*FITOWA TA 16
*Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
Wani misali kuma shine,wasu daga cikinsu sun takura wa
kansu ainun wajen ibada,yayin da suke kwana sallah su wuni azumi,kuma
ba tare da wani abin sa wa a baka na kirki ba(tunda ba sa Sana'a),da
haka har suka lalace,wahala ta ci karfinsu alhali kuwa addinin Allah
sauki gare shi,kuma babu cuta ko cutarwa a cikinsa. Bugu da kari
kuma,hadisin Manzon Allah (S.A.W) sun taho da haramcin azumin
dun-dun-dun,wasu kuma hadisan kuma sun tabbatar da cewa Annabi (S.A.W)
bai taba sallatar dare baki dayansa ba,amma ya kasance yana sallah ne
na wani lokaci kuma ya huta a wani lokaci.
Wasu kuma sun kaurace wa mutane, suka tare a dazuzzuka da
kayin duwatsu,wai don su ji dadin shagala da ibada.A sakamakon haka,da
yawa daga cikinsu suka gamu da hadarin yunwa da cututtuka,ko kuma su
afka ga namun daji.Abu ne sananne cewa wannan hali ya saba wa
Musulunci domin a tsari nasa ibada a cikin jama'a muhimmin abu ne kuma
ladanta ya fi ladan ibada a kebe.
Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 17 Insha Allah.
Abu Aisha Journalist.
Jibwis Social Media Katsina.
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve