Tuesday, 13 June 2017

SANARWA DA GAYYATA LACCAR MATA NA AZUMI SHIYYAR KATSINA.

Assalamu Alaikum

Da sunan Allah mabuwayi Wanda ya shiryar da hanyar tsira ga diyan Adam da aiko farin jakada Annabi Muhammad S.A.W da Alkur'anin da kuskure baya zuwa gareshi ta gabansa da bayansa. Allah kayi dadin tsira  da aminci ga Annabi Muhammad S.A.W da Alayensa da sahabbansa zababbu wadanda suka yada wannan addini da dukiyoyinsu da rayukansu.

Bayan haka bisa umurnin da kungiyar JIBWIS ta Kasa ta bayar na a gabatar da laccoci ga mata lokacin wannan wata na ramadhan 1438. An shirya gabatar da lacca ta shiyyar Katsina kamar haka:

RANA : ASABAT 22/RAMADHAN, 1438 AH (17/6/2017)

WURI :  MASALLACIN JUMA'A NA KOFAR KAURA KANDAHAR

LOKACI :  9:30 NA SAFE

MAUDU'AI : 
- AHLUL BAIT A WAJEN AHLUL SUNNAH  (USTAZ SAFIYYU ALKASIM SAULAWA)

- MARAYA DA WAJIBCIN TALLAFA MASA.
(Ustaz Murtadha Daura).

Muna fatan zaku bayar da  hadin kai domin nasarar wannan shiri, muna addu'a ga Allah SWT ya amsa mana ibadarmu ya aza ayyukanmu a bisa mizanin ayyukan alkhairi amin.


Sanarwa:
Nabeelatu D Aleeyu
Asst. Secretary Women in Da'awa Katsina.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve