Tuesday, 8 August 2017

Ba gina gidan masaukin baki bane matsalar su, Izalar ce matsalar su......

Ba gina gidan masaukin baki bane matsalar su, Izalar ce matsalar su......

Daga Ibrahim Baba Suleiman

Da yawa in ka lura da wadanda suke su ka akan wannan ci gaba na gidan baki da Izala tayi a birnin tarayya Abuja zaka ga ba 'yan Izala bane, ko dai masu addini da kari, ko masu adawa da sahabban Manzon Allah (S) ko 'yan chaburos.

Kuma zakaga Ahlussunnah na kwarai wadanda basa kungiyar Izala ko wane bangare suna murna da wannan ci gaba, hatta 'Yan uwan mu 'yan Izalar jos sun taya mu murna domin sun san cewa wannan ci gaba ne a cikin Izala.

Kuma daga cikin wadanda suke wannan shirme zaka iya samun cewa babu wanda ya taba bada kwandalar sa don wani aikin ci gaba a izala, amma sabida basu da albarka su suke da bakin magana.

Makarantu kuwa da Izala ta gina a fadin kasarnan, zaka iya samun masu sukar sunyi wannan Islamiyya, a kano kawai kungiyar tana da makarantu sama da 700 banda sauran jihohi, ta bangaren asibitoci kuwa kowa yasan akwai su a wurare da dama cikin kasar nan mallakar Izala, kazalika makarantu akwai su irin su makarantar koyon aikin jinya a Bauchi da wasu da dama daga cikin jihohin kasarnan kuma duk mallakar Izala.

Shugaba Sheikh Abdullahi Bala Lau da 'yan majaisar sa su sun cancanci a yaba musu, sun nunawa duniya cewa Izalar ce a gabansu ba kawunan su ba, sun samawa kungiyar kadarori maimakon azurta kawunan su, bamu da abun da zamu saka musu da shi sai addu'ar Allah ya musu sakayya da gidan Aljanna. A halin yanzu kungiyar tayi hobbasa domin gina sakateriyar kungiyar mai dauke da Babban Ofisoshi na ma'aikatan kungiyar, Asibiti, Babban Dakin taro, Makaranta da masallaci wanda zai lakume miliyoyin Naira, kuma da tallafin da muke bayarwa da shi za'ayi wannan aiki insha Allah, dan haka tuni aka bude wannan asusu domin fara wannan aiki, Ga wadanda za su taimaka ga Account na kungiyar.......

Acc Name: Jibwis
Acc No: 0001147652
Bank: Unity Bank

AccName: Jibwis
Acc No: 1013090576
Bank: Zenith

Kuma A daidai wannan lokaci muke kiran mabiyanmu marubuta a kafar yanar gizo ('Yan Social Media) da kada a sake magana akan wannan lamari, baza su daina ba, 'Yan bakin ciki ne da hassada, babu yadda kuka iya da su, kawai ku fita harkarsu, kuyi aiki domin Allah, Hausawa sunce ''Makiyinka ko ruwa ka fada zai ce ka tada kura"...

Allah ya shirya su, yasa su gane, ya raba su da ciwon hassada. Amin.

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve