Wednesday, 21 June 2017

KMAMITIN TAFSIRI NA KASA YAKAI ZIYARA GA SHEIKH ABBAS JEGA


Cikin ikon Allah min samu ziyartar Tafsirin dare na Sheikh Abbas Muhammad Jega, Madugu uban tafiya, kuma jagoran tafiyar Sunnah a Jihar kebbi a Jiya Talata 20th June, 2017 wanda yayi muwafaqa da 25 ga Ramadan 1438 wanda yake gabatarwa a garin Jega da dare.

Bayan isar da jawabin godiya da fatan Alkhairi ga Shehin Malamin tare da Al'ummar Musulmin Jihar kebbi daga bakin Shugaban Kwamitin Tafsiri na Kasa, anyi amfani da wannan dama domin gabatar da Addu'o'i na musamman ga al'ummar musulmi mudamman wadanda duke cikin tsangwama da damuwa, sannan ga kasarmu Nigeria musamman Babban Kwamanda kuma Madugu Uban tafiya Mal. Alh. Dr. Gen Muhammadu Buhari (hafizahullah wa ra'ah) kan Allah ya bashi cikakkiyar lafiya Don cigaba da aikin Alheri wanda ya faro na yin gyara ga yanayin da kasarmu ta samu kanta a ciki. ALLAH YA MAIDOSHI GAREMU LAFIYA.

Shehin Malamin yayi Addu'a ta musamman ga Matasa akan Allah ya kebo hankalinsu Don tsayuwa akan addini da kyakkyawar dabi'a, sannan yayi addu'a gamammiya ga al'ummah Don ganin an samu ingantaccen yanayi musamman abunda ya shabi tsaro, tattalin arziki, Damina mai albarka don samun isasdhen abinci a kasa

Sheikh Abbas Muhammad Jega yana gabatar da tafsir har say 3 a kowacce rana tare da Alaramma Ridwan Muhammad Kaduna wanda kwamitin Tafsiri na Kasa ya turo Don yin wannan aiki tare da sheikh a garin Jega da Birnin kebbi. Allah ya sanya wannan aiki a mizanin Hasanaat, ya Karawa rayuwa albarka

Muhammad Jameel Maharaz
Sakataren Kwamitin Tafsiri na Kasa
JIBWIS NIGERIA
26th Ramadan, 1438
21st June, 2017

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve