Wednesday, 14 June 2017

MUNA MATUKAR KAUNAR IMAM MALIK MUNA KUMA GIRMAMA SHI GIRMAMAWA TA SHA'RIAH:

1. Yana da kyau duk wanda ke da sauran hankali ya yi kokarin sanya ko wane al'amari cikin matsayin da ya dace a sanya shi, lalle daukar hanyar yarfe da sharri domin kaiwa ga inda ake buri da 'yan bidi'ah da sauran ma'abuta son zuciya ke yi tabbas ciniki ne mara riba, babban darasi da shaida a kan wannan shi ne: Irin yadda kafuran Quraishawa suka yi ta yi wa manzon Allah mai tsira da amincin Allah sharri da yarfe, amma kuma duk da haka burinsu bai cika ba, ba su iya suka hana sauran jama'ar duniya fahimtar gaskiyar da shi manzon Allah mai tsira da amincin Allah yake dauke da ita ba.
2. Babban abin da yake banbanta Masu Sunnah da Masu Bid'ah shi ne: in su masu Sunnah suka ce wane ya ce, to su kan kawo nassin maganarsa domin masu hankali su yanke hukunci da kansu, su kuwa Masu bidi'ah cewa kawai za su ce: wane ya ce ba ta tare da sun kawo nassin maganar tasa ba, saboda sun San cewa in har sun kawo nassin maganar to kuwa duniya za ta karyata ikirarinsu.
3. Lalle yana da kyau a san cewa ba dukkan abin da ake jinginawa zuwa ga Mazhabar Malikiyyah ba ne shi Imam Malik -Allah Ya yi masa rahama- ya fade shi da bakinsa ba, ko ya aikata shi da gabbensa ba, a'a fatawowi na mas'aloli da yawa almajiransa ne, ko almajiran almajiransa ne, ko almajiran almajiran almajiransa ne suka yi su, ba wai shi Imam Malik din ba ne ya yi su.
Haka nan yana kyau a san cewa a kan samu fatawar da za ta sha'hara ta yadda za ta zamanto ita ce mash'huriyar mazhabar Malikiyyah alhalin kuwa fatawa ce da take saba wa ainihin abin da shi Imam Malik din ya fada da bakinsa, ko ya aikata da gabbensa. Ke nan a duk lokacin da aka ce Malikiyyah sun ce kaza da kaza ba dole ba ne hakan ya zamanto ana nufin Imam Malik ne ya fadi hakan da bakinsa, ko shi ne ya aikata hakan da gabbensa.
4. Lalle yana da kyau a san cewa shi Imama Malik Bin Anas -Allah Ya yi masa rahama- daya ne daga cikin manyan Malaman Musulunci na Duniya, babu mai zaginsa sai azzalumi mai raunin imani, kuma mara mutunci, lalle dukkan mai mutunci tsakaninsa da shi Imam Malik shi ne addu'ar alheri. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya rahamce shi tare da sauran A'immah gaba daya.
5. Lalle yana da kyau a san cewa babban abin da masu da'awah ke cewa shi ne: Imam Malik ko waninsa cikin manyan Malamai babu ma'asumi a cikinsu, a'a ko wanne daga cikinsu yana iya yin kure a cikin ijtihadinsa yana kuma iya yin daidai, wannan kuma ba zagi ba ne ko raini ga su wadannan manyan Malaman a'a kara maimaita irin matsayinsu ne da tun tuni suka riga suka dauka suka kuma gaya wa duniya, kuma tabbas fadin hakan girmamawa ce a gare su ba wai zagi ba ne ko raini.
6. Lalle yana da kyau a san cewa lalle nuna naciya a kan gaya wa Musulmin duniya cewa: kada ku yi aiki da maganar Imam Malik ko waninsa matukar dai maganar ta saba wa ingantacciyar maganar manzon Allah mai tsira da amincin Allah, wannan mataki ko aiki kara isar da sakon shi kansa Imam Malik din ne, ba wai zaginsa ba ne ko nuna masa raini da kiyayya, babu mai ganin irin wannan aiki a matsayin nuna wa Imam Malik kiyayya, ko nuna masa raini sai irin mutanen nan da hankulansa suka kasa hankulan jakunan gidajensu.
7. Misalin masu da'awah cikin wannan mas'alah da misalin wadannan 'yan bidi'ah da ke musu yarfe da sharri da jumhuri kamar misalin wadanda ke gaya wa Kiristoci ne cewa: Annabi Isa alaihis Salam manzon Allah ne ba dan Allah ba ne ba kuma Allah ne ba shi; saboda haka kada ku bauta masa a'a ku bauta wa Allah Shi kadanSa, su kuma Kiristoci su rika maida martani suna cewa: Ai wannan zagi ne ake yi wa Almasihu Dan Allah, ai wannan kokari ne na rage darajar Isa Almasihu Dan Allah, su rika cewa dole ne mu ci gaba da bautar Isa Almasihu Dan Allah saboda shi ne mai cetonmu har abada. Tabbas a cikin wannan jayayyar da ke faruwa tsakanin Kiristoci da masu yin musu wa'azi lalle shi Annabi Isa alaihis Salam yana tare ne da bangaren da ke yi wa su Kiristocin wa'azi, sam ba ya tare da bangaren da ke cewa shi ne Allah ko Dan Allah mai cetonsu.
8. Lalle yau da za a ce Imam Malik zai dawo duniya to da lalle ne zai yaki dukkan wani wanda ke ajiye maganar Annabi mai tsira da amincin Allah a gefe; domin ya yi aiki da maganar shi Imam Malik wacce take saba wa ta shi Annabi mai tsira da amincin Allah; saboda Annabi mai tsira da amincin Allah ne manzon Allah shi ne wanda Allah Ya aiko domin a bauta masa a bisa koyawar shi Annabin, ba wai a bisa koyawar waninsa ba sawaa'un ya kasance Imam Malik ne ko waninsa. Kuma shi ma Imam Malik burinsa har kullum a lokacin rayuwarsa shi ne ya yi Musuluncinsa kamar yadda Annabi mai tsira da amincin Allah yake yi, ba wai ya yi gasa da shi Annabi mai tsira da amincin Allah ba.
Allah muke roko Ya taimake mu Ya cusa wa al'ummarmu soyayyar ManzonSa mai tsira da amincin Allah cikin zukatansu, Ya kuma cusa musu son yin aiki da ingantattun hadithansa cikin wadannan zukata nasu. Ameen.

Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve