*FITOWA TA 7
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA KUR'ANI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
A ganinsu,Mushafu Fadima shi ne kur'ani na gaskiya wanda Imamansu
suka gado shi daga Nana Fadima diyar Manzon Allah(s.a.w.) da mijinta
Ali binu Abi Dalib,Allah ya kara musu yarda.Muhammad binu Hassan
Alsaffar,wanda ake lissafa shi daga cikin manyan malaman Shi'a
magabata (ya rasu a shekara ta 290 B.H),ya ruwaito a cikin
Littafinsa,BASAIRUD DARAJATI,daga Imam Abu Ja'afar wai ya ce,"Babu
wani da zai iya da'awar cewa ya tattare Alkur'ani dukkaninsa,zahirinsa
da badininsa,sai masu wasicci," yana nufin Imamai.Har yau,a cikin
littafin ya ruwaito daga gare shi yana cewa,"Babu wani daga mutane
wanda zai ce ta tattare Alkur'ani dukkaninsa,kamar yadda Allah ya
saukar da shi,sai makaryaci.Ba wanda ya tattare shi,ya haddace shi
kamar yadda aka saukar da shi,sai Ali binu Abi Dalib da Imamai a
bayansa."[Duba Basa'irud Darajatil Kubra fi Fada'ili Aali Mahammad na
Muhammad binul Hassan binu Farrukh Alsaffar,bugun Manshuratul
A'alami,Teheran-Iran,1362,shafi na 213].
Anan zamu dakata sai min hadu a fitowa ta 8 Insha Allah.
Abu Aisha journalist
Jibwis Social Media Katsina
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve