Thursday, 15 June 2017

GOMAN KARSHE!!!



Wanda ya riski ramadan harya fita ba'a gafarta masaba hakika rabo me girma ya kubuce masa. dukkan Alkhairi yayi nisa dashi, ko wace irin asara ta sameshi, kaico! wananna raunanannan bawa yayi asara.

Ya tsawaita kukansa da nadamarsa da bakin cikinsa, wanda ya riski goman 10 karshe na ramadan amma bai sadar da dararenshi da nafila ba, bai jiyar da kanshi dadi da karatun alqur'ani ba, be haskaka gidansa da Zance mafi dadiba.

Bai rayar da masallatansu da sauraran wa'azi ba, hakika yayi tasgwaro a rayuwarsa, an hana masa zakin imani, an hana masa dandanon koyi da Annabin rahma.

(S A W ); Bai ci gajiyar da bayin Allah ke samu ba, shi manzon Allah idan goman karshe ta shigo yana kara nunka aiyukansa.

Ance yafi iska yawan alkhairi, ba'a taba samun wanda yakai kyautar manzon Allah ba ,Amma idan goman 10 karshe tazo yana rubanya aiyukansa.

Yakasance kullum mala'ika jibrilu (AS) yana zuwa gareshi kullum sunayin karatun alqur'ani mai girma, madalla da wananna malami jibrilu,

Madallah da wanda ake Koyawa manzon Allah, Madallah da wananna majalisi mai girma.

A goman 10 karshene manzon Allah ( S A W ) yakan nade shinfidarsa ta barci, yakan kauracewa hutawarsa, yakan nade kafafun wandonsa zuwa sama wato ma'ana yakan daga yayi dammara ta tada iyalansa, dan suma su rusku cikin alkhairi

Saboda ganawarsa da mamallakin al'amura baki daya.

Cikin wadannan dararene masu albarka ake haduwa da dukkan nufi, ake kaiwa ga dukkan manufa, da dukkan biyan bukata.

A irin wadanan lokutane Allah ta'ala yake bayyana ga bayinsa da mafi nunkuwar lada, da mafi gwabin gafararsa, da tabbatacciyar afuwarsa da yafiya ga bayinsa nagari.

A kowace sa'a a kowane dare na ramadan Allah ( S W T) yana yanta mutum Dubu dari ya tabbatar musu baza ayi musu azaba ba.

A daren Karshen ramadan Allah Yana yantawa ninkin haka Bayan kowace dakika da kowace awa, da kowace kibtawa, lallai Allah mabuwayine.

Mai gafarane, mai iko ne, ba'a tuhumarsa ga dukkan abinda yayi.

shine mafificin masu jin kai.

Allah ta'ala yana cewa : ku kirayi ubangijinku Allah kuna masu rokonsa da takawa da tausasawa shi baya son masu shishigi, kada ku rika barna a bayan kasa.

Bayan an gyarata, ku rokeshi kuna masu jin tsoronsa tare da kwadayin rahamarsa, lallai rahamar Allah kusa take ga masu kyautatawa.

idan ya zama Allah Yana gafartawa masu laifuffuka har yawan wananna adadi, to yayi zai zama ga bayinsa na kirki masu jin kunyar sabonsa.

Aljannah ce makomarsu wadda korama ke suna gudana a cikinta, wata irin matsaya ta gaskiya nan ga mamallakin mai tsananin iko madalla da masu azumi suna kiyayewa.

suna masu alkhairi da gasgatawa, suna tsayawa suna tabbatuwa, suna yawan tuba farkon safiya, suna masu konkomawa da maraicensu. 
Madallah da wadannan matane da Babu kamarsu.

Kayima kanka hisabi ya bawan Allah yakai dan'uwana, a Karshen ramadan gabanin Allah yayima ka.

Kaduba takardun ayyukanka daka aikata, Meka gudanar a ramadan?

Shin Dame zaka tsira sa'adda kake karanta littafin aiyukanka ranar kiyama gaban Allah da mala'ikunsa ga Annabawa da Manzanni, da iyayenka, da matanka. da surukanka, ga abokanka sun hallara, da malamanka, da sauran jama'a. kowa yayi tsit kai ake sauraro?

Kayi nazari ka gani meya gudana gareka na sallah, da azumi , da biyayya ko ciyarwa, kyautatawa ko sadaka.

Tausayi ko daidaitawa tsakanin talakawa, rangwame ko yafewa?

Himmarka cikin bin Allah ko takaitawarka ga saba mishi.

Kayi kokarin cike gurbin abunda ka rasa na ayyukanka.

To ka rika tashi a lokatun da ake ganawa da Allah a Karshen kowane dare da bayan kowane sallar farilla don neman sulhu.

Ya Allah, mu mun zalunci kawunanmu zalinci mai yawa idan har baka gafarta mana ba, kuma baka jikanmu ba, hakika lallai zamu kasance daga cikin wadanda suka yi asara.

Ya Allah ka gafarta mana dukkan kura-kuranmu ka yafe mana zunubanmu ,ka daidaita imani a zukatanmu ka karbi ayyukanmu, ka yantar da mu da iyayenmu da ya'yanmu da yan'uwanmu, daga barin wuta kasanya jannatul firdausi ta zama makoma garemu, tare da dukkan musulmi baki daya.

Kai mai iko ne akan komai wajen karba mana addu'armu mai iyawane. kada ka tabar damu ga abunda muka rokeka ya Allah.


Daga: Ummu Mus'ab Khadijah

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve