Thursday, 17 August 2017

MAZHABANCI DA KUNGIYANCI SUN SABA WA MUSULUNCI:

MAZHABANCI DA KUNGIYANCI SUN SABA WA MUSULUNCI:
Mazhabanci shi ne: Nassin Annabi mai tsira da amincin Allah ya inganta cikin wata mas'ala daga cikin mas'aloli, sannan wani ya ce ba zai yi aiki da nassin ba; saboda mazhabar da yake bi ba ta yin aiki da nassin! Lalle yin hakan haramun ne a bisa Ijma'in malaman Musulunci.

Kungiyanci shi ne: Nassin Annabi mai tsira da amincin Allah ya inganta cikin wata mas'ala daga cikin mas'aloli, sannan wani ya ce ba zai yi aiki da nassin ba; saboda kungiyar da yake memba ne a cikinta ba ta yin aiki da wannan nassin! Tabbas yin hakan haramun ne a bisa Ijma'in malaman Musulunci.

To amma idan aka guje wa mazhabanci, to lalle yin mazhaba ba yi da laifin kome. Haka nan idan aka guje wa kungiyanci to yin kungiya ba yi da laifin kome. Allah Ya taimake mu har kullum. Ameen.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve