*FITOWA TA 3.
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA SAHABBAI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A NA 2.
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
Amma mene ne dalilin wanan tsatssauran hukunci akan zababbun
halitta bayan Annabawa da Manzanni? Mene ne dalilin da ya sa yan Shi'a
suke kafirta Sahabbai? Dalilan guda biyu ne rak,ba dadi ba ragi.Na
daya shi ne fadinsu cewa wai Manzon Allah (S.A.W) ya yi wasiyya cewa
Ali binu Abi Dalib (R.A)ne zai zama khalifa a bayansa amma sai
Sahabbai suka ki kemadagas su zartar da wannan wasiyya.Maimakon haka
sai suka nada Abubakar ya zama khalifa kuma daga bayansa suka nada
Umar da Usman.Sai a karo na hudu ne aka baiwa Ali(R.A) wannan matsayi.
Dalili na biyu,a lokacin da fitina ta taso a tsakanin
al'umma sakamakon kisan gilla da aka yi wa sarkin Musulmi Usman
(R.A),yaki ya auku a tsakanin Sarkin Musulmi Ali(R.A) da jama'arsa a
hannu guda da kuma Dalha da Zubair da Aisha, Allah ya yarda dasu ,tare
da magoya bayansu a daya hannun.Yan Shi'a suna ganin wadannan Sahabbai
sun yaki Ali(R.A) a bisa zalunci.To da wadannan dalilai biyu ne yan
Shi'a suke kafirta Sahabbai: hana Ali(R.A) khilafa a farkon rasuwar
Annabi (S.A.W) da kuma yaki da shi a zamanin khalifancinsa.[Duba
AWA'ILUL MAKALAT,45 da AL'ANWARUL NU'UMANIYYA,2/244].
Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 4 Insha Allah.
Abu Aisha journalist.
Jibwis Social Media Katsina.
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve