05. http://darulfikr.com/s/23419

🎤 06. http://darulfikr.com/s/23421

🎤 07. http://darulfikr.com/s/23422

🎤 08. http://darulfikr.com/s/23423

🎤 09. http://darulfikr.com/s/23424

🎤 10. http://darulfikr.com/s/23425

🎤 11. http://darulfikr.com/s/23426

🎤 12. http://darulfikr.com/s/23427

🎤 13. http://darulfikr.com/s/23428

🎤 14. http://darulfikr.com/s/23429

🎤 15. http://darulfikr.com/s/23430

🎤 16. http://darulfikr.com/s/23431

🎤 17. http://darulfikr.com/s/23432

🎤 18. http://darulfikr.com/s/23433

🎤 19. http://darulfikr.com/s/24322

🎤 20. http://darulfikr.com/s/23602

🎤 21. http://darulfikr.com/s/23738

🎤 22. http://darulfikr.com/s/23878

🎤 23. http://darulfikr.com/s/23966

🎤 24. http://darulfikr.com/s/23967

🎤 25. http://darulfikr.com/s/24071

🎤 26. http://darulfikr.com/s/24279

💳💳💳💳💳💳💳💳💳💳💳💳💳💳

_Ayi sauraro lafiya_
Email: jibwissocialmediaktlg@gmail
Facebook: Jibwis Katsina L.G
WhatsApp: 07062584992, 08036487324, 08038977817, 08034453678, 08036958490

Thursday, 22 June 2017

KWAMITIN TALLAFAWA MARAYU, SUN TALLAFAWA MARAYU,1,252.00 YAU A BIRNINKEBBI


A yaune  kwamitin tallafawa marayu da ke masallacin *jibwis* na sheikh *Abbas jega* dake  anguwar rafin atiku  a nan cikin garin Birninkebbi suka  tallafawa marayu dubu daya da  dari biyu da hamsin da biyu (1,252.00) a wuraren da  suka  tsara  a nan  cikin garin Birninkebbi,
Shugaban kwamitin Alhaji *Abdullahi Gebe*  ne  ya  sanar da  hakan  a lokacin da  manema labarai  suka ziyarci  wurin da  ake  bayar da  tallafin  da  safiyar yau,

Haka shima Uban Doman Gwandu  Alhaji  *Khalidu Sa'ad,*  yayi kira  ga  gwamnati, yan kasuwa,  yan siyasa da kuma  Ma'aikata  da  su  bada  goyon bayan su  ga  wannan shirin  da  kungiyar izala ta  kasa  ta  kirkiro  tun  shekaru  da  suka gabata  domin  tallafin  yanada  alfano  matuka,

Anashi  bayanin  daga  bisani,shugaban kwamitin,  Alhaji *Abdullahi  Gebe  Argungu*  ya  yi  matukar godiya  amadadin kwamitin baki daya, ga  duk ilahirin  wadanda suka bada nasu tallafin  domin wannan shirin ya ci nassara, Musamman shugaban masu rinjaye  a majalisar jaha  watau  Hon. *Bello  Rilisco* akan bada tallafi mafi tsoka  a kowace  shekara,
Allah ya sa ka wa  kowa da alkhairi,

*Adamu Attahiru*
Jibwis social media
26/09/1438
21/06/2017

Wednesday, 21 June 2017

KMAMITIN TAFSIRI NA KASA YAKAI ZIYARA GA SHEIKH ABBAS JEGA


Cikin ikon Allah min samu ziyartar Tafsirin dare na Sheikh Abbas Muhammad Jega, Madugu uban tafiya, kuma jagoran tafiyar Sunnah a Jihar kebbi a Jiya Talata 20th June, 2017 wanda yayi muwafaqa da 25 ga Ramadan 1438 wanda yake gabatarwa a garin Jega da dare.

Bayan isar da jawabin godiya da fatan Alkhairi ga Shehin Malamin tare da Al'ummar Musulmin Jihar kebbi daga bakin Shugaban Kwamitin Tafsiri na Kasa, anyi amfani da wannan dama domin gabatar da Addu'o'i na musamman ga al'ummar musulmi mudamman wadanda duke cikin tsangwama da damuwa, sannan ga kasarmu Nigeria musamman Babban Kwamanda kuma Madugu Uban tafiya Mal. Alh. Dr. Gen Muhammadu Buhari (hafizahullah wa ra'ah) kan Allah ya bashi cikakkiyar lafiya Don cigaba da aikin Alheri wanda ya faro na yin gyara ga yanayin da kasarmu ta samu kanta a ciki. ALLAH YA MAIDOSHI GAREMU LAFIYA.

Shehin Malamin yayi Addu'a ta musamman ga Matasa akan Allah ya kebo hankalinsu Don tsayuwa akan addini da kyakkyawar dabi'a, sannan yayi addu'a gamammiya ga al'ummah Don ganin an samu ingantaccen yanayi musamman abunda ya shabi tsaro, tattalin arziki, Damina mai albarka don samun isasdhen abinci a kasa

Sheikh Abbas Muhammad Jega yana gabatar da tafsir har say 3 a kowacce rana tare da Alaramma Ridwan Muhammad Kaduna wanda kwamitin Tafsiri na Kasa ya turo Don yin wannan aiki tare da sheikh a garin Jega da Birnin kebbi. Allah ya sanya wannan aiki a mizanin Hasanaat, ya Karawa rayuwa albarka

Muhammad Jameel Maharaz
Sakataren Kwamitin Tafsiri na Kasa
JIBWIS NIGERIA
26th Ramadan, 1438
21st June, 2017

Tuesday, 20 June 2017

'YAN AGAJI MATA KATSINA DIVISION.

'YAN AGAJI MATA KATSINA DIVISION.
First Aid Group Of Jibwis Women Detachment Katsina.

Ziyarar duba gudanar ayyukan 'yan agaji mata da shugabar 'yan agajin sashen mata HAJIYA  AINA'U SUFYANU  tayi tare da  NABEELATU D ALEEYU (sakatariya)  a yau lahadi 23/9/1438Ah, a wuraren da aka tura (posting) 'yan agaji domin bada agajinsu a wajen   gudanar da tafsirin Al-Qur'ani mai girma na mata a wannan wata na Ramadan 1438/2017.

Alhamdulillah a yayin wannan ziyara bamu samu inda akayi kuka da 'yan agajinmu ba saidai ma samun yabo da sukayi gami da jinjina adukkan wuraren da aka turasu don gudanar da aikinsu, sanadiyyar kyawun aikinsu da dabi'unsu yasa 'yan uwa mata da dama suka nuna sha'awarsu da neman  a taimaka abasu damar sake daukar sabbin 'yan agaji don su ma su shiga wannan aiki wanda ladarsa saidai a wurin Allah.

Nabeelatu D Aleeyu.
18/6/2017.

Saturday, 17 June 2017

BAYANI AKAN QIYAMU RAMADAN A GOMAN KARSHE


Wannan wani Audio ne na wata takarda da shehin malami DR IBRAHIM JALO JALINGO ya gabatar a wani taron karawa juna sani da kungiyar JIBWIS ta Nigeria ta gabatar a garin Katsina.
Shugaban zaman kuma shine DR ALHASSAN SAEEED ADAM JOS (Rahimahullah) Kuma shine yayi Ta'alikin takardar.

Kadan daga Abubuwan dake ciki:

* Takaitaccen tarihin Dr Ibrahim Jalo Jalingo a Duniyar Ilimi.

* Sallar Tarawihi itama Qiyamu Ramadan ce? Kuma Raka'oi nawa akeyi?

* Hujjojin Mazhabobi akan Sallar Tarawihi cikin Jam'i da kuma Hujjar da tafi qarfi.

* Abin nufi da sallar Tahajjud, da sunayen da ake kiranta dasu.

* Hukuncin Fitar Mata zuwa Masallaci Domin sallar Tahajjud.

Damin saukewa a wayarka ka saurara dannan wannan link

Ayi sauraro lafiya.

© Nazeer Danjagale
Jibwis Social Media Katsina
www.JibwisKatsina.blogspot.com
1438 / 2017

Thursday, 15 June 2017

GOMAN KARSHE!!!



Wanda ya riski ramadan harya fita ba'a gafarta masaba hakika rabo me girma ya kubuce masa. dukkan Alkhairi yayi nisa dashi, ko wace irin asara ta sameshi, kaico! wananna raunanannan bawa yayi asara.

Ya tsawaita kukansa da nadamarsa da bakin cikinsa, wanda ya riski goman 10 karshe na ramadan amma bai sadar da dararenshi da nafila ba, bai jiyar da kanshi dadi da karatun alqur'ani ba, be haskaka gidansa da Zance mafi dadiba.

Bai rayar da masallatansu da sauraran wa'azi ba, hakika yayi tasgwaro a rayuwarsa, an hana masa zakin imani, an hana masa dandanon koyi da Annabin rahma.

(S A W ); Bai ci gajiyar da bayin Allah ke samu ba, shi manzon Allah idan goman karshe ta shigo yana kara nunka aiyukansa.

Ance yafi iska yawan alkhairi, ba'a taba samun wanda yakai kyautar manzon Allah ba ,Amma idan goman 10 karshe tazo yana rubanya aiyukansa.

Yakasance kullum mala'ika jibrilu (AS) yana zuwa gareshi kullum sunayin karatun alqur'ani mai girma, madalla da wananna malami jibrilu,

Madallah da wanda ake Koyawa manzon Allah, Madallah da wananna majalisi mai girma.

A goman 10 karshene manzon Allah ( S A W ) yakan nade shinfidarsa ta barci, yakan kauracewa hutawarsa, yakan nade kafafun wandonsa zuwa sama wato ma'ana yakan daga yayi dammara ta tada iyalansa, dan suma su rusku cikin alkhairi

Saboda ganawarsa da mamallakin al'amura baki daya.

Cikin wadannan dararene masu albarka ake haduwa da dukkan nufi, ake kaiwa ga dukkan manufa, da dukkan biyan bukata.

A irin wadanan lokutane Allah ta'ala yake bayyana ga bayinsa da mafi nunkuwar lada, da mafi gwabin gafararsa, da tabbatacciyar afuwarsa da yafiya ga bayinsa nagari.

A kowace sa'a a kowane dare na ramadan Allah ( S W T) yana yanta mutum Dubu dari ya tabbatar musu baza ayi musu azaba ba.

A daren Karshen ramadan Allah Yana yantawa ninkin haka Bayan kowace dakika da kowace awa, da kowace kibtawa, lallai Allah mabuwayine.

Mai gafarane, mai iko ne, ba'a tuhumarsa ga dukkan abinda yayi.

shine mafificin masu jin kai.

Allah ta'ala yana cewa : ku kirayi ubangijinku Allah kuna masu rokonsa da takawa da tausasawa shi baya son masu shishigi, kada ku rika barna a bayan kasa.

Bayan an gyarata, ku rokeshi kuna masu jin tsoronsa tare da kwadayin rahamarsa, lallai rahamar Allah kusa take ga masu kyautatawa.

idan ya zama Allah Yana gafartawa masu laifuffuka har yawan wananna adadi, to yayi zai zama ga bayinsa na kirki masu jin kunyar sabonsa.

Aljannah ce makomarsu wadda korama ke suna gudana a cikinta, wata irin matsaya ta gaskiya nan ga mamallakin mai tsananin iko madalla da masu azumi suna kiyayewa.

suna masu alkhairi da gasgatawa, suna tsayawa suna tabbatuwa, suna yawan tuba farkon safiya, suna masu konkomawa da maraicensu. 
Madallah da wadannan matane da Babu kamarsu.

Kayima kanka hisabi ya bawan Allah yakai dan'uwana, a Karshen ramadan gabanin Allah yayima ka.

Kaduba takardun ayyukanka daka aikata, Meka gudanar a ramadan?

Shin Dame zaka tsira sa'adda kake karanta littafin aiyukanka ranar kiyama gaban Allah da mala'ikunsa ga Annabawa da Manzanni, da iyayenka, da matanka. da surukanka, ga abokanka sun hallara, da malamanka, da sauran jama'a. kowa yayi tsit kai ake sauraro?

Kayi nazari ka gani meya gudana gareka na sallah, da azumi , da biyayya ko ciyarwa, kyautatawa ko sadaka.

Tausayi ko daidaitawa tsakanin talakawa, rangwame ko yafewa?

Himmarka cikin bin Allah ko takaitawarka ga saba mishi.

Kayi kokarin cike gurbin abunda ka rasa na ayyukanka.

To ka rika tashi a lokatun da ake ganawa da Allah a Karshen kowane dare da bayan kowane sallar farilla don neman sulhu.

Ya Allah, mu mun zalunci kawunanmu zalinci mai yawa idan har baka gafarta mana ba, kuma baka jikanmu ba, hakika lallai zamu kasance daga cikin wadanda suka yi asara.

Ya Allah ka gafarta mana dukkan kura-kuranmu ka yafe mana zunubanmu ,ka daidaita imani a zukatanmu ka karbi ayyukanmu, ka yantar da mu da iyayenmu da ya'yanmu da yan'uwanmu, daga barin wuta kasanya jannatul firdausi ta zama makoma garemu, tare da dukkan musulmi baki daya.

Kai mai iko ne akan komai wajen karba mana addu'armu mai iyawane. kada ka tabar damu ga abunda muka rokeka ya Allah.


Daga: Ummu Mus'ab Khadijah

Wednesday, 14 June 2017

MUNA MATUKAR KAUNAR IMAM MALIK MUNA KUMA GIRMAMA SHI GIRMAMAWA TA SHA'RIAH:

1. Yana da kyau duk wanda ke da sauran hankali ya yi kokarin sanya ko wane al'amari cikin matsayin da ya dace a sanya shi, lalle daukar hanyar yarfe da sharri domin kaiwa ga inda ake buri da 'yan bidi'ah da sauran ma'abuta son zuciya ke yi tabbas ciniki ne mara riba, babban darasi da shaida a kan wannan shi ne: Irin yadda kafuran Quraishawa suka yi ta yi wa manzon Allah mai tsira da amincin Allah sharri da yarfe, amma kuma duk da haka burinsu bai cika ba, ba su iya suka hana sauran jama'ar duniya fahimtar gaskiyar da shi manzon Allah mai tsira da amincin Allah yake dauke da ita ba.
2. Babban abin da yake banbanta Masu Sunnah da Masu Bid'ah shi ne: in su masu Sunnah suka ce wane ya ce, to su kan kawo nassin maganarsa domin masu hankali su yanke hukunci da kansu, su kuwa Masu bidi'ah cewa kawai za su ce: wane ya ce ba ta tare da sun kawo nassin maganar tasa ba, saboda sun San cewa in har sun kawo nassin maganar to kuwa duniya za ta karyata ikirarinsu.
3. Lalle yana da kyau a san cewa ba dukkan abin da ake jinginawa zuwa ga Mazhabar Malikiyyah ba ne shi Imam Malik -Allah Ya yi masa rahama- ya fade shi da bakinsa ba, ko ya aikata shi da gabbensa ba, a'a fatawowi na mas'aloli da yawa almajiransa ne, ko almajiran almajiransa ne, ko almajiran almajiran almajiransa ne suka yi su, ba wai shi Imam Malik din ba ne ya yi su.
Haka nan yana kyau a san cewa a kan samu fatawar da za ta sha'hara ta yadda za ta zamanto ita ce mash'huriyar mazhabar Malikiyyah alhalin kuwa fatawa ce da take saba wa ainihin abin da shi Imam Malik din ya fada da bakinsa, ko ya aikata da gabbensa. Ke nan a duk lokacin da aka ce Malikiyyah sun ce kaza da kaza ba dole ba ne hakan ya zamanto ana nufin Imam Malik ne ya fadi hakan da bakinsa, ko shi ne ya aikata hakan da gabbensa.
4. Lalle yana da kyau a san cewa shi Imama Malik Bin Anas -Allah Ya yi masa rahama- daya ne daga cikin manyan Malaman Musulunci na Duniya, babu mai zaginsa sai azzalumi mai raunin imani, kuma mara mutunci, lalle dukkan mai mutunci tsakaninsa da shi Imam Malik shi ne addu'ar alheri. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya rahamce shi tare da sauran A'immah gaba daya.
5. Lalle yana da kyau a san cewa babban abin da masu da'awah ke cewa shi ne: Imam Malik ko waninsa cikin manyan Malamai babu ma'asumi a cikinsu, a'a ko wanne daga cikinsu yana iya yin kure a cikin ijtihadinsa yana kuma iya yin daidai, wannan kuma ba zagi ba ne ko raini ga su wadannan manyan Malaman a'a kara maimaita irin matsayinsu ne da tun tuni suka riga suka dauka suka kuma gaya wa duniya, kuma tabbas fadin hakan girmamawa ce a gare su ba wai zagi ba ne ko raini.
6. Lalle yana da kyau a san cewa lalle nuna naciya a kan gaya wa Musulmin duniya cewa: kada ku yi aiki da maganar Imam Malik ko waninsa matukar dai maganar ta saba wa ingantacciyar maganar manzon Allah mai tsira da amincin Allah, wannan mataki ko aiki kara isar da sakon shi kansa Imam Malik din ne, ba wai zaginsa ba ne ko nuna masa raini da kiyayya, babu mai ganin irin wannan aiki a matsayin nuna wa Imam Malik kiyayya, ko nuna masa raini sai irin mutanen nan da hankulansa suka kasa hankulan jakunan gidajensu.
7. Misalin masu da'awah cikin wannan mas'alah da misalin wadannan 'yan bidi'ah da ke musu yarfe da sharri da jumhuri kamar misalin wadanda ke gaya wa Kiristoci ne cewa: Annabi Isa alaihis Salam manzon Allah ne ba dan Allah ba ne ba kuma Allah ne ba shi; saboda haka kada ku bauta masa a'a ku bauta wa Allah Shi kadanSa, su kuma Kiristoci su rika maida martani suna cewa: Ai wannan zagi ne ake yi wa Almasihu Dan Allah, ai wannan kokari ne na rage darajar Isa Almasihu Dan Allah, su rika cewa dole ne mu ci gaba da bautar Isa Almasihu Dan Allah saboda shi ne mai cetonmu har abada. Tabbas a cikin wannan jayayyar da ke faruwa tsakanin Kiristoci da masu yin musu wa'azi lalle shi Annabi Isa alaihis Salam yana tare ne da bangaren da ke yi wa su Kiristocin wa'azi, sam ba ya tare da bangaren da ke cewa shi ne Allah ko Dan Allah mai cetonsu.
8. Lalle yau da za a ce Imam Malik zai dawo duniya to da lalle ne zai yaki dukkan wani wanda ke ajiye maganar Annabi mai tsira da amincin Allah a gefe; domin ya yi aiki da maganar shi Imam Malik wacce take saba wa ta shi Annabi mai tsira da amincin Allah; saboda Annabi mai tsira da amincin Allah ne manzon Allah shi ne wanda Allah Ya aiko domin a bauta masa a bisa koyawar shi Annabin, ba wai a bisa koyawar waninsa ba sawaa'un ya kasance Imam Malik ne ko waninsa. Kuma shi ma Imam Malik burinsa har kullum a lokacin rayuwarsa shi ne ya yi Musuluncinsa kamar yadda Annabi mai tsira da amincin Allah yake yi, ba wai ya yi gasa da shi Annabi mai tsira da amincin Allah ba.
Allah muke roko Ya taimake mu Ya cusa wa al'ummarmu soyayyar ManzonSa mai tsira da amincin Allah cikin zukatansu, Ya kuma cusa musu son yin aiki da ingantattun hadithansa cikin wadannan zukata nasu. Ameen.

Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

Tuesday, 13 June 2017

SANARWA DA GAYYATA LACCAR MATA NA AZUMI SHIYYAR KATSINA.

Assalamu Alaikum

Da sunan Allah mabuwayi Wanda ya shiryar da hanyar tsira ga diyan Adam da aiko farin jakada Annabi Muhammad S.A.W da Alkur'anin da kuskure baya zuwa gareshi ta gabansa da bayansa. Allah kayi dadin tsira  da aminci ga Annabi Muhammad S.A.W da Alayensa da sahabbansa zababbu wadanda suka yada wannan addini da dukiyoyinsu da rayukansu.

Bayan haka bisa umurnin da kungiyar JIBWIS ta Kasa ta bayar na a gabatar da laccoci ga mata lokacin wannan wata na ramadhan 1438. An shirya gabatar da lacca ta shiyyar Katsina kamar haka:

RANA : ASABAT 22/RAMADHAN, 1438 AH (17/6/2017)

WURI :  MASALLACIN JUMA'A NA KOFAR KAURA KANDAHAR

LOKACI :  9:30 NA SAFE

MAUDU'AI : 
- AHLUL BAIT A WAJEN AHLUL SUNNAH  (USTAZ SAFIYYU ALKASIM SAULAWA)

- MARAYA DA WAJIBCIN TALLAFA MASA.
(Ustaz Murtadha Daura).

Muna fatan zaku bayar da  hadin kai domin nasarar wannan shiri, muna addu'a ga Allah SWT ya amsa mana ibadarmu ya aza ayyukanmu a bisa mizanin ayyukan alkhairi amin.


Sanarwa:
Nabeelatu D Aleeyu
Asst. Secretary Women in Da'awa Katsina.

Monday, 12 June 2017

KADDAMAR DA KWAMITIN TALLAFAWA MARAYU DA GAJIYAYYU A MASALLACIN KANDAHAR, MAJLISIN SHEIKH YAKUBU MUSA HASSAN 1438/2017.


A JIYA LAHADI NE SHUGABAN KWAMITIN TAFSIRI NA JIBWIS A MATAKIN KASA, KUMA SHUGABAN

KWAMITIN DA'AWA NA KASA SANNAN SHUGABAN KUNGIYAR JIBWIS NA JIHAR KATSINA KUMA

NATIONAL TRUSTEE NA JIBWIS A MATAKIN KASA AS SHEIKH YAKUBU MUSA HASSAN KATSINA YA

BUDE GIDAUNIYAR TALLAFAWA MARAYU DA GAJIYAYYU A LOKACIN AZUMIN WANNAN SHEKARA DON

SANYAYA ZUCIYAR MARAYUNMU DA GAJIYAYYUNMU SUMA SU SAMU WALWALA KAMAR YADDA

KOWA YAKE SAMU A IRIN WANNAN LOKACI.

SHEIKH YAJA HANKALIN AL'UMMA MUSAMMAN MASU HANNU DA SHUNI AKAN TALLAFAWA

WANNAN ASUSU, WANDA BABU MAMAKI SHEKARA MAI ZUWA MUMA NAMU YARAN SU SHIGA CIKIN

WADANDA ZASU NEMI WANNAN TALLAFIN. SHEIKH YA KARANTO AYOYIN AL'KUR-ANI TARE DA

TAIMAKON ALHAAFIZ USMAN ABUBAKAR BIRNIN KEBBI DOMIN KARFAFA HUJJARSA DA MADOGARAR

SHI BISA DORON NASSI.

A LOKACIN BUDE WANNAN GIDAUNIYA WADDA KUNGIYAR JIBWIS TA JIHA TA JAGORANTA, KUNGIYAR

TA BUDE ASUSUN DA BADA GUDUMMUWAR KUDI HAR N800,000. GA MARAYU SAI KUMA N200,000 GA

GAJIYAYYU. A INDA GWAMNAN JIHAR KATSINA ALH. AMINU BELLO MASARI YA AIKO DA TASHI

GUDUMMUWAR TA KASHIN KANSHI HAR N500,000. WANI BAWAN ALLAH KUMA YA AIKO DA N250,000.

SANNAN ABUN BAN SHA'AWA A WANNAN SHEKARAR KUMA SHINE, HADIMAN KUNGIYAR MASU

GUDANAR DA AIKACE AIKACEN KUNGIYAR NA YAU DA KULLUN SUN JAGORANCHI BADA WANNAN

GUDUMMUWA DON AMSA KIRA DA MUBAYI'A AKAN AYOYI DA HADISAN DAKE KWADAITARWA AKAN

IRIN WANNAN AIKI MAI TARIN ALBARKA TUN KAFIN KADDAMAR DA WANNAN GIADUNIYA, INDA TUN

DAGA SHUGABAN MEDIA KWAMITI NA JIHA ZUWA ADMIN SECRETARY NA JIBWIS DA'AWA COMMITTEE

HAR ZUWA GA ALFAAFIZ USMAN BIRNIN KEBBI SUKAYI RUWAN KUDADE MASU KWARI DON NEMAN

ALBARKAR CIYAR DA MARAYU.

A KARSHEN WANNAN GIDAUNIYA TA YAU,  AN SAMU TARA KUDI SAMA DA MILYAN 2, MUNA ADDU'A

ALLAH YA SAKAWA KOWA DA ALKHAIRI, KUMA KOFA A BUDE TAKE GA DUK MASU NIYYAR

TALLAFAWA WANNAN GIDAUNIYA TA MARAYU MUSAMMAN MASU HANNU DA SHUNI, YAN KASUWA

MANYA DA KANANA, ZABABBUN WAKILLAN JAMA'A A MATAKIN JIHA DA KASA, MASU RIKE DA

MADAFUN IKO,  DA DUK MASU KWADAYI DA NEMAN ALBARKA A IRIN WANNAN AIKI MAI TARIN

ALBARKA.

Muhammad Jameel Maharaz
Chairman JIBWIS Social Media Committee
Katsina state, Nigeria.
17th Ramadan,  1438
12th June, 2017

Saturday, 10 June 2017

RAMADAN TAFSEER DAGA MASALLATAN GARIN FUNTUA MP3 1438/2017.

RAMADAN TAFSEER DAGA MASALLATAN GARIN FUNTUA MP3 1438/2017.

1. BABBAN MASALLACIN JIBWIS (ZARIA ROAD) FUNTUA.
Mai Gabatarwa: Imam Saeedu Musa Funtua.
002 IMAM SAEED MUSA FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22648
14.2 MB 1:01:01

003 IMAM SAEED MUSA FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22650
13.9 MB59:39

004 IMAM SAEED MUSA FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22649
2.8 MB11:17

005 IMAM SAEED MUSA FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22651
14 MB1:00:12

006 IMAM SAEED MUSA FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22652
13.4 MB57:44

008 IMAM SAEED MUSA FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22654
12.6 MB53:58

009 IMAM SAEED MUSA FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22655
15.3 MB1:05:44

010 IMAM SAEED MUSA FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22656
16.1 MB1:09:26

011 IMAM SAEED MUSA FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22657
15.8 MB1:08:09

012 IMAM SAEED MUSA FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22658
12.9 MB55:31

2. MASALLACIN GARBA TASHA (DUTSEN-REME) FUNTUA.
Mai Gabatarwa: Imam Salisu Idris
001 IMAM SALISU IDRIS FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22593
4.9 MB1:21:27

003 IMAM SALISU IDRIS FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22595
10 MB1:25:47

004 IMAM SALISU IDRIS FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22607
10.9 MB1:33:18

005 IMAM SALISU IDRIS FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22617
9.8 MB1:23:58

006 IMAM SALISU IDRIS FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22618
10.9 MB1:33:29

007 IMAM SALISU IDRIS FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22619
6.6 MB56:14

008 IMAM SALISU IDRIS FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22620
9.5 MB1:21:34

009 IMAM SALISU IDRIS FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017M
http://darulfikr.com/s/22616
1.1 MB7:53

3. MASALLACIN JAMI'U HAJARAT PLAZA (KWANAR JAGWA) FUNTUA
Mai Gabatarwa: *Imam Nasir Abdurrahman.*

4. MASALLACIN ALH. BABANGIDA JARGABA (DUTSEN-REME)
Mai Gabatarwa: Ustaz Abubakar Saeed.
001 USTAZ AUBAKAR SAEED RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/21434
5.6 MB46:51

002 USTAZ AUBAKAR SAEED RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22621
6.1 MB51:22

004 USTAZ AUBAKAR SAEED RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22624
7.7 MB1:05:43

005 USTAZ AUBAKAR SAEED RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22625
5.5 MB45:59

006 USTAZ AUBAKAR SAEED RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22626
4.9 MB41:12

007 USTAZ AUBAKAR SAEED RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22627
5.3 MB44:13

008 USTAZ AUBAKAR SAEED RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22628
5.6 MB47:22

009 USTAZ AUBAKAR SAEED RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22629
5.6 MB47:33

010 USTAZ AUBAKAR SAEED RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22631
5.9 MB 50:00

5. MASALLACIN DAN DUTSE
Mai Gabatarwa: Malam Muhammad Sulaiman.
001 MLM MUHD SULAIMAN FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22635
8.2 MB1:09:30

002 MLM MUHD SULAIMAN FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22636
8.4 MB1:11:49

003 MLM MUHD SULAIMAN FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22637
8.2 MB1:09:59

004 MLM MUHD SULAIMAN FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22638
7.2 MB1:01:33

005 MLM MUHD SULAIMAN FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22639
7.5 MB1:03:29

006 MLM MUHD SULAIMAN FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22640
7 MB59:04

007 MLM MUHD SULAIMAN FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22641
9.5 MB1:20:51

008 MLM MUHD SULAIMAN FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22642
6.9 MB58:45

009 MLM MUHD SULAIMAN FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22643
8.6 MB1:12:58

010 MLM MUHD SULAIMAN FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22644
6.6 MB55:41

011 MLM MUHD SULAIMAN FUNTUA RAMADAN TAFSEER 2017
http://darulfikr.com/s/22646
7.3 MB 1:02:16

6. MASALLACIN OFISHIN QUNGIYA (JIBWIS)
Mai Gabatarwa: Imam Nasir Abdurrahman.
Rad38 Rum 1-7 Abu Khalil Funtua
http://darulfikr.com/s/21898
8.2 MB1:10:03

Rad38 Rum17-21 Abu Khalil Funtua
http://darulfikr.com/s/21900
8.1 MB1:09:02

Rad38 Rum8-16 Abu Khalil Funtua
http://darulfikr.com/s/21899
6.7 MB56:59

Rad38 Rum8-16 Abu Khalil Funtua
http://darulfikr.com/s/21901

Ayi sauraro lafiya.

© JIBWIS Social Media Katsina State.
Facebook.com/Jibwsktn
http://JibwisKatsina.blogspot.com

http://darulfikr.com/s/22648


Via FB Pages Manager For Windows Phone