Wednesday, 11 October 2017

*FITOWA TA 19.
*Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com

Babban abinda shagaltar da zukatan Sufaye a wannan mataki shi
ne sani,ko kuma yadda za'a san hakikanin abubuwa wadanda suka hada da
sanin Allah Madaukaki da siffofinsa da kuma halittunsa.Wannan shi ne
abinda suke kira ma'arifa.
Sufaye sun ba wa sani,musamman sanin Ubangiji,muhimmanci
babba inda suka ce shi ne manufa ta farko kuma mafi daukaka a rayuwar
ko wane mutum.Sun gina wannan ra'ayi nasu a kan wani hadisi kudusi da
suke ruwaitowa wanda a cikinsa Allah Madaukaki yake cewa bisa harshen
Manzonsa (S.A.W), "Na kasance taska boyayya sai na so a san ni,sai na
halicci halittu don su san ni." Suka ce sanin Allah shi ne ya fi kome
muhimmanci a rayuwa, domin sai an san shi ne za'a bauta masa yadda ya
kamata.Bayan sun tabbatar da wannan ra'ayi, sai suka tambayi kansu:Ta
wace hanya za mu iya sanin Ubangiji?
Amsar da Sufaye suka hadu a kanta ita ce,babu wata hanya
da ta dace a san Allah da ita sai hanyar zuciya.Suka ce ko wace zuciya
ta bil Adama tana iya ganin hakika, kuma mai ita yana iya sanin Allah
ta hanyarta,sai fa idan an sami wani dalili wanda zai hana ita zuciyar
yin haka.Dalilan da suke hana zuciya ganin hakika guda biyar
ne:..........
..

Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 20 Insha Allah.

Abu Aisha journalist.
Jibwis Social Media Katsina.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve