*FITOWA TA 18.
*Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
MATAKIN YAYE HIJABI
Sufanci ya ci gaba da yaduwa daga matakinsa na farko,yana
habaka,yana hadiye kuma yana mamaye dukkan tunane-tunane,falsafofi da
ra'ayoyin da ya gamu da su a bisa hanyarsa har ya kai mataki na
biyu.Wannan shi ne matakin yaye hijabi,ko kuma abinda ake kira
kashafi.
Wani muhimmin abin lura a nan shi ne,Sufanci ya zama a
koda yaushe yana dada kasaita yana kara nisa da hukunce-hukuncen
Musulunci da mabubbugar shari'a ingantacciya.Wannan kuwa ya faru ne
Saboda Sufanci ya zama juji da ake jibge duk wasu
tunane-tunane,falsafofi da ra'ayoyi na sabbin Musulmi wadanda
Musulunci ya shiga kasashensu daga baya,da kuma tsoffin addininsu
wadanda Musulunci ya kawar da su.
Wani abu da ya kara taimaka wa wannan shi ne fadi da tafarkin
Sufanci ke da shi,da kuma imanin sufaye cewa akwai wani ilmi na
boye,ko kuma ilmi ladunni,wanda mutum ba ya koyar sa,sai dai kurum ya
ji shi a zuciyarsa.Ta hanyar wannan ilmi ne abubuwa da dama,wadanda
suka saba wa addini,suka samu shiga Musulunci da rigar Sufanci. Duk
wani malami Wanda ya karanto wata falsafa,ko ya koyo wani ra'ayi ko
wata tsurfa da soki-burutsu,sai kurum ya shigo da shi cikin Sufanci ya
ce ilmin boye ne,jin sa ya yi a zuci ba koyarsa ya yi ba! Ta haka suka
cika Sufanci makil da bakin tunane-tunane, ra'ayoyi da falsafofi
wadanda suke bare ne su ga addinin Musulunci.Wadannan abubuwa sun
dauke hankalin Sufaye, suka shagaltar da zukatansu da kwakwalensu,a
yayin da suka juyo da himmarsu gaba daya zuwa gare su,suka yi ta
tattauna su,suna wallafa littafai a kan su,sai ka ce su kadai su ne
Sufanci din.
A takaice dai,kafin sufanci ya gama bada karfinsa a wannan
mataki na biyu,ya cika makil da wadannan abubuwa da muka ambata,watau
bakin tunane-tunane,ra'ayoyi da falsafofi da kuma gyauron tsoffin
addinai wadanda sabbin Musulmi suka shigo da su ta hanyar ilmi
ladunni.Don haka,SAI SUFANCI YA TASHI DAGA AIKI YA KOMA TUNANI.Sai aka
wayi gari Sufaye ba su damu ainun da yawan ibadako gudun duniya
ba,abinda suka shagala da shi shi ne,tunani kan wadannan falsafofi,
tattauna su da fadada su.
Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 19 Insha Allah.
Abu Aisha Journalist.
Jibwis Social Media Katsina.
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve