Thursday, 26 October 2017

*FITOWA TA 5.
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA SAHABBAI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A NA 2.
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com

Yan Shi'a suna nuna kiyayya ta musamman ga sarkin Musulmi Umar
binul Khaddabi(R.A).Daga cikin ruwayoyin da suka kebe masa shi kadai
akwai abinda wani malaminsu mai suna Ni'imatullahi Aljaza'iri ya
ruwaito.Ya ce, "Abinda yake daure kai shi ne,yaya Ali(A.S) ya aurawa
Umar binul khaddabi(diyarsa)Ummu kulthum,alhali kuwa miyagun ayyuka
sun bayyana daga gare shi kuma ya yi ridda ga barin addini sama da
riddar duk wani mai ridda.Har ma ruwayoyi sun taho da cewa (ranar
Alkiyama)za'a yiwa shaidan kukumi da sasari saba'in na bakin karfen
Jahannama sa'annan a ja shi zuwa ga taron hasabi.Sai ya duba
gabansa,sai ya ga wani mutum mala'ikun azaba suna kora shi,an kukume
shi da sasari dari da ishirin na Jahannama.Sai shaidan ya kusanto shi
ya ce:Me mara rabo ya yi har ya FI ni azaba, alhali ni na batar da
halitta baki daya,na kai su ga halaka? Sai Umar ya ce da shaidan :Ba
abinda na yi sai dai na kwace wa Ali binu Abi Dalib khilafa.Ga alama
yana ganin kankantar abinda ya aikata;bai sani ba cewa duk abinda ya
faru a duniya na kafirci da zalunci,ya auku ne a dalilin wannan
aika-aika ta sa."

Duba ka gani,dan uwa mai karatu,yadda yan Shi'a suke daukar cewa wai
Umar(R.A) ya FI shaidan tsakanin azaba a Lahira,kuma duk abinda ya
faru a duniya na kafirci da zalunci a dalilinsa ne!!.

Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 6 Insha Allah.

Abu Aisha journalist.
Jibwis Social Media Katsina.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve