Wednesday, 4 October 2017

*FITOWA TA 17
*Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com

Akwai kuma wadanda suka bar neman ilmi don su shagala da
ibada,tare da cewa bautar Allah ba ta inganta da jahilci.Wasu kuma
suka haramta abinda Allah ya halatta na abubuwan rayuwa dadada.Suka ki
aure,suka bar shan mai da cin nama da kayan marmari da sauran abubuwa
wadanda suke halal a Musulunci, wai duk don takawa da gudun duniya.
A karshe mun ji abinda Rabi'ah Al'adawiya take fadi cewa ita
tana bauta wa Ubangiji ba don tsoron wutarsa ko kwadayin aljannarsa
ba.Wannan irin bauta Musulunci bai san ta ba domin,kamar yadda ya zo a
cikin Alkur'ani, hatta Annabawan Allah da Manzanni bautar Allah suke
yi don tsoron azabarsa da fatan rahamarsa.
Allah madaukaki ya ba mu labarin zababbun bayinsa,Annabawa
da Manzanni,wadanda suka hada da Ibrahim da Ishaku da Ya'akubu da Ludu
da Nuhu da Dawudu da Sulaimanu da Ayyubu da Isma'ilu da Idrisu da Zul
kifili da Yunusu da Zakariyya da Yahya,sa'annan ya ce, "Lalle ne
su,sun kasance suna gudun tsere zuwa ga ayyukan alheri.Kuma suna kiran
mu a kan kwadayi da fargaba." (Suratul Ambiya:51-90) "Suna kiran mu"
ma'anarsa suna bauta mana,akan kwadayi,watau fatan rahama,da
fargaba,watau tsoron azaba.
Wannan ya tabbatar da cewa duk bautar da akayi ba akan
kwadayi da fargaba ba,to bautar bidi'a CE
wacce ta saba tafarkin Manzanni.
Duka wadannan abubuwa suna cikin bidi'o'i da
tsurface-tsurface wadanda suka shiga cikin Sufanci a wannan mataki na
farko.Kuma idan mai karatu ya lura da kyau zai ga cewa har ya zuwa yau
yawancin wadannan abubuwan suna nan tare da Sufanci, ba su rabu da shi
ba.

Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 18 Insha Allah.

Abu Aisha Journalist.
Jibwis Social Media Katsina.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve