Thursday, 10 August 2017

*FITOWA TA 2
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA KUR'ANI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:-www.jibwiskatsina.blogspot.com

Yan Shi'a suna zargin Sahabbai da sauya Littafin Allah,da canja
ayoyinsa.Suka CE wai Sahabbai sunyi haka ne ta hanyar debe ayoyi masu
yawa da aka saukar wadanda suke tona asirinsu da kuma ayoyi da suke
nuna falalar Ali binu Abi Dalib(r.a) da zuri'arsa.Abinda suke nufi da
tona asirinsu,wai bayyana a kafirci da munafuncin Sahabbai. Wal iyazu
billahi!!
Saboda haka a wurin yan shi'a,ayoyi da yawa dake cikin
Alkur'ani ba maganar Allah bace,wannan yasa suke zabar abinda ya dace
da son zukatansu acikin Alkur'ani, saura kuma suyi burus dashi.
Anan zamu dakata sai Fitowa ta 3 insha Allah.
Abu Aisha Journalist.
Jibwis Social Media Katsina

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve