*FITOWA TA 16
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA KUR'ANI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
Na biyu,wannan akida har ila yau,tana karyata Alkur'ani ta
wata fuskar dabam;domin tana kafirta ko fasikantar da wadanda Allah ya
bayar da labari cewa ya yarda da su kuma ya yi masu gafara:su ne
Sahabban Annabi(S.A.W),Allah ya kara musu yarda baki daya.Akidar ta
kafirta Sahabbai ta hanyar dangana musu sauya Alkur'ani, da boye
abinda Allah ya saukar,da yin kari da ragi a cikinsa.Allah yana fadi
dangane da Sahabban Annabinsa: "Kuma magabata na farko daga Muhajirina
da Ansar da wadanda suka bi su da kyautatawa,Allah ya yarda daga gare
su,su kuma sun yarda daga gare shi,kuma ya yi musu tattalin gidajen
Aljanna:koramu suna gudana a karkaahinsu,suna madauwama a cikinsu har
abada.wancan ne babban rabo mai girma." (Suratut Tauba:100).
Dan uwa mai karatu ka dubi abinda Allah ya ce dangane da
Sahabban Annabinsa, har ma da wadanda suka bi su da kyautatawa,sa'an
nan ka dubi abinda yan Shi'a suka jingina musu na sauya maganar Allah
da cin amanar Manzonsa,za ka san cewa lalle yan Shi'a sun yi nisa daga
barin shiriya.Muna rokon Allah ya arzurta su da tuba kyakkyawa,da
komawa ga tafarki madaidaici:tafarkin Sunnar Annabi (S.A.W).Mu kuma,ya
nesanta mu da irin wannan bata mabayyani.
MUHIMMIYAR SANARWA
Dukkan littafan malaman Shi'a, da muka yi amfani da su a rubutun
wannan takaitaccen littafi,akwai su a dakin karatu(laburare)na cibiyar
MARKAZUS SAHABAH dake Sakkwato.Laburaren a bude take ga kowa da kowa.
Tare da gaisuwar dan uwanku a Musulunci.
Dr.Umar Labdo.
Alhamdulillah, Anan zamu dakata kuma muka kawo karshen littafi na daya
sai mun hadu a sabon littafi na gaba wato littafi na biyu a jerin
littafan Shi'a Insha Allah.
Tare da dan uwanku.
Abu Aisha Muhammadul Araby Journalist.
Jibwis Social Media Katsina.
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve