Monday, 2 October 2017

*FITOWA TA 15
*Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com

Akwai kuma Sufyan Althauri wanda malami ne babba da
ya kware a kan ilmin Hadisi.Althauri mutum ne mai yawan ibada da gudun
duniya.Ra'ayinsa a kan gudun duniya ra'ayi ne mai kyau Wanda aka gado
shi daga Sahabbai da Tabi'ai.An ruwaito shi yana fadin,"Gudun duniya
shi ne takaice buri amma ba cin abinci marar kyawu,ko zama da datti,ko
sanya tufafin suf ba." Ya rasu a shekara ta 161 bayan Hijira.
Har ila yau,akwai Rabi'ah Al'adawiyya wacce ita ma tana
daga cikin manyan Sufaye na wannan mataki. Rabi'ah ta kasance mace ce
mai yawan ibada da lazimtar bautar Ubangiji.Babban abinda ta shahara
da shi,shi ne tsananin soyayya da kaunarta ga Allah mahaliccinta.Daga
cikin maganganunta an ruwaito tana cewa, "Na rantse da girmanka (ya
Ubangiji), ba na bauta maka don tsoron wutarka ko kwadayin
aljannarka.Amma ina bauta maka ne don girmama zatinka da tsananin
kaunarka." Ta rasu a shekara ta 180 B.H.
Banda wadannan da muka ambata akwai wasu mutane da dama
wadanda aka lasafta su a cikin manyan Sufaye na wannan mataki,kamar su
Zunnun Almisri da Abul Kasim Aljunaid.Koda yake Sufanci a wannan
mataki na farko bai fara gamuwa sosai da bakin falsafofi da ra'ayoyi
wadanda suka saba da Musulunci ba,amma duk da haka bai rasa samun wasu
aibuka wadanda suka lake masa ba.Ga misali,wadansu Sufaye na wannan
mataki sun gaza fahimtar tawakkali kamar yadda ya kamata yayin da suka
dauka cewa tawakkali shi ne mutum ya zauna kurum,hannu rabbana,Allah
ya kawo masa abincinsa har daka.Don haka sai yawancinsu suka bar
sana'a,noma ko kasuwanci,da sauran hanyoyin neman arziki,alhali kuwa
Musulunci yana umarni da aiki da fafutukar neman halali.

Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 16 Insha Allah.

Abu Aisha Journalist.
Jibwis Social Media Katsina.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve