Monday, 21 August 2017

*FITOWA TA 5
*Daga Littafin:-AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA KUR'ANI.
*JERIN LITTAFAN SHI'A 1
*WALLAFAR:-PROF.UMAR LABDO(hafizahullah).
*Yadawa:- www.jibwiskatsina.blogspot.com

Wani Kasurgumin malamin Shi'a,mai suna Husain binu Muhammad Annuri
Aldabarsi,ya rubuta shirgegen littafi musamman don ya tabbatar da
akidar yan Shi'a cewa Alkur'anin nan da yake a hannunmu a yau ba
cikakke ba ne,kuma akwai sauye-sauye,da kare-kare,da rage-rage,a
cikinsa.Littafin wanda ya sa wa suna FASLUL KHIDAB FI ITHBATI TAHRIFI
KITABI RABBIL ARBAB,(Watau Yankakkiyar Magana A Kan Tabbatar Da Sauya
Littafin Mamallakin Mamallaka),ya kunshi dubunnan ruwayoyi daga Imaman
Shi'a da Malamansu wadanda suke tabbatar da cewa wai wadannan
sauye-sauye, da kare-kare, da rage-rage Sahabbai,wadanda suka hada da
Abubakar da Umar da Usman,Allah ya yarda dasu baki daya,su ne suka
zartar da su.A cikin littafin har ila yau,an tabbatar da cewa malaman
Shi'a kaf,magabatansu da na bayansu,sun hadu a kan wannan akida.[Duba
Faslul Khidab na Aldabarsi,shafi na 34].

Anan zamu dakata sai mun hadu a fitowa ta 6 Insha Allah.
Abu Aisha journalist
Jibwis Social Media Katsina

No comments:

Post a Comment

Your Comment will help us to improve