*FITOWA TA 6
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA KUR'ANI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com
Yan Shi'a suna da nasu Alkur'ani dabam,Wanda suke kira MUSHAFU
FADIMA,watau kundin Fadima.Dangane da Wannan littafi,malaman Shi'a
suna dangana ruwaya ga Imaminsu na shida,Imam Ja'afar Sadik,cewa wai
ya ce,"Fadima ta bar wani kundi Wanda ba kur'ani ba ne,amma kuma
Kalmar Allah ce da yayi wahayin ta zuwa gare ta.Shi kundin shiftar
Annabi ne kuma rubutun hannun Ali."[A duba Basa'irud Darajati na
Alsaffar,shafi na 176].A wata ruwayar kuma,ya ce,"Shi kundi ne da ya
ninka kur'ani uku kuma amma,na rantse da Allah, babu kalma daya a
cikinsa ta kur'aninku."[Duba Alkafi na kulaini,mujalladi na 1,shafi na
171].
Anan zamu dakata sai fitowa ta 7 Insha Allah
Abu Aisha journalist
Jibwis Social Media Katsina
No comments:
Post a Comment
Your Comment will help us to improve