A yaune kwamitin tallafawa marayu da ke masallacin *jibwis* na sheikh *Abbas jega* dake anguwar rafin atiku a nan cikin garin Birninkebbi suka tallafawa marayu dubu daya da dari biyu da hamsin da biyu (1,252.00) a wuraren da suka tsara a nan cikin garin Birninkebbi,
Shugaban kwamitin Alhaji *Abdullahi Gebe* ne ya sanar da hakan a lokacin da manema labarai suka ziyarci wurin da ake bayar da tallafin da safiyar yau,
Haka shima Uban Doman Gwandu Alhaji *Khalidu Sa'ad,* yayi kira ga gwamnati, yan kasuwa, yan siyasa da kuma Ma'aikata da su bada goyon bayan su ga wannan shirin da kungiyar izala ta kasa ta kirkiro tun shekaru da suka gabata domin tallafin yanada alfano matuka,
Anashi bayanin daga bisani,shugaban kwamitin, Alhaji *Abdullahi Gebe Argungu* ya yi matukar godiya amadadin kwamitin baki daya, ga duk ilahirin wadanda suka bada nasu tallafin domin wannan shirin ya ci nassara, Musamman shugaban masu rinjaye a majalisar jaha watau Hon. *Bello Rilisco* akan bada tallafi mafi tsoka a kowace shekara,
Allah ya sa ka wa kowa da alkhairi,
*Adamu Attahiru*
Jibwis social media
26/09/1438
21/06/2017
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve