Monday, 21 August 2017

*FITOWA TA 5
*Daga Littafin:-SUFANCI DA AKIDUN SUFAYE.
*Jerin Littafan Sufanci Na 1.
Wallafar:-Prof.Umar Labdo(hafizahullah)
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com

Ma'aruf Alkurkhi,daya daga cikin kasaitattun sufaye na farko,yana
cewa:"Sufanci shi ne yin riko da duk abinda yake na gaskiya,da debe
kauna daga dukkan abinda yake hannun mutane."Junaidu kuma,wanda shi ma
kasaitaccen Sufi ne daga cikin magabata,cewa ya yi,"Sufanci shi ne
tsarkake zuciya ga barin bin ta mutane,da kokarin rabuwa da halaye na
assha da dabi'u na Allah wadai,da bushe sifofin adamtaka,da gudar
sha'awe-sha'awen zuciya,da lazimtar sifofi kyawawa,da shagala da
ilimin hakika da aikata abinda yake mafi kyawu a koda yaushe,da yin
nasiha ga dukkan talikai,da yin riko da gaskiya da kuma bin Manzon
Allah (S.A.W) ga shari'a."
Har ila yau,wani gawurtaccen Sufi da ake kira shazali yana
cewa,"Sufanci shi ne tursasa rai bisa bautar Allah,da juyar da shi rai
din zuwa ga hukunce-hukuncen Ubangiji."
Wannan shi ne ma'anar Sufi da Sufanci kamar yadda sufayen su
da Kansu suke fadi.Mabambantan ra'ayoyi da muka kawo kuwa dan misali
ne kawai na sabanin dake tsakanin sufaye dangane da hakikanin wannan
tafarki da masu bin sa.Kuma za'a yi tsokaci da cewa yawancin kalmomin
da suke amfani da su wajen bayanin ma'anar Sufanci da hakikanin Sufi,
kalmomi ne dake cike da ma'anoni na aro da jirwaye da hannunka mai
sanda.Wannan dabi'ar sufaye ce wacce take lazimtar su ko da yaushe;ba
sa magana kai tsaye don bayanin abinda suke nufi,sai dai su yi ta
kewaye-kewaye,suna amfani da kalmomi wadanda a wani ya yi suke kama da
zaurance.

Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 6 Insha Allah.
Abu Aisha journalist
Jibwis Social Media Katsina

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve