Wednesday, 16 August 2017

*FITOWA TA 3
*DAGA LITTAFIN:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA KUR'ANI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A NA 1.
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah)
*YADAWA:-www.jibwiskatsina.blogspot.com
Wani babban malaminsu mai suna Hashim binu Sulaiman Albaharani
yana fadi acikin wani littafi nasa da ya rubuta a kan tafsiri, "Ka
sani cewa a hakikanin gaskiya wacce babu kokwonto a cikinta,gwargwadon
ruwayoyi mutawatirai,wannan Alkur'ani da yake hannunmu sauye-sauye sun
faru a cikinsa bayan rasuwar Manzon Allah (S.A.W) kuma wadanda suka
tattara shi bayan Annabi(s) sun debe kalmomi da ayoyi masu yawa daga
cikinsa.[Duba ALBURHAN FI TAFSIRIL QUR'AN na Hashim binu Sulaiman
Albaharani,bugu Almadaba'atul Ilmiyya,Qum-Iran,1393,Shafi na 36.
A cikin littafin Alkafi,littafin da ya fi ko wanne inganci a
wajen yan Shi'a,an yi bayanin gwargwadon abinda aka debe daga cikin
Alkur'ani. Marubucin littafin,watau Muhammad binu Ya'akub
Alkulaini,ya ce, " An ruwaito daga Abu Abdullahi (watau Imamin Shi'a
na shida) cewa Alkur'anin da Jibrilu ya zo da shi ga Muhammad (S.A.W)
aya dubu goma sha bakwai (17,000) ne". [A duba Alkafi na Muhammad binu
Ya'akub Alkulaini,Darul kutubul Islamiyya,Teheran-Iran,ba
tarihi,Mujalladi na 2,shafi na 634]. Wannan yana nufin kenan cewa
kur'anin da yake hannunmu dan ragowa ne kawai;domin kuwa a bisa ga
wannan ruwaya wadanda suka tattara littafin a bayan rasuwar
Annabi(S.A.W) sun debe kimanin sulusi biyu na littafin. Zamu tabbatar
da haka idan muka lura da cewa Alkur'anin da yake hannunmu, wanda
musulmi suka sani a yau,ayoyinsa dubu shida da dari biyu da talatin da
Shi'a ne (6,236)kawai,kamar yadda malaman Sunna suka tabbatar. [Duba
Tafsiru Ibnu Kathir na Isma'il binu Kathir,bugun Maktabatus
safa,Alqahira,1423/2002,mujalladi na 1,shafi na 7.
Anan zamu dakata sai fitowa ta 4 insha Allah.
Abu Aisha Journalist
JIBWIS SOCIAL Media Katsina

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve