Wednesday, 16 August 2017

FITOWA TA 3
*DAGA LITTAFIN:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE
*Jerin Littafan Sufanci Na 1
*Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:-www.jibwiskatsina.blogspot.com

Har ila yau,akwai masu ra'ayin cewa asalin wannan kalma shine
assuf.Shi assuf wani tufafi ne mara kyawu sosai,amma yana da karfi da
aminci,wanda aka lura yawancin sufaye na zamanin da suna amfani da
shi.Don haka sai ake jin cewa daga sunansa suna samo sunansu.Wasu kuwa
a ra'ayinsu,wannan kalma an fiddo ta ne daga kalmar nan ta larabci
assafa'u,watau tsarkin zuciya da kyawun hali.Dalilin masu wannan
ra'ayi shi ne,shi tabbatar da sifofin tsarkin zuciya da kyawawan
halaye shi ne manufa ta farko a wajen yawancin sufaye,kuma shi ne
kashin bayan galibin darikunsu.Don haka,suna ce,lallai wannan kalma
ita ce asalin kalmar Sufi.
To amma daga cikin wadannan ra'ayoyi guda biyar duka,ra'ayi daya ne
rak yafi zama karbabbe.Wannan shi ne ra'ayin masu cewa Kalmar Sufi an
fiddo ta daga Kalmar assuf.Dalili akan wannan kuwa shine,idan aka koma
ga ka'idojin Nahawun larabci,to daga Kalmar assuf ne kawai za'a iya
fitar da Kalmar assufiyyu,watau Sufi kai tsaye.Sauran kalmomin da aka
ambata duka:sofiya da suffa da Banu sufa da assafa'u,ba'a iya fitar da
Kalmar Sufi daga cikinsu a bisa tsarin Nahawun larabci ingantacce.Kuma
koda yake ba ko wane Sufi ke amfani da tufafin assuf ba,to amma
dacewar Kalmar da ka'idojin larabci da kuma kasancewar yawancin sufaye
na zamanin da suna amfani dashi,shi ya sanya wannan ra'ayi ya fi
karbuwa ga Malamai.
Wannan magana kenan akan asali. Kalmar Sufi.Amma idan muka koma ga
hakikanin abinda ake nufi da kalmar,to anan sai mu iske cewa anyi
sabani.Bari mu saurari abinda sufaye da Kansu suke fadi dangane da
hakan.
Sai mun hadu a fitowa ta 4 Insha Allah
Abu Aisha Journalist.
JIBWIS SOCIAL MEDIA KATSINA

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve