Tuesday, 14 November 2017

*FITOWA TA 22
*Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com

      MATAKIN DAYANTAKAR SAMUWA

         Wannan mataki ba shi da bambanci sosai da matakin yaye hijabi.A hakika ma shi ciko ne gare shi,ko kuma dori  a kan gininsa.
          Sufaye a wannan mataki suna bincike game da halitta baki daya,da kuma yadda halitta ta samu daga mahalicci.Wannan bincike da suke yin sa ta hanyar nazari da tunani a bisa kaidojin falsafar Girkawa da mazhabobinta,ya kai su ga daukar cewa dukkanin halitta,a hakika,ba kome ba ce sai zato da tsammani,ko kuma hoto ce kawai,kamar yadda ake fadi da Hausar zamani.suka ce halittu duka ba kome ba ne a hakika,kuma ba su da samuwa,abinda ya sa kawai muke riya samuwarsu shi ne GANIYA,ko kuma fahimta,wacce muke rarrabe samuwar tasu da ita.Idan da za mu rasa Wannan GANIYA ko fahimta,ta hanyar rasa hanyoyin koyo guda biyar da muke da su,to da sai mu tabbatar da rashin halitta.Sun ba da misali da cewa,dukkan abubuwan da ake gani da ido ba su da samuwa a wajen makaho,haka nan abubuwan da ake ji da kunne ba su da samuwa a wajen kurma,haka nan abubuwan da ake ji a jika,ko ake shafar su,ba su da samuwa a wajen wanda ya rasa ni'imar shafa.

Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 23 Insha Allah.

Abu Aisha journalist.
Jibwis Social Media Katsina.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve